Yadda Na Kera Injin Keke-Napep Mai Amfani Da Hasken Rana – Wani Manomi

PASTO PAUL DANIEL wani mai basira ne da Allah ya ba shi baiwar sarrafa na’urori masu amfani da hasken rana. A baya ya kera na’urar ban ruwa mai amfani da hasken rana, yanzu kuma ya iya samun fasahar kera babur mai kafa uku (KEKE-NAPEP) mai amfani da karfin hasken rana. Manomi ne wanda ya ke da muradin kera abubuwa da da ma gaske. A bisa haka ne wakilin LEADERSHIP A YAU, KHALID IDRIS DOYA, ya yi tattaki har garinsu domin zantawa da shi. Ga yadda hirar ta kaya:

Ka gabatar wa masu karatunmu da kanka?

Sunana Pasto Paul Daniel, ina zama a karamar hukumar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi. Allah ya bani fasahar sarrafa na’urori da amfani da hasken rana, don ko a kwanakin baya na taba samar da Injin ban ruwa mai amfani da hasken rana, yanzu ga shi ne kera Keke-Napep mai amfani da hasken rana.

Ya ya aka yi ka samu basirar inganta wannan babur mai taya uku (KEKE NAPEP) da ke amfani da hasken rana maimakon fetur ko gas?

Da yake ina yawan amfani da abubuwan da suka shafi hasken rana yawanci ina sha’awar abin da ya shafi hasken rana ‘Solar Energy’ saboda ina gani wannan abu ne da Allah ya kawoshi don ya sauwaka wa jama’a wahalhalu da kuma tsadar rayuwa, kan haka ne cikin tunanin da na ke yi, na ke tunanin cewa da ya kamata a duk duniya a ce duk injin da yake amfani da Mai a daina amfani da shi a koma amfanin da na’urar hasken rana musamman kan duk wani inji mai motsi.

Shi ne ya kaini ga tunanin cewa bari in fara da Keke-NAPEP  don in ta dauka wato ya nuna kenan duk wani abu da ke amfani da inji da mai to za a iya amfani da hasken rana kuma a samu biyan bukata. A lokacin da wannan basira yake shigo mini ban sa tsammanin zan iya samun wadannan kayayyakin a nan ba, a hankali a hankali dai ina harhada kayayyakin da zan yi aikin harzuwa lokacin da na zo na sadu da wani kwararre, mutumin kasar Sin wato kasar (China), sai na tura masa irin tsarin da na yi na wannan Keken.

Shi kuwa sai ya ce mini, idan har ina so in yi amfani da wannan abin inji dadinsa zai bani shawara inyi amfani da irin nasu fasahar in gwada in gani, domin dama shirina ina so ne in yi amfani da naurar sarrafa fanka wanda za a iya kara mata gudu ko a rage mata gudu. maimakon Totur shine ya ce a’a shawarar da zai bani in yi alaka da kamfaninsu za su iya turo min Totur din  da su suka yi na irin wannan harkar, da muka daidaita sai ya turo mini, sai na biyashi kudin, daga baya sai na zo na gwada na ga yayi, shi kansa ma ya yi ta mamaki ya dauka sai wani ya zo ya koya mini, na ce masa a’a ai wannan abin dama tuntuni ina da basirarsa babu kayan aikin ne kawai da tuntuni ban hada irin wannan ba sai wannan lokacin.

Ga shi mun ga ka cire dukkan Injunan da ake sawa cikin Keke NAPEP, ka saka wadansu irin na’urorori masu kamar batura sun cika wajen sun zauna daidai menene ka cire ko menene ka yi?

Wato Inji ne kawai na cire, amma na bar karafan Sharp da ke juya tayoyin bayan Keke NAPEP din, ban cire su ba, sai na je wurin masu sarrafa na’urori na nuna musu irin tsarina da a bin da nake so, na ce su hada mini ‘sharp’ da sarka da wasu abubuwa, sai na kawo wani abu da ke da suna ‘DC MOTOR’ wanda shine abin da ke amfani da wutan hasken rana din, sai na daura bayan na hada kuwa na sata a hanya na jarraba ban ga ta nuna wata damuwa ba.

