Dga Rabiu Ali Indabawa,
Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Nijeriya (NULGE) na shirin gudanar da zanga-zanga domin mamaye gidajen kasar na dukkan ‘yan majalisar tarayya bisa nuna goyon baya ga kudirin da ke neman a soke majalisun kananan hukumomin da ‘yan majalisun suka yi.
Kungiyar ta ce duk masu goyon bayan kudirin makiyan Nijeriya ne da dimukradiyya, kuma ba su damu da halin kunci da bukatun shugabanci da ‘yan Nijeriya ke ciki a yankunan karkara ba. Shugaban NULGE Ambali Olatunji ya yi magana game da kudirin a gaban majalisar wakilai da ke neman soke matakin gwamnati na uku.
Wani dan majalisar wakilai, Bob Solomon, ne ke daukar nauyin dudurin dokar. Olatunji ya ce idan ba a kashe kudirin nan take ba, ma’aikata a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa za su gudanar da zanga-zanga a Majalisar Dokoki ta kasa, bayan haka za su mamaye gidajen kasar na dukkan mambobin majalisar.
“Ana barazana ga rayuwarmu; ba za mu zauna mu zuba ido muna kallo ba. Za a yi zanga-zangar kasa a can a Majalisa ta kasa. “Yanzu ba sa wakiltar mu, suna wakiltar kansu ne. Bob Emmanuel, wanda ya ci gajiyar tsarin kananan hukumomin, a yanzu ya zama abin takaici har yana son a soke tsarin.
“Shi dan jam’iyyar (PDP) ne shi ya sa muka nemi jam’iyya ta kira su domin su yi oda. Duk mutumin da ya yi yunkurin kashe tsarin kananan hukumomi yana kashe makomar siyasarsa ne. “Babu wani dan majalisar dokoki, wanda yake bangaren talakawa da ya kamata ya shiga wannan mummunar dabi’ar kuma ko waye sai mu yake su duka, ”in ji shi.
Shugaban na NULGE ya bukaci gwamnoni, wadanda suka yi imani da kananan hukumomi kuma suka gudanar da zabe a cikinsu, da su yi magana kan wannan shirin na dagula tsarin da ke kusantar da gwamnati kusa da mutane.