Daga Rabiu Ali Indabawa,
An kama wasu mutane biyu da ake zargi da kisan wata yarinya a Bauchi, kuma sun a lokacin da aka kama su suke fada wa ’yan sanda dalilin da ya sa suka aikata wannan mummunar aikin. Wani shafin yanar gizo mai yada labarai, PRNigeria ya ruwaito cewa wadanda ake zargin, a cikin wani faifan sauti na tambayoyin sun furta cewa wani marabou Malamin duba ya ba su kwangilar kawo farjin karamar yarinya don yin tsafi kan kudi Naira 500, 000.
Mutane biyun da ake zargi, Abdulkadir Wada, mai shekara 19, da Adamu Abdulrauf, mai shekara 20, sun yi ikirarin ne lokacin da jami’an rundunar ‘yan sanda ta Jihar Bauchi ke yi musu tambayoyi bayan an kama su. Da yake magana da harshen Hausa, Wada, babban mai laifin, ya ce shi da abokin aikin nasa, Abdulrauf, sun tafi Kwata, yankin da babban wansa yake wanda shi wan nasa yana aure.
Bayan sun isa yankin, sai suka kama wata karamar yarinya zuwa cikin wani gini da ba a kammala ba kuma suka shake ta har lahira. “Daga nan Abdulrauf ya zare wuka daga aljihunsa ya yanke al’aurar yarinyar. Marabout ne, wanda a yanzu haka ya gudu, ya nemi mu kawo masa wani bangare na jima’i a kan kudi Naira 500,000, ”in ji shi.
“Don haka, na tattauna da wani abokina wanda ake kira Musa wanda ya shawarce ni da in guji Wada. Washegari, yayin da nake shago ina aikin kanikanci, sai na hadu da Wada a gareji. Sannan ya bani wata (laya), wanda na jefa a cikin aljihu. Daga baya, mun sake haduwa da shi inda ya ce in raka shi zuwa wani wuri da ake kira Kwata.
“Lokacin da muka isa yankin, mun ga ‘yan mata biyu a wani wuri. Muka tsaya mun kira su. Wada yanzu ya cire wani kyalle daga aljihunsa ya haska shi a fuskar daya yarinyar, inda nan take yarinyar ta fadi, sai ya dauke ta zuwa cikin wani gini wanda ba’a kammala ba, kuma ya cire kayanta, kamar yadda Malamin dubar ya umurta. ”
A yayin haka kuma, Kakakin rundunar ‘yan sanda na Bauchi, DSP Ahmed Mohammed Wakil ya fada wa PRNigeria cewa nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan sun kammala bincike.