Connect with us

ADON GARI

Yadda Mutuwar Aure Ke Yi Wa Al’ummar Hausawa Kisan Mummuke…

Published

on

Assalaamu alaikum, barkanmu da sake saduwa a wannan shafi namu mai albarka; cikin wannan jarida tamu mai farin jini da daukaka, wato Leadership A Yau. Idan ‘yan’uwa ba su manta ba, a sati biyu da suka gabata mun faro bayani ne a game da yadda mutuwar aure ke wargaza tarbiyyar yara.
Ko shakka babu, kusan halin da a yau al’umma ta samu kanta a ciki, na tabarbarewar tarbiyyar matasansu da lalaci da kaskanci, wajibi ne a alakanta hakan da mace-macen aure, domin kamar yadda muka ambata a baya, ‘ya’yan da iyayensu suka rabu suna rayuwa ce ta garari, domin za ka iske ba su da wani takamaimai matsuguni, sawa’un matan ne ko kuwa mazan ne. Wannan kuwa ya faru ne a sakamakon duk lokacin da saki ya ratsa gida, kuma ya kasance suna da yara. To uban ba damuwarsa ba ce ya dauki yaran, zai bar wa matar da ya saka din ta kwashi yaran ta tafi da su, ko da kuwa babu wani kebantaccen daki da yaran za su zauna a gidan su uwar tasu. Idan aka yi rashin dace, auren mace ya mutu alhali tana da yarinta ko budurwa, kuma ya kasance gidan su ita uwar babu daki, sai ka ga an bar ‘yar ta koma kwana a gidan kakarta, ko kuma ta wuni a gidan su uwar tata, da dare ta tafi gidan ubanta ta kwana. A irin wannan yawace-yawacen wuraren kwanan ne akan samu batagari cikin samari su lalata yarinyar, ko da yardarta ko kuma ta hanyar fyade. Wani abin takaici, uban da ya yi cikin samun wannan yarinya ko yaro ko kuma yara, dukkanin wani nauyi na dawainiyarsu ba damuwarsa ba ce! Bai san cin su ba, bai damu da shan su ba, bai kuma damu da lafiyarsu ba. Shi bukatarsa ko damuwarsa ba a kan yaran yake ba, yana kan al’amuransa na rayuwa.
Sau da dama aure kan mutu, mutuwa ta gangan, za ka iske sababin da ya sanya mutuwar aure sababi ne wanda inda an yi hakuri da zai fi alheri. Sau da yawa, namiji kan saki matarsa bisa hujjar ta masa laifi, wannan laifin ma kila bai taka kara ya karya ba. Amma a hakikanin gaskiya idan ka bincika wata ya gani a waje kuma yake son auren ta, kuma ga shi ba shi da muhallin da zai ajiye mata biyu. Don haka zai saki wannan matar domin ya auro wadda yake so, kafin ita ma daga baya ya ci moriyar ganga…… Domin da zarar ta haihu, shi kenan wata zai hango. Haka wannan al’amari ke gudana tsakanin al’umma a yau, uba ya san jima’i, ya san ya yi wa matarsa ciki ta haihu, amma fa bai san tarbiyyatar da yaran na rataye a wuyansa ba. Da a ce uwa a wani dare za ka iske ta ki amincewa mijinta, zai yi ta kokarin kawo mata dalilai na haramcin hakan, idan shi din ma’abocin addini ne, ko kuma yana da sanin hakan. Amma fa sau da yawa bai san kula da yaran shi ne mafi muhimmanci sama da wannan abin da ta hana shi.
Yara tarbiyyantar da su wajibi ne, dole ne a kula da su a kuma kyautata musu rayuwa, har ya kasance sun zama abaiban alfahari a tsakanin al’umma, su kasance ‘ya’yan da Annabi S.A.W zai yi alfahari da su ranar Kiyama a gaban sauran annabawa. Domin muhimmancin tarbiyya ce, Ubangiji ya tanadi tsananin azaba ga wadanda ba su kare kawunansu daga wuta ba. A gefe guda kuma, ba ya halatta a samar da yaran da za su zama fitina a tsakanin al’umma, zai zama babban laifi, a wani lokacin ya zama sababin shigar mutum wuta, matukar ya samu yaran da bai tarbiyyantar da su ba. Shi ya sa Manzon Allah S.A.W ya bayar da ceto ga wanda yake da yara mata biyu, kuma ya tarbiyyantar da su, ma’ana Manzon Allah S.A.W ya tsaeratar da irin wannan mutumi daga wuta.
Idan muka yi tsinkaye cikin batutuwa na, za ku yarda da ni cewar lalle ana haifar yara, amma ba a iya ba su tarbiyya, ana tauye hakkoki nasu. Kenan wajibi ne a samu wata hukuma ta musamman domin dakile wadannan abubuwa, wato ba wai a hana saki ba, a’a, a tilastawa dukkanin wani uba da ya rabu da matarsa lalle ya dauki yaransa ya rike su, kuma a tabbatar yana kyautata rayuwarsu da tarbiyyarsu daidai karfinsa. Amma matukar za a zuba idanu a bar jama’a suna irin wannan rayuwa, wallahi ba za a rabu da samun ‘yan kwaya, da masu fyade da yara kanana masu luwadi ba.
Kamar yadda muka fada, ‘ya’yan da iyayensu suka rabu, ba su da takamaiman muhalli, wannan ba boyayyen abu ba ne, yau suna nan gobe suna can. Ba su da wanda ke bibiyar matsalolinsu, domin ita uwar tana ta kanta, idan kuma tana gidan wani ne, to shi ma ba zai yarda da dawainiyar ‘ya’yanta ba. Don haka, irin wannan dama da yara ke samu dole su shiga ko su kulla alaka da bata-gari, ko kuma a lalata musu rayuwa cikin karfi da yaudara.

Zan ci gaba insha Allah.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: