Connect with us

RAHOTANNI

Yadda NIS Ke Bunkasa Zuwa Matakin Kwarewa A Duniya

Published

on

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) a matsayin ma’aikatar gwamnati da aka kafa ta bisa dokar majalisa a shekarar 1963, za ta cika shekara 57 da kafuwa idan Allah ya kai mu watan Agustan 2020.

A tsawon wadannan shekarun da ta yi da kafuwa, ta yi shugabanni guda 15, inda wanda yake kai a yanzu, CGI Muhammad Babandede (MFR) shi ne shugaba na 16. A karkashinsa, baro-baro kowa na iya ganin irin gagarumin ci gaban da ake samu a mataki-mataki. Daga yayin rubuta fasfo da biro da takarda zuwa wallafawa ta na’ura, a yanzu kuma zuwa ingantaccen da ake yi da na’urar zamani mai karko da aminci. A bangeren biza ma an samu ci gaba daga samarwa ta hanyar buga tambari a takarda zuwa na’urar da ake daukar bayanai da tambarin yatsu. Haka nan an samu sauyi daga tsohon yayi na gabatar da bukatar fasfo da biza ta hanyar cike-ciken takardun zuwa nema ta shafin intanet a duk inda mutum yake da kuma sauya biyan tsabar kudi a hannu zuwa ta shafin intanet da kuma sauran sauye-sauye da aka samu.

Tsohon fasfo

A karon farko a cikin wadanan shekaru 57 da NIS ta yi da kafuwa, hukumomin shige da fice na kasashen nahiyarmu da sauran na kasashen duniya suna ziyartar shalkwatar NIS domin nazarin yadda shugabanta yake kawo sauye-sauye masu ma’ana. Hukumar ta karbi bakuncin shugabannin hukumomin shige da fice na kasashen ECOWAS a wani taron koli da suka yi a Abujan Nijeriya. Sashen shige da fice na Gambiya ya yo tattaki na musamman domin nazarin yadda NIS ke samun bunkasa.

Samfurin cikin tsohon fasfo

Haka nan hukumomin ‘yan sanda da na kula da tsaron iyakoki na kasashen duniya daban-daban sun kawo ziyara domin tattauna yadda za su yi hadin gwiwa da NIS wajen gudanar da aiki cikin kwarewa a duk duniya musamman wajen bai wa ‘Yan Nijeriya martabar da ta kamata ta fuskar tafiye-tafiye zuwa kasashen da hukumomin suke don zama ko gudanar da halastaccen kasuwanci. Wakazalika, NIS ce ta tsara shirin dawo da ‘Yan Nijeriya gida daga kasashe da dama da mayar da sauran ‘yan kasashen da ake kawance na ci gaba da su zuwa gida, wanda hakan ya kara wa Nijeriya mutunci a idon duniya.

Tsohon fasfo da NIS ta sauya zuwa sabo na zamani

Bugu da kari, gangamin da aka fara yi a kan alfanun fasfo ga tafiye-tafiye cikin kwanciyar hankali ya samo asali ne daga wata mukala da CGI Babandede ya rubuta shekaru da dama kafin ya zama shugaban NIS, inda mukalar ta samu karbuwa aka mayar da ita kundi. Kundin ya samu goyon bayan hukumomin da ake kawance na ci gaba da su ciki har da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Duniya. Gangamin wanda aka karade jihohin kasar nan 36 har da Babban Birnin Tarayya Abuja da shi, ya fayyace irin hadurran da ke tattare da safarar bil’adama da fasa-kwaurin bakin-haure kamar yadda yake kunshe a cikin kundin inda aka rarraba kwafensa ga masu neman fasfo a daukacin ofisoshin fasfo yayin gangamin na wayar da kai. Wannan ya haifar da kyakkyawan sakamako wajen dakushe hada-hadar masu safarar bil’adama da bakin-haure bisa yadda aka samu raguwar matsalar da kuma cafke gungun masu aikatawa a filayen jiragen sama da iyakokin kasa na ruwa da kan-tudu.

Irin sauye-sauye na ci gaba da aka samu a NIS a sassa daban-daban a zamanance; abubuwa ne da ya dace a yi murna da shagulgula a kai musamman idan mutum ya san yadda aka rika shan wahalar aikin fasfo a baya da kuma irin yadda aka inganta fasfon a yanzu; da ya kawo martaba ‘yan kasa a lokacin da suke tafiye-tsafiye a kasashen waje. Dole a jinjina wa NIS a kan wannan namijin kokari nata na kawo sauyi mai ma’ana a kan fasfo wanda ya jawo hankalin Babban Gidan Talabijin a Duniya da ke Amurka CNN yin nazari na musamman a kai da kuma yaba wa Nijeriya da ‘Yan Nijeriya bisa yadda aka amince da fasfon ana watayawa da shi a duniya.

CGI Muhammad Babandede (MFR)

Shudin fasfo na Nijeriya ya kasance abin da ya sauya makomar ‘Yan Nijeriya da dama a kasashen waje, don haka wajibi ne a yi murna da farin ciki a kansa. NIS ta samu bunkasa daidai da ci gaban zamani bisa yadda aka mayar da ayyukanta a kan turbar ci gaban kimiyya da fasaha musamman bisa samar da katafaren ginin fasahar sadarwa ta zamani, ayyukanta za su tattara bai-daya domin yi wa ‘yan kasa da bakin waje aiki mafi inganci.

Hakika irin habakar da NIS ta samu a cikin shekara hudu na shugabancin CGI Babandede, na da matukar al’ajabi. Duk wadannan abubuwa da muka kawo tsakure ne, domin za a ga abubuwan mamaki kwarai da gaske idan aka ziyarci shafin intanet na hukumar a cikin watan Agustan 2020, yayin da NIS za ta baje kolin gagaruman sauye-sauyen da ta samu domin murnar cikarta shekara 57 da kafuwa.
Advertisement

labarai