Dan dai ana bibiye da mu, a karshen watan Disambar shekarar 2016 mun samu damar zantawa da fitaccen ma`aikacin Rediyon Tarayya na Kaduna, wanda har ya kai Shugabantar gidan rediyon na FRCN, wato ‘Zonal Director ZD.’ Wakilinmu Mustafa Ibrahim Tela ne ya yi waccan tattaunawar, kuma sai ya zama yana ta bibiyar yadda za a yi ya sake zama da shi ZD din.
A wannan lokaci Wakilin namu ya samu daman sake zantawa da Alhaji Halilu Ahmad Getso, inda ya yi dogon bayani na fadi-tashi a aikin Jarida sai dai kash a wannan hira ta wannan lokaci ZD na FRCN, wato mukami mafi girma da ya rike a aikinsa, wanda ke cike da kalubale na yabo da kushewa.
A wancan lokacin bayan hirar su da shi ta yi zurfi, sai ya ke tambayarsa daga cikin abubuwan da ba zai manta da su ba, sai ya ce suna da yawa, daga ciki ya kawo wani labara, inda wani kasurgumin kato ya rutsa shi da sharbebiyar wuka da dubujin Kanbu da Goro da layoyi, wanda ya yi nufin halaka Alhaji Halilu Ahmad Getso, inda ya rutsa shi a ofis shi kadai bayan kowa ya tashi aiki, shi kuwa ya na ciki yana aikinsa kamar yadda ya saba yi.
Haka kuma kasancewar shi mai tambayar bai samu ya yi wannan tambaya tun a wancan karon ba, wanda rashin yin wannan tambaya a wannan lokaci ya jawo makaranta wannan jarida sun yi ta rubuto wasiku ko wayoyi a gare ni, ko shugabanina a aiki, banda kuma wanda su ka tambaye ni ni da su yaya aka yi ya fita a wannan hali?
Ga abin da Alhaji Halilu ya ke cewa game da waccan tambaya. Ya ce bayan da wannan kasurgumin kato ya rutsishi a ofis da mugun makami na halaka dan adam, shi ne ya tambaye shi me ya yi zafi haka? Kuma wanne laifi Halilu Ahmad ya yi masa? Shi ne ya ke ce masa ai ya yi shiri ne ya zazzagi iyayen gidansa, irinsu Balaraba Musa da sauran ‘yan jam`iyarsa ta PRP tun a wancan lokacin.
Sai Alhaji Halilu Ahmad Getso ya ce a wanne shiri ne na zazzagi wadanan mutane da ka fada? Mutumin ya ce a shirin JAKAR MAGORI. Sai Halilu Getso ya ce ba shi ya ke shirin ba. “Sai na lallaba shi na ce bari in kira mai shirin Jakar Magorin, lokacin Alhaji Ado Safyanu Gumal ne ke yin shirin. To ka ji yadda na lallaba na zare jiki na fita na bar shi.”
Wakilin namu ya tambayi Alhaji Halilu Ahmad Getso, to shi wannan kato ya ya fita daga ofis dinka? Inda ya ka da baki ya ce, “shi ne dana fita sai na tambayi masu tsaron gidan, na ce ya aka yi kuka bari wani kato ya je har ofis dina zai kasheni! Suka ce ai ba su gan shi ba. Na ce, ya baku gan shi ba, alhali ta gabanku ya wucce? Suka ce wallahi ba su gan shi ba. Na ce ku je ku fito da shi. Shi ne suka je suka fito da shi daga ofis dina, ya na kara, duk ya cika gidan da kara.
Kuma abin mamaki, kujerar da ya zauna ya gaza tashi a kanta, ya riketa gam, haka aka dauko shi yana kara, aka futo da shi kamar ya manne da kujerar. To ka ji yadda muka rabu da shi.”
Wakilin namu ya kuma tambayi Alhaji Halilu Ahmad Getso, game da cewa duk da shekarunsa, amma da kansa ya ke tuka motarsa? Sai ya ce shi abin da ya fi so ke nan, ya tuka mota da kansa, kuma haka yake tun farkon aikinsa, ba shi da Direba, duk inda za shi da kansa ya ke tuka mota, kuma komai nisan tafiya haka yake yi a zamansa na Legos haka yake yi, ko Nijar ko Kwatano za shi, duk inda za shi a Nijeriya ko kasashen makota haka ya ke yi.
Sanna ya ce ya fi son tafiyar dare, ya fi yenta, domin ta fi sauri, saboda a lokaci ana takure kasa, kuma gari yana sanyi, mota da injinta sun fi son wannan yanayi. Haka kuma ya fi son tafiya shi kadai, duk inda za shi, kuma yana da aladar inda ya ga wuri ya ba shi sha
awa ko dare ko rana ya kan tsaya ya yi nafila ko ya huta ya tafi abinsa.
Ya ci gaba da cewa tafiya shi kadai sirrinta shi ne, in da wani kila ya zama matsoraci, tafiya da matsoraci kuwa ba ta da dadi. Domin ya tabe baro wani gari bayan Magariba a Jihar Kebbi, kilo mita 700, amma a Getso ya Kwana!