Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home MANYAN LABARAI

Yadda Na Zana Tutar Nijeriya -Akinkunmi

by Tayo Adelaja
October 5, 2017
in MANYAN LABARAI
4 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Muhammad A. Abubakar

Shekaru 62 da suka gabata bayan wani Ɗan Jarida ɗan kasar Birtaniya ya kawo zabin assasa sunan “Nijeriya”, wani dalibi mai shekaru 23 kuma haifaffen garin Ibadan shi ne ya zana tutar ta Nijeriya. Michael Taiwo Akinkunmi a lokacin yana karantun Injiniya a makarantar ‘Norwood Technical College’ dake Birnin Landan ya karanta tallar gasar ne a Jarida inda ake neman al’umma su shiga gasar domin zana Tutar ta Nijeriya.

Sai ya aike da saƙonsa garin Lagos, bayan wani lokaci ne, shekara guda a watan Oktoba sai aka gayyace shi zuwa Ofishin Kwamishinan Nijeriya a birnin Landan. A lokacin ne ake fada masa cewa; tutar da ya zana ta kore da fari (Green and white) an zabe ta. Kuma ya yi nasarar cin Fam 100 wanda ya yi daidai da Dala 281 a shekarar 1959. Tare kuma da saka sunansa a cikin kundin tarihin Nijeriya. An yi masa wannan tagomashin a watan Oktoban 1959 shekara 1 kafin samun ‘yancin kai. A yanzu haka Akinkunmi ya zama tsohon ma’aikacin gwamnati da yake rayuwa a wani yanki mafi talauci a garin Ibadan. A ƙafa ake isa gidansa mai ɗauke da kalar kore da fari (irin tutar Nijeriya). Sun rabu da matarsa shekaru 20 da suka wuce. Kuma yana rayuwa ne da ɗansa ɗan Shekaru 28.

Ba shi da wayar hannu, sannan kuma tun a farkon shekarar 1990 rabonsa da motar kansa. Yana jin daɗin tafiya a tsakankanin makwabtansa, kuma yana kaiwa wasu abokan karatunsa guda biyu ziyara. Irin waɗannan ziyarar da yake kaiwa ne ya karawa rayuwarsa armashi.

Akinkunmi yana jindadi idan ya tuna wannan ranar, amma ba zai iya tuna abin da Jonathan ya fada masa ba. Kuma yana da matsalar tuna sunayen tsoffin abokanansa. Da ake tambayarsa shekarunsa sai ya ce shekarunsa “Saba’in da biyar ne (75).” Amma bayan Ɗansa ya gyara masa adadin shekarunsa, ya amince da cewa; shekarunsa 79 ne. Ɗan nasa ya tabbatar da cewa; har yanzu kwakwalwar Babansa kalau take.

Amma duk da haka Akinkunmi bai iya bada sunan Kwalejin da ya yi a birnin Landan daidai, sannan ba ya iya tuna dalilin da yasa aka yi masa tiyata kwanaki kaɗan da nasarar gasar da ya samu na zana tutar Nijeriya. Kuma ba ya iya tuna abu guda daya da ya aikata a ranar 1 ga watan Oktoban 1960 bayan Nijeriya ta da ga tutar kanta a karo na farko wanda ya zana. “Na san na yi farin ciki.” Da yake amsa tambayar ya ya ji a wannan rana.

Wani Dalibin Jami’ar Ibadan mai suna Sunday Olawale Olaniran a lokacin da ya san Akinkunmi da kuma lokacin da ya bayyana shi a matsayin “Gwarzon da ba a girmama ba,” ya bayyana cewa; “a lokacin da na same shi a shekarar 2006 bai fadi wani abu wanda bai dace ba.” Olaniran ya ce zai iya tuna cewa yana fadin; “Allah ya taimaki Nijeriya.” Ko kuma ya ce; “Nijeriya na ci gaba kuma zata ci gaba da yin nasara. ‘Duk da idan ka kula da shi ba wani kulawa yake samu ba.”

