Yadda Rasuwar Mai Kanurin Lagos… Ta Kawo Jita-jitar Rasuwar Zulum

Jita-jitar

Daga Muhammad Maitela,

Hatsarin motar da ya yi sanadin rasuwar Mai Kanuri na Legas, Alhaji Mustapha Muhammadu, tare da wasu mutune biyu da ba a bayyana sunayensu ba, ya jawo jita-jitar cewa, tawagar Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ce ta gamu da hatsarin mota a kan hanyarsu daga garin Mafa zuwa Maiduguri da yammacin jiya Talata.

A ranar Talata Gwamna Zulum tare da tawagarsa sun tafi mahaifarsa a karamar hukumar Mafa, domin sabunta rijistar jam’iyyar APC dake gudana, wanda akan hanyarsu ne ya rsiki motocin tawagar Marigayi Mai Kanuri na Legos, inda motar ake ciki ta yi hatsari a lokacin da suke dawowa Maiduguri.

Majiyar ta tabbatar da cewa, hatsarin ya yi jawo sanadin mutuwar Mai Kanuri, Alhaji Mustapha Muhammadu, tare da mutum biyu, inda daya daga cikinsu shi ne direban motar, wanda ya samu rauni, shi ma bayan ’yan awanni ya rasu.

Bugu da kari, tawagar gwamnan, wacce ta hada da tsohon gwamnan jihar, Sanata Kashim Shettima, da sauran jiga-jigan gwamnatin jihar suka dauko gawarwakin zuwa birnin Maiduguri.

Haka kuma an yi jana’izar Marigayin Mai Kanuri da kimanin karfe 2.30 na yammacin ranar Talata, a gidansa dake Bulumkuttu a Maiduguri.

Da yake karyata jita-jitar cewa tawagar Gwamna Zulum ta yi hatsari har ya rasu, Kakakin Gwamnan, Malam Isa Gusau, a sanarwar manema labarai da ya fitar da yammacin Talata a Maiduguri, ya ce, “Bakidayan batun da kafar yada labaran gidan rediyon waje ke yadawa a dandalin yanar-gizo, wanda yake nuna cewa yau (jiya Talata) tawagar Gwamna Zulum ta yi hatsari, kuskure ne kuma ba gaskiya ba ne.”

Ya ce, “a lokacin da muke bayyana bakin ciki da alhinin rasuwar Mai Kanuribe na Lagos (Sarkin Kanuri Mazauna Legas), Alhaji Mustapha Muhammad, wanda ya rasu tare da wasu mutum biyu a hatsarin mota a yau Talata, akan hanyar Maiduguri zuwa Mafa a jihar Borno, haka kuma muna shaida wa jama’a cewa ba tawagar Gwamna Zulum ce ta yi hatsari ba.”

Ya sake nanata, bakidayan labarin ba gaskiya ba ne, sannan ko shakka babu Mai Kanuribe ya kudiri tafiya zuwa Mafa, domin bayyana cikakken goyon bayansa ga Gwamna Zulum da jam’iyyar APC.

Har wala yau, Mai Kanuri ya bar garin Mafa kuma a lokacin da yake kan hanyarsa ta koma wa Maiduguri, wanda a daidai wannan lokacin Gwamna Zulum ya na cikin garin Mafa.

Malam Gusau ya kara da cewa, Gwamna tare da Sanata Kashim Shettima da sauran mukaraban gwamnati, akan hanyarsu ta dawowa ne daga Mafa suka yi kicibis da hatsarin, wanda ganin haka ne suka raka gawar Mai, tare da sauran wadanda hatsarin ya rutsa dasu zuwa Maiduguri.

Exit mobile version