Connect with us

LABARAI

Yadda Mutum 1,500 Ke Rayuwa Da Bandaki Uku A Kauyen Tafawa Balewa

Published

on

Lamarin da ban mamaki, a yayin da al’ummomin kauyen Tsohon Fada da ke kusa da kauyen Kutaru a karamar hukumar Tafawa Balewa wanda adadinsu ya haura sama da 1,500 su ke rayuwa da bayan gida ‘Masai’ guda uku kacal.

A gefe guda kuma suna da rijiya guda daya ne tak da kuma fanfon tuka-tuka guda daya, inda mafiya yawan al’umman kauyen ke yin kashi a bainar jama’a wanda hakan ka iya jawo musu cututtuka da dama, a daya barin kuma babu asibiti koda ta shan magani ne.

A wani zagayen da  hadaddiyar kungiyar farar hula ta NEWSAM mai rajin samar da ruwa mai tsafta da kuma muhalli mai inganci hadi da tsaftar jiki, ciki har da ‘yan jarida wato ‘WASH’ suka yi a wasu kauyen da ke cikin garin Bauchi a makon jiya, kungiyar ta zagaya domin ganin halin da jama’an kauyeka ke ciki kan tsaftar ruwa da na muhalli.

A kauyen Kuratu da ke karamar hukumar Tafawa Balewa jama’an kauyen sun nuna gayar damuwar da suke ciki kan sha’anin ruwa da na tsaftar muhalli, inda suka shaida yanayin da suke rayuwa da cewar zancen babu dadin ji.

Sarki Bozo wanda shine Sarkin kauyen Kutaru ya shaida mana yadda suke rayuwa kan tsaftar muhalli da bayan gida, kafin hirarmu ta yi nisa, ya ma bayyana cewar hatta shi kanshi a matsayinsa na Sarki gidansa babu bayan gida, inda ya shaida cewar sukan shiga daji ne kawai su yi kashi.

Ya ce, “Adadinmu zai haura dubu 1,650 da muke rayuwa a wannan kauyen na Kutaru, muna da rijiya guda daya ne tak da kuma fanfanon tuka-tuka guda daya tak. A da fanfon tuka-tuka guda uku ne amma biyu sun lalace sai ya zamana saura guda daya ne tak ke aiki.

“Akalla gidaje sama da 150 ne a wannan kauyen muna matukar shan wuya na samun ruwa. Idan ka zo kauyen nan da rani sai ka tausa mana, domin wahalar da muke sha kan neman ruwa ba magana,” A cewar Sarkin Kuratu

Ya kara da cewa, “Ni da iyalaina idan muna jin kashi muna shiga cikin jeji ne mu yi; kuma kusan dukkanin gidajen da suke kauyen nan haka muke yi, gidajen da suke da masai a cikinsu basu wuce goma ba, wasu din ma sun lalace,” Inji Boso

Baba Boza ya kara da cewa, “Muna neman agajin hukumomin da abun ya shafa su tausaya mana su dubi yadda muke rayuwa domin kawo mana dauki; tabbas bamu jin dadin yadda muke fama da kuma shan wuya kan sha’anin ruwa,” Kamar yadda Sarkin ya shaida

Shi ma wani mazaunin kauyen na Kutaru mai suna Birsu Mato ya shaida yadda suke cikin ukuba kan sha’anin ruwa da tsaftar muhalli, “ba za mu iya sanin adadin yaran da suke rayuwa a wannan kauyen ba; amma mu manya mun haura 1,500, gidaje kuma za su dushi 150. Muna rayuwa ne a cikin wahalar ruwa sosai, domin a ce mana wannan adadin amma muna amfani ne da rijiya daya da kuma bohul guda daya tak; bayan gida ‘Masai’ babu a gidaje da dama,” Inji Birsu

Ya yi amfani da wannan damar wajen kiran gwamnatoci a dukkanin matakai da su kawo musu dauki domin ceto rayukansu daga kamuwa da cutattuka, “Ba mu da asibiti a wannan kauyen, idan mun samu rashin lafiya na mace ko na yaro mukan tafi Tafawa Balewa ne ko Zwul,” A cewar shi

Baya ga wannan kauyen, tawagar ta kuma sake nausawa kauyen Tsohon Fada da ke makwaftaka da kauyen Kuratu domin gano halin da suke ji, lamarin da za mu iya cewa ya fi na kauyen baya kazanta.

Mun zanta da Madaki Iliya, na kauyen Tsohon Fada ga kuma abun da ke cewa, “Da mazanmu da matanmu za mu kai dubu 1,500 da muke rayuwa a wannan kauyen. A dukkanin fadin kauyen nan rijiya ko kuma fanfanon tuka-tuka ko guda daya babu wanda wata gwamnati ta samar mana.

“Fanfon tuka-tuka guda daya ne tak muke dashi a wannan kauyen shi din ma mun roka ne a wajen wani tsohon shugaban karamar hukuma ita din ma yanzu haka bata wani aiki sosai,” Kamar yadda ya shaida

Dangane da bayan gida ‘Kashi’ ya shaida cewar suna yankar daji ne kawai su kewaya da su da iyalansu, inda yake bayanin cewar a dukkanin fadin kauyen gidaje uku ne kadal suke da bayan gida.

Ta yaya kuke rayuwa ta fuskacin samun ruwa? “Mukan je wani kauye ne mai nisa kusa da mu idan muna bukatar ruwa a can muke dibowa kullum haka muke fama. A zahirin gaskiya muna gayar shan wuya kan hidimar ruwa da kuma bayan gida, muna yin kashi a cikin daji amma muma hakan na damunmu.

“Sau tari idan ‘yan siyasa sun zo neman kuri’armu mukan shaida musu halin da muke ciki, sannan sukan yi mana alkawari amma da zarar suka ci ba mu sake ganinsu sai wani zaben kuma,” A cewar Iliya

Ya kara kuma da cewa, “Muna son mu bayyana wa gwamnati halin da muke ciki amma bamu samu zarafi ba; muna rokon don Allah indai ana gwamnatin adalci ne a zo a duba yadda muke rayuwa a cikin kauyuka domin a inganta mana rayuwa,” Inji Madakin kauyen

Shugaban tawagar Media na shirin WASH a jihar Bauchi, Mista Devid Ayodele ya ce babban hikimar da ke cikin wannan zagaye domin duba halin da jama’an kauyuka suke ciki kan sha’anin ruwa da tsaftar muhalli shine domin a fadakar da su don su nemi hakkinsu a wajen ‘yan siyasa na tilasta musu kan su inganta musu sha’anin ruwa da tsaftar muhalli.

Jami’in ya bayyana cewar dazarar aka kyautata sha’anin ruwa da na muhalli hakan zai kawo raguwar kamuwa da cutattuka da ake mafa da su a cikin al’umma, don haka ne ya bayyana cewar sun kaddamar da wani kamfen mai suna ‘Bote4Wash’ wanda ke kiran jama’a su yi amfani da kuri’arsu domin a kyautata musu harkar ruwa da na muhalli, “idan muka dauki kuri’armu a matsayin hanyar da za a kyautata mana sha’anin ruwa da tsaftar muhalli, shi kenan sai mu zabi dan takarar da muka gamsu ya mana alkawarin idan ya ci zai inganta mana sha’anin ruwa, a dukkanin mukaman siyasa ne kuwa, kama daga dan majalisar jiha, tarayya, sanata ne ko gwamna mu tabbatar mun zabi wanda zai kyautata mana sha’anin ruwa da tsaftar muhalli,” in ji shi.
Advertisement

labarai