Nasir S Gwangwazo" />

Yadda Na ‘Saki’ ’Yan Fim Na ‘Auri’ ’Yan Hiphop –Farfesa Abdalla

A cigaba da tattaunawa ta musamman da Editan LEADERSHIP A YAU LAHADI, NASIR S. GWANGWAZO, ya ke yi duk mako da mashahurin farfesan nan a Arewacin Najeriya, kuma mai binciken da ya zama tamkar wani rumbun adana tarihin al’adar Bahaushe a zamance, wanda a yanzu shi ne shugaban jami’ar NOUN, FARFESA ABDALLA UBA ADAMU, a makon jiya mun tsaya ne a inda ya ke bada labarin irin kalubalen da ya fuskanta da ’yan fim din Hausa. Za mu dora daga inda mu ka tsaya. A dai sha karatu lafiya:

Kai, sai da gwaggona na ta bugo min waya watarana da wani ya zage ni a Freedom Radio ta ce, ‘ka rabu da wadannan mutanen’. Na ce, ‘to shikenan na rabu da su’. Sai na tattara abin duk na watsar! Saboda haka ko mutum ya gayyace ni ya ce wai ya yi fim ga shi na duba, sai na ce ‘ba zan duba ba, ka saki fim dinka a kasuwa. Idan Allah Ya taimake ka ya samu nasara, ya samu nasara kenan. Idan bai samu nasara ba, kai ka yi asara, amma ba zan duba ba’. Don idan na bude baki na yi magana, sai a ce kaza da kaza. Idan a ka zo za a kaddamar da fim sai a ce wai mu zo, sai na ce ba zan zo ba. Akwai wani fim da a ka yi Hindatu (Hindu), a ka matsanta lallai-lallai sai mun zo, na ce mi ba zan zo ba, saboda idan mu ka zo mu ka yi magana, sai a ce ai mun san da ma Farfesa ba son mu ya ke ba. Duk dai irin wannan surutan!

Amma a ka dai takura min a kan sai na zo! Na ke jin Baharu ne ma ya matsanta ya ce sai na zo. Na ce ‘to’. A ka je a ka yi ma na tirela a Film House, sai a ka ce me za ku ce? Sai na ce ni fa ba zan magana a nan ba. Ado (Gidan Dabino) ma ya ce ba zai magana ba. A ka ce ‘a’a, wannan ai dalilin da ya sa don a yi gyara a yi mene ne. Na ce ‘to shikenan’, na tashi na ce, kuskure na farko ita jarumar an nuna ta na cin ‘apple’, ba a nuna ma na cewa ‘apple’ ba kayan marmari ne da a ke sayar da shi a kasuwar wannan kauye a wannan lokacin ba kuma a na maganar lokacin da babu karfe ma a gidan, ballantana a ce wai har an shigo zamani. Komai da kasko a ka yi shi ko da ice, sutura na saki ne, amma sai ga shi ta zauna ta na gatsa ‘apple’, wanda babu shi a lokacin a kasar Hausa. Na ce ‘amma za ku iya amfani da yalo ko data ko goruba ko agwaluma ko dai wani abu da mu mu ke da shi tun a da. To, sai daga baya wani ya ke gaya min ya ce, a cikin taron wani daga can baya ya na zaune kusa da shi ya ke cewa, ‘ka gani ba! Da ma mun ce Farfesa sai ya kalubalance mu, sai ya zage mu’. To, Ado shi ma ya tashi ya yi nasa raddin.

 

An ce kun kalubalanci sunan fim din ma.

To, shi kansa Hindu ya na nufin wacce ta zo daga Indiya. Ya za a yi ka ce sarauniyar kasar Hausa ta shekara wajen 300 da ta wuce wai an kira ta Sarauniyar Indiya, alhali ba mu fara ganin abin Indiya ya zo ma na nan wurin ba sai lokacin da Turawan mulkin mallaka su ka zo su ka fara nuna ma na finafinai! To, ya za a yi daga sunan an kira mace ’yar Indiya? Ai abinda ya ke nufi kenan Hindu; Ba’indiya, wacce ta zo daga Indiya. Meye amfanin haka? Me ya sa ba a kira ta Laure ba ko Jummai ko dai wani suna da za a tabbatar cewa a kasar Hausa a ke? To, Mai girma Aminu Ado Bayero (Wamban Kano) shi kuma ya tashi ya ce ai kwata-kwata ba a bi tsarin sarauta yadda ya ke ba. Ya ce ‘kamata ya yi masu fim idan za ku yi fim a kan sarauta ku zo gidan sarauta ko ku zo ku samu wadanda su ka san sarautar su yi mu ku bayani. Kuma Aminu Ado digirinsa a ‘Mass Communication’ ya yi. Ka ga kuwa ba za ka ce bai san abinda ya ke yi ba. Ya ce, ‘ku zo a yi mu ku bayani, amma wannan duk abinda a ka yi ba daidai ba ne’. To, ka ji yadda surutun da hayaniyar su ka yi yawa, kuma da ma can Ina da sha’awar kida da waka…

 

To, ya ka riski wannan harkar wannan wake-waken Hiphop da Rap?

