A ranar Asabar ne rundunar sojan Nijeriya ta gabatar da wasu bayanai game da yadda ta gudanar da aikin ceto yaran nan 344 da aka sace daga makarantarsu da ke garin Kankara a cikin Jihar Katsina, a ranar 11 ga watan Disambar da ta gabata. An sami nasarar kubutar da yaran ba tare da rauni ba, an samu turjiya daga masu garkuwar wadanda suka yi wa sojojin kwanton-bauna.
Manja Janar John Enenche, Mai Gudanarwa, Ayyukan Yada Labarai na rundunar Tsaro, da Manjo Janar Ahmed Jibrin, mai ritaya, tsohon Daraktan, hukumar Leken Asiri na Soja, ya ba da labarain a ranar Asabar lokacin da aka nuna su a wani shiri na musamman na Gidan Talabijin na Nijeriya, “Barka da Safiya Najeriya.” Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa Jibrin a halin yanzu shi ne Mashawarci na Musamman, Fasaha, ga Ministan Tsaro, Manjo-Janar Bashir Magashi maia ritaya.
Jibrin ya ce bayan sace yaran, Ministan ya jagoranci wata tawaga, ciki har da Shugabannin Ma’aikata da Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, zuwa Katsina da Kankara. Ya ce Ministan ya ba da ka’idojin shiga da ke jagorantar sojoji don tabbatar da cewa an ceto yaran da aka sace ba tare da asarar rai ba kuma a cikin mafi kankanin lokacin da zai yiwu. “Bayan umarnin, rundunar ta rufe kan masu satar daga bangarori daban-daban guda hudu, gami da karfafawa da aka yi daga wasu bangarorin don tabbatar da cewa an rufe wurin baki daya.