Hukumar da ke kula da harkokin shari’a a Nijeriya (NJC) ta bada shawarar a yi ritayar tilas wa Grand Kadi na jihar Yobe Shu’aibu Talba, da kuma Alkalin babban kotun jihar Osun, Justice Abdulkareem Abdulrasak bisa zargin ayyana shekarun bogi.
Matakin bukatar gaggauta tsige manyan jami’an shari’ar ya faru ne a yayin zaman majalisar koli na NJC karo na 93 da ya gudana a ranar 16 ga watan Disamban 2020.
Kafin daukar wannan matakin an bincike korafe-korafen da aka shigar kan Alkalan inda aka samu korafin suna da inganci, bayan wannan majalisar kolin ta yi watsi da korafe-korafe 18 da aka shigar kan Alkalai daban-daban a fadin kasar nan bisa rashin sahihanci.
Hukumar a yayin dai wannan zaman, sun kuma bada shawarar daukar sabbin jami’an shari’a guda 69 domin tabbatar da yanke hukunci na tafiya yadda ake so a fadin kasar nan.
Sanarwar ta ce, Talba ya sha ayyana shekarun haihuwarsa har sau biyo a lokuta daban-daban, wanda da fari yake amfani da cewa an haifesa ne a ranar 1 ga watan Fabrairun 1955 ya koma 27 ga watan Agustan 1955 daga baya ya maida 30 ga Disamban 1959.
“An gano cewa ya kamata ne ya yi ritaya a ranar 1 ga watan Fabrairun 2020 a bisa ayyana shekarar haihuwarsa na 1 ga watan Fabrairun 1955.
“Bayan zaman majalisar, ta cimma matsayar baiwa Gwamna Mai Mala Buni shawarar ya yi masa ritayar dole.”
Har ila yau, hukumar ta bukaci gwamnatin jihar Yobe da ta cire albashin da ya amsa daga ranar 1 ga Fabrairu, 2020 har zuwa yanzu, a cikin kudinsa na giratuti.
Dangane da batun Justice Abdulkareem Abdulrasak, sanarwar ta shaida cewar bayan bincike kan takardar korafin wani babban Lauya mai mukamin SAN, Chif Yomi Alliyu ya shigar a kansa, an gano ya yi karyan shekarun haihuwa daga ranar 3 ga watan Satumban 1955 zuwa 3 ga watan Satumban 1957.
“Majalisar ta bada shawarar shi wannan Alkalin a masa ritaya na dole wanda ake son gwamna Gboyega Oyetola na jihar Osun ya aikwatar wanda zai fara aiki daga ranar 3 ga watan Satumban 2020. An kuma bukaci gwamnatin jihar ta zare albashin da ya amsa tun daga ranar 3 ga watan Satumba 2020 daga kudinsa na giratuti.”
Hukumar dai ta nemi dukkanin kudaden da gwamnonin suka cire daga giratuti din wadanda aka nemi a kora ta a shigar da su zuwa lalitar National Judicial Council.
Har ila yau NJC ta yi fatali da korafe-korafe guda 18 da aka shigar kan Alkalai daban-daban bisa gaza gamsuwa da bayanai da rashin sahihanci.