Kungiyar Plateau United dake jihar Filato ta lashe gasar firimiya ta Nijeriya ta shekarar 2016 zuwa 2017 bayan da ta doke kungiyar Enugu Rangers ta jihar Enugu da ci 2-0, a filin wasa na Rwang Pam da ke jihar a ranar asabar din da ta gabata.
Hakan ya sa kungiyar ta hada maki 66 a wasanni 38 da aka buga a gasar, yayin da wadda tayi na biyu a gasar wato Mountain of Fire ta jihar Legas ta hada maki 62 bayan ta sha kashi a hannun El-Kanemi Warriors ta garin Maiduguri.
Kungiyar kwallon kafa ta Enyimba International ce tayi ta uku a gasar bayan da ta doke Katsina United da ci 1-0 a garin Aba. Yayin da kungiyar kwallon kafa ta Akwa United ta kammala gasar a matsayi na hudu duk da ta doke Kano Pillars da ci 3-0 a jihar Akwa Ibom.
Nasarar da Plateau United din ta samu zunzurutun kudi har naira miliyan 50, yayin da kuma zata wakilcin Nijeriya a gasar cin kofin zakaru na nahiyar Afrika tare da Mountain of Fire wadda tayi na biyu, sai kuma kungiyar Enyimba wadda tayi matsayi na uku ita ma zata wakilci Nijeriya a gasar Confedaration cup shi ma na Afrika.