Connect with us

RIGAR 'YANCI

Yadda Na Fanshi Kaina Daga Masu Garkuwa – Hakimin Tungar Malam

Published

on

A Ranar Lahadin makon da ta gabata ne masu garkuwa da mutane suka kai farmaki a garin Tungar Malam da ke a karamar hukumar mulki ta Suru a jihar kebbi, inda suka  tarwatsa mutanen garin  da harbin bindiga kirar AK47 kafin yi awon gaba da Hakimin Tungar Malam mai suna Alhaji Ibrahim Sarkin Yaki suka kuma tabkawa matansa duka kafin suka wuce dashi zuwa cikin dajin Gwauron Dutsi inda suka yi garkuwa dashi Hakimi Alhaji Ibrahim Sarkin Yaki har tsawon kwanaki hudu a hannu, in ji Hakimi Alhaji Ibrahim Sarkin Yaki.

Wakilin LEADERSHIP A YAU ya yi tattaki zuwa garin na Tungar Malam don binciken gaskiyar faruwar lamarin inda yayi tarar da Hakimain garin ya samu fansar kai sa a hannun masu garkuwa da mutanen ga abin da   Hakimin garin ke cawa” a ranar Lahadi ta makon da ya gabata masu garkuwa da mutane suka kawo farmaki a garin Tungar Malam da misalin karfe 2 na dare suka shigo gida na kawai sai suka fara dukar mata na da kuma harbin bindiga ta ko ina, inda suka nemi in bada kudi sai na ce babu kudi a hannun amma bari in sa a kawo kudi sai kawai suka ce tun da babu kudi zama wuce da kai, daga nan sai suka tasa ni gaba muna tafiya a cikin dajin Gwauron Dusti har tsawon sa’o’i biyar muna tafiya idan nagaji sai a duke ni har gari yawaye mu na tafiya kafin muka kai inda suka ci gaba da garkuwa da ni”.

Haka kuma Hakimi Alhaji Ibrahim Sarkin Yaki ya ci gaba da cewar ” yayin da masu garkuwa da mutane suka dauke ni  daga gida na zuwa inda suka ci gaba da garkuwa da ni sun sanya mani wani kyalle suka rufe  huska ta  domin suma suna sanye da wannan kyalle a faskokinsu mai launin  baki sai muna ta tafiya inda suka sanya ni a tsakiyarsu mutun Takwas dukkan su na dauke da bindiga kirar AK47 sauran bindigogin na cikin buhu, inji shi”.

Haka kuma ya ce, “yayin da suka dauke ni daga gida na ashe sun bar layin waya kusa da gida na inda suka sanya shi bisa wani dutsi sai suka kewaye wurin da wani jan kyalle da kuma sanya hakin ganye a tsakiyar dustin , bayan gari ya waye ne mutanen garin na tare ‘ya’ya na suka biyo hanyar cikin daji don neman inda aka bi da ni”.

Daga nan ne sai daya daga cikin yarana yagan wannan wuri da suka sanya layin waya sai ya dauka ya sanya shi a cikin wayar sa ta hannun bayan kwanaki uku sai masu garkuwa da ni suka kira layin da suka bari sai yaro na da ya gan layin sai ya dauka inda yayi magana dasu na cewar su  kawo Naira Miliyan Hudu kafin su saki ni ko kuma su kashe ni .

Bisa ga haka ne yara na suka samo Naira Miliyan Biyu domin su kaiwa masu garkuwa da ni a matsayar kudin fansa, inda  suka nemi a kai kudin a wani  gun inccen wutar lantarki  wato ( Electric pual wire)  a  kusa  kwanar Gwauron Dusti da ke a Babban Titin mota mai zuwa garin Dakingari da kuma Bunza don aje Naira Miliyan Biyu din kafin su iya sako Hakimi Alhaji Ibrahim Sarkin Yaki.