Ta wacce hanya ka ke yin cajin batur din Keken?

Wannan batur din mai amfani da hasken rana ne idan akwai faifan da ke tara hasken rana (Solar Panels) ina diba na dorasu na hada su da faifan da ke tara hasken rana za ta iya ta yi caji cikin awa biyu ko uku. In kuma ta yi cajin nan to za ka iyayin awa shida kana aiki ita, saboda in ta yi awa shida sai ka sake caji, amma in kana da faifan da ke tara hasken ranan a samanta za ka rika yin aiki har dare in dare yayi kuma tunda ba hasken rana sai ka koma kan cajin batur din da ka yi, ka yi ta aikinka da shi har zuwa lokacin da zai kare.  Kuma ka ga idan dare ya yi faifan da ke tara hasken ranan ba zai yi aiki ba, amma cajin da ka yi shine zai maka aiki har na tsawon awa shida.

Na ga faifan naka da yawa kuma kamar baturan da ke caji da hasken ranar ma da yawa me za ka ce?

Eh gaskiya ne ya kamata ne asa faifan da ke tara hasken rana wato (Solar Panel ) da kuma baturan guda shida ne, in ana so ta yi karfi sosai, ko wannan da na yi yanzu guda biyar ne nasa amma shi ma yana da karfi sosai don ranan da na hada katti mutane goma sha biyar suka hau kuma ta yi tafiya da su, ka ga za ta dauko kayan amfanin gona da yawa kenan. amma karfinta da gudunta da yawan kayan da za ta dauka in aka sa guda shidan ya fi guda biyar din, akwai wanda ya yi karatu a kasar Sin ya ce koda babbar kwatarniyar daukar kaya ‘Truck’ muka dora a bayanta za ta dauki hatsi manyan buhunhuna guda bakwai kuma ta ja, ka ga wannan ba karamin sauki ne ga manoma ba.

Wani sauki za a samu da amfani da wannan keken sabinin wacce take amfani da Mai?

Saukinta shi ne wato duk abin da kake amfani da Mai ka ga akwai rigima da yawa, ka ga in ana karancin Mai ko ka na da kudi ma ba za ka samu ka saya ba, in neman kudi ka ke yi da ita duk abin da ka samu tilas sai ka cire na Mai ka ajiye, idan wannan namu din ne kuma babu ruwanda da wannan batun. Wannan mai amfani da hasken rana ba za ka yi mata juyen bakin mai ba, ba ruwanka da shan Man fetur, abinda kawai zai hau kanka shine ka samu ruwan birki ka rika sawa, sannan bayan sati biyu ko uku ka sa masa Man giris a wuraren da ke dan motsi-motsi, ka ga man giris din nan bai wuce naira 200 ba, kuma ka ga za yi wata daya ko biyu ma kana amfani da shi. akwai sauki sosai a ce kana ta hawan abin hawanka ba ka biyan kudin Mai kudin juyen bakin Mai, kuma  ka huta da Kananun gyare-gyare da sauransu, ba ta hayaki ba ta diri sai dai ka danna oda wato (horn).

Irin wannan guda nawa za ka iya yi a rana?

Idan akwai kayan aiki irin wannan za a iya yin guda goma zuwa ashirin amma in ba kayan aiki to sai ka ga kana ta fama ka nemo wannan ka nemo wancan.

Idan mutum na son ya mallaki wannan keke-napep din nawa zai tanadar?

