Yadda Noman Shinkafa Da Kasuwancinta Ke Samar Da Riba A Nijeriya

Shinkafa

Na farko, Noman Shinkafar:

 

Lokacin noman Shinkafa a Nijeriya ya sake dawowa. Ruwan sama ya sauka a manyan sassan kasar inda akwai kasa mai kyau don Noman Shinkafa a birane daban-daban na kasar. Idan kana zaune a cikin yankunan da ke da kasa mai dausayi, to hanzarta shiga cikin kyakkyawan kasuwancin noman shinkafa. Na ga gulbi mai yawa ko da a Kaduna wanda ina tsammanin zai yi kyau sosai ga noman shinkafa. Me zai hana a gwada shi? Zuba jari shine game da daukar dama ta farawa. Noman shinkafa yana daya daga cikin ingantaccen saka hannun jari, kuma ga duk mai son saka jari kada ya raina shi. Wannan saboda damar samun aiki da riba.

 

Dayan abu mai kyau game da noman shinkafa shi ne cewa bai daukar sama da watanni hudu tsakanin shuka da girbi. Saboda haka, duk yawan kudin da ka saka a yanzu, kana da tabbacin dawowarsu nan da watanni hudu masu zuwa, akwai tabbacin yiwuwar biyan bashi cikin sauri idan ka karbi rance don saka hannun jari a noman shinkafa.

 

A wani bangare na kokarin da gwamnati ke yi na tabbatar da samar da wadataccen abinci ga ‘yan kasarta, noman Shinkafa shima yana daya daga cikin irin hannun jarin da gwamnatin ke shirin tallafawa ta hanyar karbar bashi da kayan aiki ga duk wani manomi da yake son shiga, wanda hakan yana da matukar girma da fa’ida ga masu noman shinkafa.

 

Noman shinkafa yana tafiya kai tsaye kuma baya bukatar kwarewa sosai, kowa na iya noma da girbin shinkafa, ba tare da la’akari da kwarewarka da kuma asalin sana’ar shinkafa ba. Shinkafa ta kasance mai yawan amfanin gona na girma, irin ‘Acre’ na daya daga cikin shinkafar da ke iya samar da buhunan shinkafa sama da 100. A kasa akwai wasu abubuwan da ake bukatar yi don tabbatar da hakan –

 

(a) Kyakkyawan dausayi, kasa mai karancin karfi

 

(b) Yawan noman shinkafa na musamman

 

(c) Takin da ya dace da aikace-aikacen da suka dace

 

(d) Kula da shukar a lokacin da ya dace

 

(e) Da shukar wuri.

 

Idan aka sanya wadannan a gaba, to tabbas ana cikin cinikin kasuwancin shinkafa!

 

A cikin amfanin gona, Shinkafa tana da saurin shiga a kasuwa, ba sai ka jira watanni ko shekaru ba kafin ka iya sayar. Yana sayiwa da sauri wanda za a iya zubar da komai daidai a gonar sai dai kawai idan kana son sarrafa shi ko adana shi. Wannan shine dalilin da yasa noman shinkafa ya zama babban dama.

 

Shinkafa ita ce mafi yawan abincin da ake ci a kasar Sin, Indonesiya, Tailand, da Nijeriya, wacce ta kasance kasar Afirka ta Yamma da ke da mutane sama da miliyan 150. Ana iya shirya sarrafa ta hanyoyi daban-daban kamar, Farar Shinkafa da miya, Jollof, tuwan shinkafa, da sauransu. Ba za ka iya shakkar amfanin shinkafa a yawancin kasashe a duniya ba. Yanzu, idan kana da niyyar shiga ciki, a nan akwai mataki-mataki yadda ake noma da girbin shinkafa.

 

  1. Zaba tsabar iri mai kyau:

 

Mafi kyan iri, mafi kyan shinkafar da za a samar. Nemi ingantaccen gaskiyar kuma ka yi zabin iri, ba kawai ka shuka kwaya ba tare da nuna bambanci ba, a’a ka rarrabe tsakanin mai kyau da mara kyau. Kyakkyawan aikin samar da shinkafa yana bukatar ka zabi zuriya da hannu. Rashin zabin iri mai kyau shine babban dalilin da yasa manoman gida suke samar da kadan.

 

Idan ka zabi mafi kyaun tsabar shinkafa, girbinka zai dace da lokaci da kuzarin da aka saka a zabar tsaba. Amma idan ka yi sakaci da wannan! To, za a yi asara.

