Connect with us

MANYAN LABARAI

Yadda Naira Dubu Dari Ta Hana Mutanen Barkiya Samun Lantarki Shekaru Biyu

Published

on

Mutanen garin Barkiya da ke cikin karamar hukumar Kurfi a jihar Katsina sun shafe kusan shekaru biyu suna fama da matsalar hasken wutar lantarki saboda matsalar kudi da ba ta wuce Naira 100,000 ba.

A wata ziyarar gani da ido da wakilan kafafen yada labarai suka kai ciki harda wakilin Leadership Ayau sun ganewa idanuwan su yadda wannan matsala ta canza wannan gari na Barkiya da kuma wasu sauran garuruwa da ke kusa da kauyen Barkiyan.

Bincike ya nuna cewa ba garin Barkiya bane kadai wannan matsala ta shafa ba akwai wasu garuruwan da suka hada da garin Banye da ke cikin karamar hukumar Charanchi da ‘Ƴan Marke da suka kwashe shekara biyu da wannan matsala

Daya daga cikin mutanen da muka zanta da su  ya bayyana cewa tuni suka kai rahoton lalacewar wannan wuta, wanda yace asalin abin ya faru ne daga babar hanyar wuta ta Dutsinma wanda daga can ne wutar ta ta so zuwa garin Barkiya da sauran garuruwan da ke kusa da Barkiyan.

“Yadda abin ya faru shi ne, akwai wani lokacin da aka samu matsalar wutar akan babar hanyar Dutsinma saboda haka sai aka raba wutar domin ayi aiki, bayan an kammala gyaran sai ba a maida wutar Barkiya ba, kuma har zuwa yanzu ba mu san dalili ba” inji wani Mutun dan garin Barkiya

A cewar wannan matashi sun kai rahotan wannan matsala a ofishin hukumar samar da hasken wutar lantarki da ke karamar hukumar Kurfi domin daukar matakin da ya da ce, amma har zuwa lokacin da ‘yan jarida suka kai ziyara babu abinda ya biyu baya.

Ya kuma kara da cewa ana cikin wannan jiran masu gyara aka samu wani barawo ya cire wani kyabil mai kawo wuta a jikin taransufoma saboda haka, ko dai an gyara matsalar farko to akwai wata sabuwa daban.

A ta bakin wani ma’aikacin hukumar kula da hasken wutar lantarki ta KEDCO ya bayyana cewa naira dubi dari na iya maganin wannan matsala, tunda babu faduwar turkin wuta ko cirewar wata waya akan hanya.

Wasilu Dahiru wani matashi ne da muka ci karo da shi a farkon shiga garin Barkiya ya shaida mana cewa sun kwashe fiye da shekara biyu ba su da wuta a garin Barkiya, ya ce a lokacin akwai wutar sama da injin nika biyar ke akwai kuma duk suna mafani, amma zuwa yanzu guda daya kacal ya rage ma su.

Kazalika mutanen garin sun kafa wani kwamiti domin tattaunawa da lalubu bakin zaran wannan matsala wanda mai garin Barkiya ya kafa da kan shi, amma dai har yanzu haka bata cimma ruwa ba.

Garin Barkiya dai fitaccen gari ne a cikin karamar hukumar Kurfi kuma nan mahaifar Sanata Injiniya Kabir Abdullahi Barkiya mai Wakiltar Yanki Katsina Ta Tsakiya a zauren Majalisar Dattawa, wanda hakan yasa wasu ke ganin kamar akwai sakaci ace garin Sanata guda wannan matsalar taki ci taki cinyewa.

Duk da haka sai da Laadership Ayau ta yi kokarin jin ta bakin Sanata mai Wakiltar yankin Katsina ta tsakiya a zauren majalisar Dattawa, Sanata Kabir Abdullahi Barkiya, domin jin ko akwai wani kokari da yake na ganin ya share masu hawayensu akan wannan matsalar da ta kwashe tsawon shekara biyu, amma abun ya ci tura.

Suma a na su bangaran Kamfanin rarraba wutar na karamar hukumar Kurfi, Malam Abubukar ya tabbatar da faruwar wannan lamari inda ya ce yanzu haka garuruwan ‘Ƴan Marke da Barkiya da kuma Banye, suma fama da wannan matsalar wutar na tsawon lokaci, saboda duk hanyarsu daya.
Advertisement

labarai