Bayan an Kai kudin sai Hakimi Alhaji Ibrahim Sarkin Yaki ya samu ‘yancin kansa, inda ya kara da cewar ” bayan sun sake ni suka tabba mani cewar sun sake ni ne bisa ga sharadin a kawo sauran kudi Miliyan Biyu ko kuma su koma dawo wa  su dauke ni, inji shi”. Har ilayau Sarkin Yaki ya ce ” mun sheda wa jami’an tsaro inda har DPO ya zo yayi mani jaje da kuma Shugaban karamar hukumar mulki ta Suru .

Ya kara da bayyana cewar ” bayan na samu ‘yancin kai na daga hannun ‘yan ta’adda sai tafi asibiti domin  jinya saboda irin dukan da suka tabka mani”. Yanzu dai tsoron da muke ciki a gari na shine cewa” muna neman gwamnatin da jami’an tsaro su taimaka muna don kada a koma samun irin wannan matsala”. Saboda ‘yan ta’addan nan sun ce idan ban kawo sauran kudi ba za su dawo garin. Don haka muna kara kira ga dukkan masu ruwa da tsaki kan harakar tsaro da su kawo wa mutanen garin Tungar Malam dauke.

Haka shi ma wani mazaunin garin  wanda  kuma shedun gani da ido ne mai  suna Alhaji Sa’adu ya ya soma da bayyana wa wakilinmu  cewa” Ina kwace da misalin karfe 2 da minti 11 na ranar Lahadin makon da ya gabata masu garkuwa da mutane suka shigo garin namu inda suka rika harbin bindiga ta ko’ina a cikin garin na Tungar Malam na fito da naji kuka a gidan Hakimi Alhaji Ibrahim Sarkin Yaki, amma saboda harbin bindiga sai na tsaya guri daya ina kallo ana dukan Hakimin mu ana tafiya dashi a cikin daji amma bana iya komi ga lokacin saboda mutanen na da yawa  kuma suna dauke da bindigogi tun ina ganin su har suka bace mani, inji shi “.

Yanzu hakan da nake zantawa kai idan dare yayi bamu kwana a cikin garin na Tungar Malam tare da matanmu saboda tsoron kada a kashe mu domin sun ce wa Hakimi zasu dawo .

Bisa ga haka kowanen mu daban daban muke kwana sai da safe sannan mu hadu da mu da matan mu domin a halin yanzu ban san inda matana da yara ke kwana ba. Bugu da kari ya ce ” muna kira ga gwamnatin da jami’an tsaro da su tamaika muna na kawo muna dauke a garin na Tungar Malam bamu da kudi kuma bamu da karfin iko sai Allah . Saboda” Don Allah a taimaka mu na a ceci rayuwarmu”.

Haka kuma wakilin namu kira shugaban karamar hukumar mulki ta Suru , Umar Maigandi don jin ta bakinsa kan wannan lamarin ta wayar hannu inda ya ce” Lalle wannan lamarin ya faru amma ba a garin Dakingari amma idan ku kara so Birnin-kebbi ku kira ni don bayyana Matakin da karamar hukumar ta dauka”.

Bayan ‘yan jaridu da suka ziyar ci garin na Tungar Malam don zantawa da Hakimi Alhaji Ibrahim Sarkin Yaki da abin  ya rutsa dashi sun kara so a Birnin-kebbi sun kira shugaban karamar hukumar mulki ta Suru kamar yadda ya bayyana a cikin wayar tarho, amma sai ya ki  bawai ‘yan jaridun damar zantawa da shi”.

Daga karshe wakilin namu ya samu jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar kebbi, DSP Nafi’u Abubakar inda ya  tabbatar da aukuwar lamarin ya kuma kara da cewar” yanzu hakan hukumar ‘yan sanda na iya kokarin ta na ganin cewar ta cafke wadannan ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane a yankin na karamar hukumar mulki ta Suru da kuma sauran wasu yankunan jihar ta Kebbi baki daya, inji shi DSP Nafi’u”.

Daga nan ya yi kira ga al’ummar yankin karamar hukumar mulki ta Suru dasu sanya ido ga abubawan da ke faru wa a yankunan nasu don bayar da bayanan sirri ga hukumar ta ‘yan sanda, don gudun sake aukuwa lamarin.

Advertisement

labarai