Aisha Seyoji" />

Yadda Maza Suka Kwace Wa Mata Al’adar Yafa Mayafi A Kabilar Tuareg

A yau mun kewaya duniya inda mukaci karo da mutanen Kabilar Tuareg, filin namu na yau zai sada ku ne da mutanen Tuareg da ke saharar kudancin yammacin Libiya, Aljeriya, Nijer, Mali da kuma Burkina Faso.
Mutanen Tuareg ko a ce twareg ko ku ma touareg(kel Tamashek) mutane ne na saharar can kudancin yammacin Libya har zuwa kudancin Algeria, Nijer, Mali da Burkina Faso. Makiyaya ne da akan same su har ta arewacin Nijeriya.
Mutanen Tuareg na da yaren su mai suna Tuareg ko a ce masa Tamashek.
Sun samo sunan su na mutanen Blue colour ne daga kalan kayan al’adar su da suke sawa a sakamakon haka yake rinar musu jiki. Makiyaya ne ma’abota addinin Islama daga Arewacin Afrika. Dan kuwa suna daya daga cikin yarukan da aka fadi a tarihin Islama wadan da suka bada gudumawan su wajen yada addinin na Islama Daga arewacin Afrika har ta wuraren sahel.
Mutane ne masu shiryayyen rayuwa kama daga kan shugabanci, zamantakewa da sauran su. Sun jagoranci kungiyoyin yan kasuwar sahara, su kuwa wadannan kungiyoyi sanannu ne wurin tada zaune tsaye kama daga kafun zuwan turawan mulkin mallaka har bayan zuwan su.
Yanayin daukakar matan mutanen Tuareg zai zo daya da yadda al’adar larabawa ta dau mata.
Sutura
Matan Tuareg basa yafa mayafi kamar yadda aka sani mazan su ke yafawa.
Babbar sutura mai muhimmanci wurin tuareg shi ne tagelmust ko kuma ace eghewed ko kuma litham. Wadda ake ce da shi shesh sai kuma ko yaushe sukan yafa indigo blue mayafi da ake kira Alasho. Yafa wannan mayafi da mazan ke yi ya samo asali ne daga yarda da sukayi da cewa yana kore mugayen halittu ko kuma za’a iya alakanta shi da yanayi na saharar da suke tafiya akai. Kuma sukan saka abun hannu mai dauke da ayoyi da al-Kurani da sauran abubuwan tsari. Da zarar ka ga namijin tuareg da wannan mayafi to alamace da zai nuna cewa ya girma mayafin kan rufe musu fiska ne wurin idon su da hancin su.
Mayafin da suke rufe fiska da shi ana kiran sa Tagelmust.
Akwai rawani(turban) wadda maza ke sawa
Alosho:shi ne blue din mayafin da mata da maza kan saka.
Bukar: bakin rawani wadda maza ke sa wa.
Tasuwart: mayafin mata ne
Takatkat: riga ce maza da matan su ke sakawa.
Takarbast: guntuwar riga shima mata da mazan su ke sakawa.
Akarbey: wando ne na maza.
Afetek:sakakkiyar rigar mata
Afer:mata ke sawa
Bernuz:doguwar rigar saka da ake sawa don sanyi
Akhebay: sakakkiyar rigar mata mai colourn green ko blue mai haske
Ighateman:takalmi
Iragazan:sandal na leda
Kamar yadda na fadi a baya ana kiran su blue din mutane saboda indigo din mayafin su yakan musu fentin blue a jiki. Shi wannan mayafin sukan yi amfani da shi ne lokacin bikukkuna ama a zahiri suna saka kaya kaloli daban daban.
Abinci
Taguella burodi ne fale-fale da akeyi daga garin alkama sai a dafa shi da garwashi,ama fa shi wannan bredin bisine shi ake a cikin kasa mai zafi idan ya dahu sai a gusura shi kana na aci da miyar nama. Akwai kuma faten gero da suke kira da cink ko liwa wadda suke yin sa kamar ugali ko fufu. Akan tafasa gero kuma ayi kunu sai a zuba madara ko kuma miya mai kauri .
Suna da madarar rakumi da kuma na akuya da suke kira akh,sai kuma cheese(man shanu) ta komart da kuma tona shi kuma yogurt ne da ake daga su. Sa’annan akwai kuma Eghajira shi kuma beberage ne da ake sha da ladle. Ana yin sa da gero da farko ana samun dakakken gero,man akuya,dabino,madara da sukari sai ayi yawanci suna yin sa a bikukkuna.
Akwai sanannen shayin su mai suna atai ko ashahi wadda ake daga garin bindiga,da koriyar ganyen shayi sai kuma sukari. Bayan an dafa akan sai saita shi har sau uku daga cikin buta zuwa waje sai a kuma mayarwa har sau uku bayan wannan na’a na’a da sugar wadda sukan sai saita shi daga tsayin da zayyi daga saman kafada i zuwa setin kafa zuwa cikin kananun kofunan shayin.