Akwai wani yaro a na kiran sa Abdullahi Mighty ya yi waka, shi ne na farko a cikin ’yan Hiphop da ya fara yin cd ya ke sayar da shi, sai a ka zo a ba ni kwafi. A lokacin British Council (Kano) su na gayyata ta a matsayin na dinga yi mu su abubuwa na ‘Cultural Communication’ wajejen 2001/2, sai su ka nuna su na sha’awar a dinga shirya wani taro tsakanin su da matasa. An yi a kan fim, an gama ‘Connecting Futures’, sai su ka yi a kan filmakers (’yan fim), sai a ka zo a ce kuma a kan kida. Lokacin da su ka su ka ce su na neman mawaka, mawaka sun fi dubu da su ka tarar mu su a gurin, har sai da malaman Kano su ka zo su ka ce da su su ba su yarda su shirya wannan abu ba. Sai su ka ce to za su dauki abin su kai Kaduna. A ka ga cewa Kano za ta rasa. To, su Britishi Council sai su ka rubuta mi ni wasika su ka ce su na so na zo na zama mai bada shawara a kan wadannan abubuwa, sai na ce da su, ‘to idan haka ne ga yadda yakamata ku fito da abin; maimakon ku kyale kowa ya zo ya yi, ku dinga hada shi da gargajiya. To, shi ya sa su ka ba ni dama na kira Barmani Coge, na kira Muhammad Dahiru Daura, duk mu ka kira su a ka yi ‘concert’. To, don a tallata ‘concert’ din ta gargajiyar sai mu ka kirawo mutane ’yan Hiphop wadanda za su jawo hankalin matasa a kan abin, saboda yaro idan ka ce yaro ya zo ya saurari Barmani Coge, sai ya ce ‘shi wannan yane?’ Shi bai gane wannan hayaniyar ba! To, amma idan ka ce masu budewar za su zo su yi dan tsalle-tsallensu da kaza da kaza a kan dandalin, to za su je. Ba mu kira ’yan nanaye ba, saboda ’yan nanaye idan banda soyayya babu abinda su ke yi a kai. To, saboda haka mu yaran da mu ke hari yara ne matasa, wadanda su ka san duniya. Lokacin a Britishi Council su na shiga intanet su na ganin su 2pak da sauransu. Don haka sai na ce bara mu samo waye ya ke yin irin wannan abubuwan? Sai a ka Billy’O. ban san shi ba, na je na nemo shi na ce ‘Billy’O, zo za ka yi ma na wasa’. Ya ce ‘to’. Ya zo kuwa ya hau dandali ya yi. A ka ce Shaba, shi ma mu ka nemo shi. To, a hankali da ya ke ’yan Hiphop din ba su da yawa sun san juna, sai a ka zo a ke samu na ‘don Allah mu ma mu na son a ba mu dama mu dan yi show’, sai na ce ‘ba zan biya ka ba’, sai su ce, ‘kyauta za mu yi’. Shikenan sai a ka yarda. To, ka ji a haka a ka tafi.

To, wannan dan ‘show’ din da su ke yi sai ya birge ni. Da British Council su ka rufe su ka daina komai da komai, ni sai na bi yaran. To, daya daga cikinsu shi ne Hassan K’Boys. A dandalinmu su ka fara yin wakarsu Kariya a kan cutar HIB. Shikenan sai na bi su na ke bin diddiginsu. Yadda dai na ke bin marubuta na dinga bin ’yan fim, amma ’yan fim ma da na bi maburuta ’yan fim ne, kamar Bala Anas, Ado Gidan Dabino, su Dan’Azumi Baba. Ba ruwana da wani; idan mutum harkar fim ya ke yi, amma ba marubuci ba ne, to babu ruwana da shi, amma idan marubuci kuma ya shiga harkar fim, to su na fi damuwa da su. To, haka wadannan yaran mawaka na rika bin su Ina karfafa mu su gwiwa. Idan sun kawo waka na saurara na ce wannan ya yi, amma ku gyara ku yi kaza-ku yi kaza, saboda Ina da sha’awar kidan. Ban da sha’awar na yi fim a lokacin, ban da sha’awar na yi wani rubutu, amma Ina da sha’awar kidan. To, shi ma fim din daga baya da a ka rika zagi na a na cewa mene ne-mene ne, sai na bari na yi ‘documentary films’ wajen guda goma. Duk sai na zuba su a Youtube kyauta kowa ya gani a ‘channel’ dina mai suna ‘Foundation for Hausa Performance Artiste’. To, haka mu ka rika bin yaran nan a hankali har a ka kawo yanzu.

Exit mobile version