Bello Hamza" />

‘Yadda Mijina Ya Yi Wa ’Ya’yana Biyu Fyade’

A jiya Litinin ne, wata ‘yan kasuwa ,mai suna Misis Tope Ogba ta bayyana wa kotun dake kula da cin zarafun mata da laifukan da suka shafi lalata da mata dake Ikeja ta jihar Legas, cewa, mijin ta mai suna Mista Gabriel, ya yi wa ‘ya’yan su mata biyu fyade.
Da lauyan mai gabatar da kara na jihar Legas ta jagorance ta wajen bayar da shaida, (Misis K A Momoh-Ayokambi), Tope a bayyana cewa, mijin nata ya yi lalata da ‘yar karama ‘yarsu ya kuma kusan banka mata wuta a lokacin da ta kai kara wajen hukuma.
Ana tuhumar Gabriel ne, da cin zarafin ‘ya’yan nasa ta hanyar lalata da su, ‘yan matan masu shekara 25 da 20 da kuma mai shekara 13 a gidansu dake a garin Oke-Ogbe kusa da Atura Bus a kan hanyar Badagry ta jihar Legas.
Tope ta bayyana wa kotun cewa, bata da masaniyar abin da yake tafiya na lalatar da yake yi ‘yan matan, tana kuma tunanin an yi shekaru ana yi har sai da ‘yar karamar yarinyar ta bayyana mata.

Ta kuma bayyana cewa, “Ban san abin da yake tafiya ba har sai da ya farmaki ‘yar karamar yarinyar daga nan ne, na kuma samu labarin irin yada yake lalata da manyan yaran nawa daga wasu mutane a unguwarmu.
“Da farko dana tambayi manyan yaran nawa sun karyata amma na samun cikkaken bayanin ne daga Malamar ‘yar tawa ta uku, inda ta bayyana mani dalla dalla yadda ya nemi ya yi lalata da ita.
“Da na fuskance shi da labarin sai ya ce, wannan wani hadin kai ne don a ci masa mutumci a tsakani na da yaran nawa, sai na bayyana masa cewa. ‘yar karamar yarinyarmu ta kawo mano labarin a kan shi.
“Tun da na fuskance shi da labarin, ban sake samun zaman lafiya a cikin gidan ya shiga duka na babu kakautawa ya na kuma yi mani barazana a kowanne lokaci.”
‘Yar kasuwa ta kuma bayyana cewa, wata daya bayan ta sanar da hukuma a kana bin da ake ciki sai ya kara kamari a kan yadda yake ci mata mutunci.
Data take amsa wani tambaya ta bayyana cewa, bata da masaniyar lokacin da aka fara cin zarafin yaran nata, bata san lokacin da ya fara yin lalatar da yaran ba.
“Ban san lokacin da ya fara lalata da yaran ba, ni nake fita neman abin da iyalin za su ci daga sana’ar da nake yi.
Bayan da ta gama bayar da shaida sai aka nemi ‘yar karamar yarinyar ta kawo nata shaidar, inda alkaliyar ta nemi kowa ya fita daga cikin kotun saboba yarinyar ‘yar karama ce don kuwa shekarar ta 13, inda ta bayar da shaida a kan yadda mahaifin nata yake lalata da ita.
Daga nan ne aka daga karar zuwa ranar 7 ga watan Maris don ci gaba da sauraron yadda za ta kaya.

Exit mobile version