 

  1. Kiwata ‘Ya’yan irin tun a matakin farko:

 

Shirya tsaba da kuma shuka iri da farko don ya girma a cikin gandun daji shine matakin farko. Lura sosai da kasar wurin ta hanyar rufe ta da rufin polythene mai haske a cikin wasu don sarrafa cututtukan kasar. Saboda yawancin kasa masu dauke da kwayoyin cuta da nematodes suna yin lalata idan aka dasa shinkafa, domin suna barin shi da karancin amfanin kasa.

 

Haka kuma, an nuna cewa yawan shinkafa koyaushe yana karuwa da kusan kashi 36 ta hanyar amfani da fasahar ‘solarization’ don daga shukoki. Haka zalika, dasa shinkafa da ta balaga a girba da sauri fiye da wata. Bayan makonni biyu zuwa uku, kwarorin zasu isa girbi.

 

  1. Nemi kasar dausayi:

 

Kasa mai dausayi tana ba da sauki wajen noman shinkafa, saboda ba ka da damuwa na ban ruwa. Kodayake ana iya shuka shinkafa a cikin yanayin busasshiyar kasa da fadama mai rami da kuma ban ruwa, amma an nuna cewa shinkafa tana samar da kari a kan gandun dajin kasa mai ruwa. Don haka, kamata yayi a neme ta. Shirya kasar ta hanyar sharewata da amfani da Taraktoci har sai kasar ta yi laushi don ainihin dasa shukar shinkafarka.

 

  1. Sarrafa Shinkafar:

 

Bayan dasawa na tsawon watanni biyu, gonar shinkafar zata isa cire ciyawa, to lokaci zai yi da za ayi amfani da maganin kashe ciyawar a hankali. Wasu mutane suna shafawa ciyawar Magunguna sau biyu kafin girbi. Ana amfani da taki a cikin kimanin wata guda bayan hakan. Yi amfani da takin da ya dace (Takin gargajiya), kuma yi amfani da shi ta hanyar fesawa a cikin gonar da madaidaicin yawa.

 

  1. Girbe Amfanin:

 

Tsakanin watanni 4 na dasa shuka, amfaninka zai kasance a shirye don girbi. Lokacin da ta balaga, launin shinkafar zata canja daga kore zuwa launin ruwan kasa. Bayan haka, ka san amfanin gonarka ya isa girbi.

 

Kana bukatar shigowa ka girbe amfanin gonar cikin hanzari don gujewa cin kwari kamar yadda dabbobi da yawa ke ciyar da irin shinkafar. Kana bukatar koyon abubuwa da yawa game da yadda ake maganin kwari.

 

Duk kokari da kudin da ka sanya a gonar, ka tabbatar da cewa cikin watanni biyar za ka yi murmushi a hanyarka ta zuwa banki.

 

Na biyu, Raba Shinkafar:

 

Fatan kasuwancin raba shinkafa a Nijeriya ya zama kan gaba ga duk mai saka jari wanda a halin yanzu yake neman kasuwancin da zai saka jari. Shin kai dan kasuwa ne mai sha’awar rabawa ko samar da kasuwancin? Bayan haka yi la’akari da raba shinkafa a kasuwanci na musamman wanda zai ba ka damar murmushi a hanyar zuwa bankinka.

 

Za ka yarda da ni cewa da wuya a sami wani gida a cikin Nijeriya da basa cin shinkafa. Wannan yana nufin cewa za a sami kyakkyawan sakamako akan saka hannun jari a cikin wannan kasuwancin. Muhimmancin shinkafa ga talakan Nijeriya ba zai taba raguwa ba. Wannan labarin zai tsaya kan raba shinkafa ko wadata shi, kuma me yasa yakamata a yi la’akari da shi a matsayin kyakkyawar saka hannun jari.

 

Kodayake a kwanan nan Ministan Noma da Raya Karkara, ya yi ikirarin cewa, “Nijeriya za ta zama kasar da ta fi kowace kasa fitar da shinkafa a Afirka cikin shekaru biyar”, amma har yanzu tattalin arziki na nuna akasin haka, inda jama’a ke cin buhunan shinkafa a kullum.

 

  1. Ribar da ke ciki:

 

Dogaro da karfin kudinka, za ka iya fara wannan kasuwancin da naira miliyan 5 ko kasa da haka. Kasuwancin raba shinkafa yana kawo jari sosai cikin hanzari. Misali, ana sayar da buhun 50kg na shinkafa na yau da kullum a kasuwa kan farashi Naira 25,000, yayin da karami ya kai 14,500. Yanzu, ka yi la’akari da irin ribar da kasuwancin zai samar.

