Sanin kowa ne cewa, sana’a ba karamar gudummowa take bayarwa ba, wajen tafiyar da harkokin rayuwa, ga duk wanda ke yinta, ba ma kawai sai maigida ba.
Akwai rufin asiri, ko da kuwa yaya ita sana’ar take. Wadanda suke da sana’a suna tafiyar da harkokinsu na yau da kullun ba tare da sun je gurin wani sun yi ‘yar murya ba.
Wannan ma shi ya sa na tattauna da wadannan mutanen, wanda kowa ya bayyana ta sa gudummowar dangane da hakan.
Da farko dai shi Alhaji Abubakar Mai Albasa Sarkin Kasuwar Maraba cewa ya yi, maganar gaskiya al’amarin kuma ko wata gargada babu, idan har aka ji maigida wanda shi al’amarin tafiyar da gidan ya rataya a wuyansa bai da wata sana’ar yi, ai babu yadda zai tafiyar da gidan kamar yadda yake so.
Zai yi ma sa matukar wuya ya samu gudanar da tarbiyyar ‘ya’yansa kamar dai muradinsa, ita ma matar idan ba sa’a ya yi ba, zai yi wuya ta yi masa tarbiyya, daga karshe shi ma da kansa yana iya samun kansa cikin wani al’amarin da bai taba tsammani ba sanadiyyar rashin sana’ar yi, don haka ya yi kira da kada a yi watsi da sana’ar yi komai kankantar ta kuwa.
Shi kuma maiunguwa Sa’idu Muhammadu Buhari, International market, yana ganin ita sana’ar yi ga maigida ba karamar garkuwa ba ce gare shi. Bai gane muhimmancinta, sai lokacin da ya rasa ta, zai iya gane cewa tana yi masa babban rufin asiri, musamman ma wajen tafiyar da rayuwarsa, wannan ma shi ya sa ya kara yin kira ga magidanta su samu sana’ar yi.
Saboda kuwa idan har maigida na da sana’ar yi babu wanda ya isa ya rena masa wayo, bugu da kari kum a zai fi mutunci a idanun al’umma.
Daga karshe, Alhaji Yusuf Umar Sarkin Hausawan Masaka babbar maganar da ya yi wadda kuma take da muhimmanci sosai cewa ya yi, ai maganar sana’ar yi ko wani abin yi shi ne abu na farko wanda ya kasance tubali ne na yadda zai tafiyar da rayuwarsa ta gida, idan kuma babu wani ginshiki wanda zai dauki nauyi gini ai babu ginin ke nan.
Idan kuma har abin ya kasance babu wata sana’ar yi, ai wannan ba karamar matsala bace. Daga nan kuma ita maganar a yi aure da tafiyar da gida, idan har babu sana’r yi, ko wani abin yi ai tamkar wanda ya ce, ya dauri aniya tafiya har ya shiga mota, lokacin da aka fara amsar kudi ya gane cewa ashe baida kudin da zai bayar wadanda za su bada damar a yi tafiyar tare da shi.