A lokacin, Olaniran yana tattara tarihin Nijeriya ne domin maida shi wani karamin takarda. Yana tsaka da binciken tarihin ne, ya gano wanda ya zana tutar Nijeriya. A lokacin ne ya iya gano inda yake. “Wasu mutane sun ce ya mutu, don haka na manta da batun nemansa, kawai na yi rubutu akan tutar kawai.” Inji Shi. Sai dai duk da haka Olaniran ya ci gaba da bincikarsa har sai da ya gano shi a garin Ibadan.

“Akinkunmi yana rayuwa ne shi kadai. Makwabtansa ne ke kula da shi. A ranar farko da muka haɗu, na sami wannan Toshon mutumin yana ta magana shi kadai. Yanayin da na same shi ya saka ni kuka.” Ya kara da cewa; “Sai na yi magana da wani ɗan Jarida muka koma bayan kwana biyu kafin tunawa da ranar ‘yancin kai.” Ya ci gaba da cewa; “shi kanshi ɗan Jaridar yaki yarda da cewa wannan mutumin na nan a raye.” Amma labarin da aka tattara an buga shi a fitowar Jaridar na ranar 1 ga watan Oktoban 2006. Olaniran ya bayyana cewa; bayan wannan labarin ya fita ne da yawan ‘yan Nijeriya suka san halin da Akinkunmi yake ciki.

Akinkunmi kudin fensho yake karɓa a lokacin da Olaniran ya same shi, kuma kudin fenshon dinma ba koyaushe yake samu ba a don haka ba ya iya kula da kanshi. “Wasu ‘yan Nijeriya sun je wurin shi sun kai masa kayan abinci, da kayan sakawa.” Inji Olaniran.

A lokacin taya murnar Nijeriya “Golden Jubilee” a watan Oktoban 2010, shugaban ƙasa ya karrama shi a matsayin fitaccen ɗan Nijeriya. A karon farko da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta karrama shi a bayyane.  Bayan shekaru huɗu da ya gano rawar da Akinkunmi ya taka a tarihin Nijeriya, Olaniran, sai ya zama fitacce a tsakanin shugabannin Nijeriya. Akinkunmi ba zai iya tuna bukukuwan da aka shirya dominsa don karrama shi ba, amma yana iya tuna lokacin da ya dawo Nijeriya da digirinsa a shekarar 1964. Bayan shekara 29 yana aiki da gwamnati, sai ya yi ritaya.

Abin da kawai zai iya tunawa shi ne “cutar yawan tunani” wato “Relapsing feɓer,” na damunsa. Sannan yana karkashin kulawar magani a tsawon shekaru. Wata Uku da suka gabata ne, Likitoci suka dakatar da shan maganinsa, ko sunansa ba ya iya tunawa.

Ya ce; wani abu da ba zai iya mantawa da shi ba, shi ne kulawar da ya samu da kuma goyon bayan da aka nuna masa da tarbar da ya samu a lokacin da ya dawo ƙasarnan bayan an canza tambarin “Union Jack” zuwa tutar da ya zana ta “kore da fari da kore.” Ya ce; “na zama shahararre a dukkanin fadin wurin. Kowa na kira na da Mista ‘Flag Man’ (ma’abocin tuta).”

SendShareTweetShare
Previous Post

‘Yan Gudun Hijira Na Yunƙurin Komawa Bama Da Ƙafa

Next Post

Ƙiris Ya Rage Mu Tarwatsa Ondo Aka Kama Ni –Kwamandan Boko Haram

RelatedPosts

Allurar Rigakafin

An Fara Yin Allurar Riga-kafin Korona a Nijeriya

by Muhammad
7 hours ago
0

Yau Ake Sa Ran Buhari Da Osinbajo Za Su Karbi...

'Yan Adaidaita

An Sasanta Yajin Aikin ’Yan Adaidaita Bayan… Motocin ‘Kano Line’  Sun Koma Jigilar Jakara-Kasuwa

by Muhammad
1 week ago
0

Babu Hanunmu A Ciki Wannan Yaji – Shugaban ’Yan Adaidaita...

Adaidaita

Yajin Aikin Adaidaita: Acaba Ta Dawo A Kano

by Muhammad
2 weeks ago
0

Ya Jefa Jama’a Cikin Tsaka Mai Wuya Yadda Aka Koma...

Next Post

Ƙiris Ya Rage Mu Tarwatsa Ondo Aka Kama Ni –Kwamandan Boko Haram

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version