Yadda Na Samu Kwarin Gwiwar Sana’ar Girke-girke Duk Da Ina Namiji – Abba Yero

Abba Yero

Wani matashi mai himma da hazaka da ya jajirce kan koyon sana’ar girke-girke kuma ya samu kwarewa, inda ake kawo masa ayyuka da suka hada da sarrafa abincin da za a ci a wurin taron biki, suna, da sauran sha’ani daban-daban da na maza da mata. Ya tattauna da BASIRA SABO NADABO, inda ya bayyana irin gwagwarmayar da ya sha a matsayinsa na namiji har ya kai ga cimma burinsa a wannan sana’a. Ga tattaunawar:

 

 

Da farko za mu so jin cikakken sunanka da tarihinka

Sunana Abba Umar Yhero wanda aka fi sani da YHERO’S KITCHEN. An haife ni a garin Kano, na yi karatun firamare har zuwa HND duk a cikin garin na Kano, sannan na yi saukar Alkur’ani Mai Girma da sauran wasu littattafai da suka shafi addini.

Malam Abba dan kasuwa ne ko ma’aikaci, ko kuma mai sana’ar kansa?

A’a ba daya, sai dai kai tsaye zan iya kiran kaina da mai sana’ar kansa kasancewata chef.

Wasu da yawa zasu yi mamakin yadda kai tsaye ka kira sunan kan da mai sana’ar girke-girke, za mu so Abba ya yi wa LEADERSHIP HAUSA cikakken bayanin yadda sunan ya samo asali.

Wannan suna ya samo asali tun daga yarinta, ina da wata dabi’a ta son yin dandanon abinci ina nufin wanda ake girkawa, in dan rika sa cokali ina debo dan romon ina lasa a hannuna, to mamanmu ba ta son dabi’ar nan gaskiya, a cewarta wai yawu nake mai da mata a miya, har hanani shiga kicin ake yi saboda kar na yi dandane, a lokacin akwai wasu ‘kitchen set’ na wasan yara da ake kawowa irin tsarabar Saudiyya din nan sister dina tana da shi, to sai na dauki wata yar tukunya a ciki nake fakaitar idon mama in shiga kitchen in zubo miya, ko na dauko Maggi in sa ruwa in fito baranda dinmu in dinga lasa, har dan murhu nake yi na duwatsu.

To a lokcin in babanmu ya gan ni sai ya ringa tsokanata yana cewa Mr. Chef mai ake dafawa ne sai dai in yi dariya kawai, ina girma hankali na zuwarmin wani wasa ko yarinta ana rage su, sai na fara sha’awar yin girki na gaske da kaina, na kan bi mama kicin ko in kunna tauraron Dan’adam kawai don na kalli sabon abinci in gwada yadda ake yi, kusan daga nan komai ya fara.

Ma Shaa Allah! Ya ka ji a sadda ka fara amsa sunan mai girke-girke?

Eh, gaskiya na fada miki shi wancan sunan ana fada ne kawai a matsayin zolaya, na fara amsa sunan ne da gaske bayan na yi wata ‘Catering School’ a Abuja, a lokacin in na yi girki na kan zauna in kale shi in ta jin dadin wai yau ni na yi girkin da ake doki da rububin cin sa, sai na rungumi sana’ar hannu biyu sabanin da da ake yin fada da ni in an fada.

Wane irin girke-girke kake yi? Ina nufin na nan gida Nijeriya ko har da kasashen waje?

Ina yin kowanne saboda na halarci makarantun girki mabanbanta har guda 4

Allah Ya kara basira, fannin fulawa fa ita ma Chef Abba ya kan sarrafa ta?

Ameen ya rabbi, ina sarrafa ta sosai ma, zan iya cewa na fi sarrafa ta fiye da komai, duba da yawancin kayan tande-tanden namu dangin fulawa ne.

Ka san kowace sana’a da nata kalubalen, chef Abba wani kalubale ya fuskanta?