Yawancin zanukan yaren Tuareg na kayan kyale kyale ne su sarka dankunne abun hannu da sauran su,suna da zanen su na miji da matar sa sanye da kayan kawa na al’ada,sukan yi na leather da linzamin karfen da ake masa ado da suke kira trik,sai kuma takobi masu kyau. Kwararru ne wurin yin abubuwan hannu na al’ada kamar su tanaghilt ko zakkat( cross din mutanen agadez,croid d’Agadez)
Takobin tuareg(takoba),sarakuna na gwal da azurfa da ake kira takaza da kuma dankunne tizabaten. Akwatin matafiya masu dauke da adon tagulla da karaguna masu kyaun gani kuma ana iya amfani da wadannan akwatuna wajen daukar abubuwa.
Kasancewar samaniyar wurin sahara ya kasance mai fili da haske ya saka mutanen tuareg suka zama masana taurari.
A cikin sanin su akwai su azzag willi(benus),wadda yake nuna lokacin tastsar akuyoyin su.
Shet ahad (pleiades) ‘yan’uwa mata guda bakwai na dare.
Amanar(orion)jarumin sahara
Talemt(ursa major) farkawar macen rakumi
Awara(ursa minor) yarinyar rakuma ta kwanta bacci
Gine gine
A lokacin da mutane ke kara cigaba wajen kawata muhallin su,haka zalika suma tuareg an sansu da bukkokin su na kiwo. Masu yanayi iri iri akwai wadda suke rufe shi da fatar namun daji,wasu kuma da tabarma. Yanayin gine ginen ya banbanta saboda yanayin wurin zamar da suka kaura.
A al’adance shi wannan bukka ana yin sa ne tun farko a lokacin aure dan ana daukar sa a matsayin abunda zai nuna mutum ya yi aure har akwai wani karin magana na su da suke fadawa masu aure masu bukka wannan shi zai fada maka mutumin yayi aure. Yandu zamani ya kawo musu changy ta yadda akan yi wa mata bukkanta ta mussaman a tsakar gidan mijin ta.
Tarihi ya nuna cewa farko sukan yi gida ne a saman bishiyar acacia,tasagesaget. Suna da kuma wasu gidajen kamakamar su ahaket(bukkar fatar akuya jar bukka).
Tafala(zanar kararen gero).
Akarban ko takabart(gidan da ake a lokacin sanyi)
Ategham(gidan lokacin zafi)
Taghazamt(gidan da ake dan dogon zama) ahaket(gidan da ake da tabarma domin lokacin rani mai samar skuare da buli buli domin kiyaye iska mai zafi)
Auratayya
Auren dangi ko auren ‘yan’uwa na kusa ya kau a buranen su sai a kauyuka kuma yawanci suna yi ne don farantawa iyayen su mata wadda sukan rabu daga baya su auri wadda ba yan dangin su ba,sarakunan su,malaman su na auren mata sama da daya,sabanin al’adar tuareg na auren mace daya,haka kuma sabanin ra’ayin wasu matan da basa son abokanen zama.
Yanayin zamantakewar auren su ya rabu kashi kashi wasu sukan zauna gidan iyayen mata wasu gidan iyayen miji,masu zama gidan iyayen mata kan yi hakan ne a shekaru uku ko biyu na farkon aure lokacin da miji ya biya sadaki tare da sauran abubuwan da ya dace na al’ada ya kuma bada kyaututtuka ga dangin matar sa daga nan sai su zabi wurin da zasu zauna amarya kan iya raba kiwon ta daga cikin na iyayen ta sai ta gina madafin ta daban da na mahaifiyar ta.
Gadon su ya samo asali ne daga addinin islama don haka dai dai da yadda addinin ya tsara ake yi sai dai idan mamacin ya rubuta wasiyyar sabanin haka.
Iyaye maza su ne masu tsawatar wa,ama kamar su kawunen yara ko kuma baffanun su kan zama kamar abokanen wasa ne ga yaran,matan da suka aurar da yaran su kan dauko yaran yan uwa suna taya su yan aikace aikace. Duk da cewa mazajen matafiya ne ama yaran kabilar sukan samu tsawatarwa daga masu wadata,shugabanni,da kuma malaman addinin su wadda su basa bin tafiyar kasuwanci. Su ke nuna wa yara maza matasa aikin da ya kamata suyi tare da daura su akan karatun islama,su kuwa yara mata dama suna kusa da iyayen su mata sukan koyi aikin gida da kuma kiwo.

Exit mobile version