Muhammad Maitela" />

Yadda Mukaddashin Gwamnan Borno Ya Dare Gadon Mulkin Jihar Na Riko

Borno

Mukaddashin Gwamnan jihar Borno, Umar Usman Kadafur ya dare bisa kan gadon mulkin jihar Borno dam, biyo bayan bukatar da Gwamna Zulum ya mika wa zauren majalisar dokokin jihar wajen amince wa mataimakinsa rike mulkin jihar na tsawon kwana 21 a hutun kwana 21 da ya dauka.

 

Bugu da kari, bincike ya nuna cewa Kadafur ne farkon mataimakin Gwamnan da ya samu amincewar majalisar dokoki cikakken iko a doka ya gudanar da mulki kwatankwacin Gwamna.

 

Wanda tun daga wannan lokaci, Umar Kadafur ya samu cikakkiyar damar gudanar da mulkin jihar tare da hadin gwiwa da jami’an tsaro, a lokacin bikin sallah da sauran ayyukan yau da kullum.

 

Sabanin sauran jihohin arewacin Nijeriya, sannan duk da yadda yake yau kimanin shekaru sama da 10 jihar Borno ta na fuskantar hare-haren yan ta’addan Boko Haram. Haka kuma, dangane da yadda ake ci gaba da kai hare-haren mayakan Boko Haram a wasu garuruwa da kauyuka, a nan ma mukaddashin Gwamnan ya dauki kwararan matakan hada gwiwa da jami’an tsaro domin samar da cikakken tsaro a lokutan bukin sallah.

 

Ko a ranar 13 ga watan Mayun 2021, mukaddashin Gwamnan jihar Borno, Umar Usman Kadafur ya jagoranci manyan jami’an gwamnati hadi da sauran al’ummar musulmi domin gudanar da Idin Karamar Sallah a farfajiyar filin Ramat a birnin Maiduguri.

 

Yayin da mukaddashin Gwamnan, bayan kammala sallar Idin ya mika gaisuwar sallah ga al’ummar jihar Borno tare da yaba wa jami’an tsaro a jihar dangane da kwazon samar da tsaro da kiyaye doka, tare da sadaukarwar da suka nuna a yaki da matsalar yarrow.

 

Har wala yau, a ranar sallar mukaddashin Gwamnan, wanda bisa yadda yake ga al’ada ya karbi gaisuwar girmamawa daga yan majalisar zaryaswa tare da sauran manyan jami’an gwamnatin jihar, a gidan gwamnatin jihar.

 

A hannu guda kuma ya karbi ziyarar gaisuwar Shehun Borno, Mai Martaba Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi a sa’ilin da ya kai waukaddashin Gwamnan ziyarar Sallah. Wanda bisa ga al’ada hakan yana gudana a kusan kowane sarakunan gargajiya kan kai wa Gwamna na lokacin gaisuwar sallah.

 

Wanda a wannan lokacin ziyarar sallah mukaddashin Gwamnan ya sake bayar da tabbacin bunkasa samar da tsaro tare da inganta rayuwar yan gudun hijira a jihar.

Exit mobile version