Kalubale na farko da na fara samu shi ne masu bashi, wanda mutum zai kira ya ce a yi masa ‘Birthday Cake’ ko Snack haka in an zo karba za’a taho da kudin, a lokacin gaskiya ina marmarin in ga wai yau ni aka ce in yi abu kaza to in na yi irin haka karshe kudin ko za’a bani ba duka ba, daga baya mama take ce min in nutsu in gyara abin ya koma ‘Pay before serbice.’

Nasara kuma fa? Wace irin nasara ka samu daga lokacin da ka fara amsa sunan chef na gaske?

Na samu nasarori da yawa ta hanyar girki duk da har yanzu ban maida shi sana’a ba, ina da inda nake zuwa aiki daga Litinin zuwa Juma’a, wanda kusan in ba karshen mako ba ba na amsar aikin mutum, amma hakan ba zai sa in ce ban ga ranarsa ba, ya min rana fiye da yadda ban za ta ba, ta girki na hadu da mutanen da nake ganin kamar sun min zarra, na kan sami kudin da zan kashe a cikinsa har in ba wa wani. Sannan yana daga cikin babbar nasarar da na samu bude Catering School dina ta karan kaina, wadda nake koyar da dalibai duk bayan wata 2 ko 3.

A da can da kake yaro kafin ka fara sha’awar girki, menene burinka in ka girma?
Burina shi ne aiki da Kwamfuta, saboda yana birge ni in na ga babana yana daddanna tasa, wanda Alhamdulillah burina yanzu ya cika saboda na karanci ‘Computer Engineering’ kuma ina morarsa.

Wane abu ne yake faranta maka rai game da sana’arka?

Na kan ji dadi ganin samun albarka daga bakin iyaye, mijin ‘yar’uwata ko makusantan wanda suka koyi girki a wajena.

Chef Abba wadanne hanyoyi kake bi wurin tallata sana’arka?

Ta hanyar dalibaina, saboda ranar yaye su na kan basu damar gayyato mutane biyu, wani a nan zai ga abin ya birge shi, ko kuma in aka ci karo da hotunan da suka yi a kafar sadarwa.

Wane irin goyon baya ka samu daga iyayenka duba ga yadda wasu suka fahimci sana’ar girke-girke ga maza?

Mamana da babana sun bani goyon baya dari bisa dari, sai dai lokacin da na gama karatun sikandirena na nuna a gida cewa ni fa bangaren girke-girke na ke son komawa gaba daya, lokacin na ga bacin ran babana sosai ya ce ya zama dole in nutsu in yi karatu na sosai, zan iya harkar girki ba sai ta makarantar boko ba zai biyamin ko nawa ne in shiga makarantar girkin da na ke so matukar zan mai da hankali a karatuna.

Ga aiki, ga kuma sana’a. Shin ta wani hanya kake samun damar yin sana’ar fulawar ga masu oda?

Ina fita aiki ne daga karfe 2 na rana zuwa 5, ina kokarin ganin na yi aikina kafin ya shiga lokacin aikina, in kuma yana da yawa to akwai masu taya ni da na riga na koya musu, za mu fara tare in lokacin aikina ya yi zan mike in bar musu ragowar su karasa.

A karshe wace irin shawara za ka ba ‘yan’uwanka maza?

Kar mu raina sana’a ko yaya take, domin shi namiji ba kamar mace bane, ya zamar masa dolen- dole sai ya yi nema, kar ka tsaya duba mai mutane ke cewa akan irin sana’a da kake yi matukar ka san abin da kake yi bai sabawa dokar addininka ba, sannan mu ji tsoron Allah a komai da muke yi ko muka sa gaba, saboda Allah yana cewa ku neme ni a lokacin da kuke cikin walwala, ni kuma sai in tallafa muku yayin da kuka shiga tsaga tsanani, kar ka ce za ka yi amfani da wata dama da ke hannunka wajen sabawa Allah ko yin wani abin tir.

 

Exit mobile version