Daga Alhussain Suleiman Dakace,
Rashin tsaro ya shafi harkokin noma musamman manoman Ridi suma abin ya shafe su. Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Jami’in watsa labaran kungiyar hadaddiyar ‘yankasuwa ta Jihar Kano, sannan mai neman takarar sakataren kungiyar kasuwar Dawanau da ke Jihar Kano, Alhaji Auwalu Alhassan Zara, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a kasuwar sayar da abincin ta Dawanau. Sai dai A. A. A. Zara ya koka game da yadda tallafin da gwamnati take bayar wa baya zuwa ga manoma na gaskiya sai dai wadanda ba su san yadda ake noman ba, da kuma an mayar da noma sana’a da an samu gaggarumar cigaba ta bangaren noma .
Malam Auwalu Alhassan ya yi kira
ga gwamnati da ta rika sauraren matsalolin yankasuwa, ya ce, abin bakin ciki ne ace bakin ‘yankasuwa daga wasu kasashe ke fitar da farashin kaya a wasu kasuwannin kasarnan babu shakka wannan zai iya haifar da cikas ga harkokin kasuwanci.
Daga karshe ya yi kira ga wasu ‘yankasuwar da suke aikata algus da su ji tsoron Allah su daina, amma ya jinjina wa shugabannin masu kungiyar masu sayar da Ridi da ke kasuwar a kan yadda suke bakin kokarin su wajen kama duk wanda aka kama yana aikata rashin gaskiya acikin kasuwar .