Duba da halin da matasa suka tsinci kai a cikin musamman na rashin ayyukanyi, hakan tasa muka rungumi tsarin sabunta sana’ar Wal’ada domin goyar da matasa wannan sana’ar Kire kire a Kasuwar Kofar Ruwa dake Jihar Kano, jawabin haka ya fito daga bakin Sunusi Safiyanu (Dan Kasuwa) a lokacin da yake yiwa Jaridar Leadership Ayau karin haske kan gagarumar nasarar da aka samu tun lokacin da suka kafa wannan wuri. Yace munyi dogon nazari tare da tunani kan abubuwan da ya kamata mu bujiro dasu domin amfanin al’umma tare da tallafawa kokarin Gwamnatin Jihar Kano Karkashin jagorancin Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje na kakkabe matslaar zaman kashe wanda a taksnain matasan JIhar Kano..
Safiyanu Dan Kasuwa yace wannan sana’a ta kere-kere ta hada da yadda muke sarrafa karafuna wajen fitar da fasalin kofofi da taguna, abubuwan zama da kayan karatu da suka hada da tebura da kujeru, wannan kuma shi ne abinda ke baiwa matasa sha’awa har suke mayar da hankali wajen ganin sun koyi wannan sana’a wadda muka hakkake alfanunta nada yawa ga matasan wannan lokaci.
Babbar matsalar wasu daga cikin yaran bahaushe shi ne son ci a huce, wadda kuma alokuta da dama hakan ce ke haifar da tsintar kai cikin sana’ar damfara, sace sace da munanan dabi’u. saboda haka ganin muna da wadatattun matasa masu fikirar da horo kadan suke bukata su zama abin amfani ga al’umma, Wannan tasa muka yanke shawarar sabunta tsarin daga yadda aka gada iyaye da kakanni.
Daya ke tsokaci kan irin nasarorin da suka samu cewa ya yi, yanzu haka wadannan kayayyaki da muke sarrafawa har daga makwabtan kasashe ake zuwa ana saya, musamman makwabtanmu daga Nijar wadanda muke musayar fasaha dasu, su kawo irin kayan da suke amfani dasu, mu sarrafa masu shi ta yadda zasu kawatar da al’umma, suma kuma suna koyi namu domin shigar dasu tasu kasar. Wannan ya bamu damar kyautata dadaddiryar alakar dake tsakanin Nijeriya da Njiar.
Da ya waiwaya bangaren Gwamnati, Alhaji Dan Kasuwa ya jinjinawa Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje bisa yadda yake tiri tiri da duk wata sabgar koyon sana’un dogaro da kai, wadda muna jin dadin yadda Gwamnatinsa ke bamu tallafi aduk lokacin da bukatar hakan ta taso.
A karshe Auwal Khalid Dahiru (Mai Kama) ya bayyana cewa akwai kalubale da ake fuskanta, musamman wajen mu’amalar raba kayan aiki da batun tattara kudaden kayan, wadda alokaci da dama ake samu wagegen gibi wajen dawo da jimlar kudin kayan da wasu suka karba, hakan tasa muka sauya tsari wanda kuma zuwa yanzu kwalliya ta biya kudin sabulu. Musamman ganin daga cikin yaran da muka horar akwai wanda yanzu likkafa ta yi gaba suna kasar waje suna ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau kullum.