 

A matsayinka na mai rabawa ko dillali, za ka iya samun jaka akan N24,000, ko N24,500, kila idan kasan daya daga masu shigo da kaya ka samu kasa da haka. Idan ka kawo buhun shinkafa 50 a rana akan kudi Naira 24,500, zaka samu ribar 500 d 50 = N25,000.

 

A kasa, ga wasu nau’ikan shinkafa da ake da su a kasar.

 

Shinkafar Ofada:

 

Shinkafar Ofada suna ne na gama gari wanda ake amfani da shi don bayyana shinkafar da ake samarwa a cikin gida wacce miliyoyin ‘yan Nijeriya suke daukarta a matsayin dayan mafi kyawu. Ana samar da ita a kudu maso yamma da kuma kudu maso gabashin Nijeriya. Idan aka kwatanta da wasu, farashin yana dan daga sama, amma bukatar tana da yawa saboda masana harkar abinci sun yi imanin cewa yana ba da karin abubuwan gina jiki.

 

Shinkafar Stallion/Aroso:

 

Shinkafar Aroso ita ce dayan mafi girma kuma ana rarraba ta a duniya, tare da inganci na musamman a duk duniya.

 

Wadannan su ne wasu nau’ikan Shinkafar Stallion: Caprice, Tomatoes King, Africa Princes, Caprice Golg da sauransu. Wadannan suna da yawa a kasuwannin Nijeriya.

 

Shinkafar Basmati:

 

Wannan wani nau’in shinkafa ne mai kyau kuma mai inganci saboda yadda ake samar da ita, albishir da irin wannan shine cewa yana da dandano na musamman mai ban sha’awa, ba ta da danko kuma tana dauke da abubuwa masu muhimmanci guda takwas kamar amino acid, sodium, folic acid, da sauransu. Tana da kamshi na musamman wanda yasa ta ficewa. Yawanci ana cin ta a cikin kasashen Afirka ke da Faransanci.

 

Shinkafar Brown:

 

Shinkafar brown ita ce cikakkiyar hatsi tare da taushi, mai dandano da lafiya, watau tana bukatar tauna sosai kafin a hadiye ta.

 

Shinkafar Brown ta fi farin shinkafa kuma galibi ana samunta a manyan kantuna.

 

Inda ake saya:

 

A halin yanzu, akwai shinkafa iri daban-daban a kasuwar Nijeriya. Duk wacce ka ke son samarwa, zaka iya samunsu daga kasuwa.

 

Dangane da Kaduna, kana iya samun wannan shinkafar a kasuwannin masu kamar, Kasuwar bacci, bakin dogo da wasu wurare.

 

Ba tare da yin la’akari da birni na Nijeriya ba, akwai dubban ‘yan kasuwa da ke warwatse a cikin birnin wadanda ke shirye su saya. Don haka, idan ka saka hannun jari a cikin wannan kasuwancin, tabbas za ka yi murmushi a hanayar banki. Maganar taka tsantsan ita ce, ka yi kokari kada ka sayar da mugun riba.

 

  1. Matakin Amfani:

 

Yawan jama’ar Nijeriya ya jawo masu saka jari da yawa. Baya ga sauran baiwa na duniya, Nijeriya na da manyan damar kasuwanci wanda a yanzu ya hada da shinkafa a matsayin babbar kasuwa. Ana kiyasta yawan mutanen Nijeriya sama da mutane miliyan 170, a cewar Majalisar Dinkin Duniya (UN).

 

  1. Babban Matsayin Buwatu:

 

Yawan jama’ar kasar, da kuma yawan cin abinci, musamman shinkafa, suna da muhimmanci ga kowane mai son kasuwanci ya sami kudi na gaske. Yana da muhimmanci ka duba kasuwar Nijeriya da kyau. Ko da a yankinka, za ka yarda da ni cewa manyan masu sayar da kayayyaki a irin wadannan wurare suna da yawa, kuma idan ka yi la’akari da nisan da ake safarar irin wadannan kayayyaki daga jirgin zuwa inda za su, irin wadannan mutane za su karkata ga saya daga gare ka, idan ka bude kantin sayar da kayayyaki.

 

Kana iya sanar da ‘yan kasuwa kasuwancinka don samar musu da adadin da ake bukata a gare su, yayin da ka ke la’akari sosai da adadin darajar da za a iya bayarwa a cikin dan gajeren lokaci.

 

Yi la’akari da wannan bayanin kuma saka hannun jari cikin hikima. Don haka, muna yi muku fatan nasara, a lokacin da ku ke fara wannan kasuwancin!

Exit mobile version