Karim Benzema a yanzu shine dan wasa daya tilo da Real Madrid take da shi wajen zura kwallo a raga, wanda hakan ya sa kociyan kungiyar ya dogara dashi kacokan wajen samun kwallaye duk kuwa da shekarunsa.
Hakan ya sa masu ruwa da tsaki a harkokin wasanni sun ce rashin cin kwallaye daga bangaren shahararren dan wasan gaba na Real Madrid Karim Benzema a wasannin da kungiyar ke bugawa na kassara kokarin kungiyar gaba daya saboda rabonsa da ya ci wa Real Madrid kwallo tun makon karshe na watan Disambar shekarar 2020 da ta wuce.
Rashin cin kwallaye dan wasan na shafar rashin kokarin Real Madrid, domin shi ne ya ci kwallaye 12 daga 37 da ta zura a raga a kakar bana wanda hakan yasa ake ganin shine kashin bayan kungiyar a wannan kakar.
Bayan rashin cin kwallon, dan wasan bai kai hari ko da daya ba a karawar da Real Madrid ta yi da kungiyoyin Elche da Celta Bigo da kuma Osasuna a gasar La Liga wanda hakan babban abin dubawa ne musamman ga kociyan kungiyar wanda a koda yaushe yake goya masa baya.
Daga nan ya sake yin karawa uku ba tare da ya ci wa Real Madrid kwallo ba a fafatawar da ta yi da Cadiz da Shahktar a kofin zakarun turai da kuma wasan hamayya na El Clasico a gidan Barcelona.
Benzema ya taba yin wasanni bakwai ba tare da ya ci kwallo a kakar farko da Zinedine Zidane ya fara horar da Real Madrid, sai dai lokacin Cristiano Ronaldo yana kan ganiya yana kuma fitar da kungiyar kunya.
A kakar bana da Benzema ke kan gaba ya ci wa Real Madrid kwallaye 12 a wasanni 21 da ya buga, wadanda ke biye da shi sun hada da Luka Modric da Casemiro da kowanne yake da kwallaye guda hur-hudu a raga.
Sai dai hakan na nuna Real Madrid ba ta da takamaiman mai cin kwallo da zai taimakawa Benzema kamar yadda sauran kungiyoyi ke yi kuma babbar matsala ga kungiya kamar Real Madrid.
Misali Bayern Munich tana da Robert Lewandowski a matakin lamba tara, wanda ya ci kwallo 23 a bana kuma tana da dan kasar Jamus wato Thomas Muller wanda ya ci kwallaye tara a raga a mai taimaka masa.
Jubentus tana da Cristiano da ya ci kwallo 18 da kuma Albaro Morata mai 10 a raga, ita ma Paris Saint-Germain tana da Kylian Mbappe da kuma Neymar wadanda duka suna iya zura kwallo a raga a kowanne yanayi.
Barcelona tana da Lionel Messi da kuma Antoine Griezmann, Atletico Madrid tana da masu cin kwallaye Luis Suarez da Joao Felid, Liberpool kuwa tana da Mohamed Salah da kuma Sadio Mane.
Kawo yanzu Luka Jobic baya buga wasa sosai da shi da Mariano Diaz, Eden Hazard yau da lafiya gobe jinya, Rodrygo jinya, Binicius Junior ba labari shima, in banda Asensio kadai da ke nuna hazaka.
Ya zama wajibi Real Madrid ta samo karin masu ci mata kwallaye, idan har tana son kare kofinta na La Liga ta kuma lashe Champions League na bana wanda take muradin lashewa idan an koma hutu cikin watan Fabrairu.
A kakar tamaula ta bana Real Madrid na kasa kokari idan ta hadu da kananan kungiyoyi a wasanninta, saboda haka sai ta sayo matasa masu zafi da za su dunga zura kwallaye a raga domin ta cimma burinta.
A satin da ya gabata Zidane ya bayyana cewa dole kungiyar tana bukatar dan wasa mai zura kwallo a raga biyo bayan canjaras din da tawagar tasa ta buga a daren Asabar da kungiyar Osasuna a gasar La liga.
Real Madrid dai tana ci gaba da saka kaimi domin ganin ta samu nasarar lashe gasar La liga ta bana kuma da ace ta samu nasara a wasan na ranar Asabar zata zama ta daya akan teburin gasar ta bana.
“Tabbas akwai karancin zura kwallo a raga a wannan tawagar tamu saboda haka muma fatan nan gaba kadan zamu samu dan wasan gaba wanda zai taimaka mana saboda zura kwallo a raga yayi kadan a wannan kungiyar” in ji Zidane
Real Madrid wadda take ta biyu a teburin La liga ta shiga shekarar 2021 da kafar dama, bayan da ta doke kungiyar kwallon kafa ta Celta Bigo daci 2-0 a gasar Spaniya ranar biyu ga watan Janairu a filin wasa na Alfredo Di Stefano sai dai ta kasa doke Osasuna a wannan satin da ya gabata.
A watan na Janairu kungiyar za ta fafata a karawa uku a La Liga, da daya a gasar Spanish Super Cup wanda ta lashe a bara a Saudiyya da kuma fafatawa a gasar cin kofin Copa del Rey wato gasar cin kofin kalubale na kasar.
A kwanakin baya kociyan kungiyar, Zinadine Zidane, ya bayyana cewa ‘yan wasan kungiyar za suyi iya kokarinsu wajen ganin sun farantawa magoya bayan kungiyar rai ta hanyar lashe kofi duk da cewa har kawo yanzu ‘yan wasa basa shiga kallon wasan.
Zidane ya kalubalanci ‘yan wasan da su dage wajen zura kwallo a raga domin hakkin kowanne dan wasa ne yayi kokarin zura kwallo a raga domin taimakawa kungiyara wajen cikar burinta na lashe kofi a bana.