Ba ta da wani tsada kusan dukkan kudin da ake iya sayan Keke NAPEP da shi  za ka iya sayan wannan ma da shi, wato takan kama daga dubu 450 zuwa gaba bisa ga irin girmanta da hadin da aka mata akwai ma har dubu 700 ana samu, kuma tsadanta ya dogara daga yanda kake yin oda a kawo maka kaya ka ga misali kamar ‘DC MOTOR’ wannan na’ura idan ka yi odansu da yawa to yin haka zai sa ka samu saukin kayan amma in kwaya dai-daya kake saya sai ka ga kana sayansa da dan karen tsada, kuma dalilin da ya sa za a a ga kamar yana da tsada saboda wadannan kayayyakin ba a nan ake samowa sai an fita kasar waje. Amma ya kamata gwamnati ta shigo ciki tasa hannun wannan kwararre mutumin kasar Sin din nan ya ce mini a kasarsu duk wata masana’anta da suke amfani da hasken rana ana ba su tallafi daga gwamnati.

Su a can suna samu da sauki, wata matsalar da ake samu shine bayan ka sayi kaya kudin dauko kayan ya fi kudin kayan tsada, kuma ko mu ki ko mu so wadanda suke sayan Manmu nan da shekaru 20 suna iya raguwa da yawa koma su daina saya, yanzu akwai kasashen da suke so su yi doka cewa bayan shekaru 20 ba su son su ga mota mai amfani da mai kan titinsu.

A baya ka yi Injin ban ruwa mai amfani da hasken rana domin noman rani, ko akwai gudummawa da goyon baya da ka samu don ci gaba da yin wannan aiki?

Abin dai kadan-kadan muke tafiya har yanzu, ba mu yi da yawa ba, amma muna kan tattaunawa da wasu domin a yi da yawa yanda manoma za su samu, domin yinsa da yawa tilas sai an tanadi dukkan kayayyakin da ake bukata da yawa kuma kayayyakin ba a nan ake samunsu ba sai an yi odan su, shi ya sa dole ne sai an hada guiwa an samo da yawa sai a sameta a cikin sauki yadda ba zai yiwa mutane nauyi ba.

Kana hasashen nan gaba za a iya yin irin wadannan keke-napep din da yawa kuwa?

Eh, akwai tunanin a yi su da yawa don na ga irin wahalan da  muke sha wajen amfani da duk wasu kayyakin Inji da muke amfani da su don tilas sai ka yi amfani da Mai kuma lamarin na kawo tsadar rayuwa sosai, ina da tunanin cire Injin mota ma in yi Mai amfani da hasken rana da batur kawai tsalla ina fatan nan gaba kacan na samu cimma wannan nasarar tawa.

Ya zancen kargon baturan da ake wannan amfanin da su?

Gaskiya su baturan Solar suna dadewa sai dai in mutum bai sayi mai kyau ba amma in mai kyau ne zai yi shekara biyar ana amfani da shi bai lalace ba.

Kana da karfin jarin yin wadannan ayyuka kuwa?

A gaskiya bani da shi da ina da shi da na yi wadannan abubuwa da yawa na sa su a hanya don su ke samar wa jama’a da saukin rayuwa, amma yanzu babu karfin jari, kana ji kana gani ga mutane suna shan wahala kana da hanyar taimaka musu ba ka da ikon taimakawa don ba jarin, sai dai ka zuba ido amma inda za mu halin da zamu yi su da yawa, inda ana daukan mutane ne akan naira dari ka ga in ka sa aka samu ragin naira 50 ka kawo sauki ga al’umma, saboda haka ne anan ina kira ga gwamnati da masu kasuwanci gwamnati ta taimaka tasa hannunta kan wannan sana’a da in aka koya wa yara zai taimaka musu rage zaman banza. Kuma al’umma za su sami sauki kwarai da gaske, don duk jarin da mutum ke da shi in baya sayan Mai to ya fi kowa samun sauki.

Me kake son gwamnati ta yi maka?

Ina so in roki gwamnati da ta tallafawa talakawa tasa hannunta cikin wanan abin idan aka sami sassauci za a samu nasara sosai mutane za su sami sauki, kuma za mu iya bai wa matasa horo don su koyi yanda za su yi wannan sana’a zai taimaka wajen  rage matsalar rashin aikin yi a tsakanin al’umma.

Exit mobile version