Kowa da yadda rayuwar babbar makaranta take zuwa masa, wani ya riski abin da yake zato wani kuma ya ga akasin haka. To shin yaya abin yake ga bakonmu na Duniyar Makarantu a wannan makon? Ku biyo mu cikin hirar kamar haka:
Da farko za ka fara fadawa masu karatu sunan ka tare da dan takaitaccen tarinka…
Da farko dai sunana Safiyanu Muhd Dan Zuru. An haifeni a garin kano unguwar Sauna Nassarawa Local Gobernment na fara makarantar firamare a Sauna Tahfizul Kur’an, sannan kuma na tafi sakandare a Zamfara unguwar dan baba. Duk da irin wahalar da ke cikin karatu hakan bai sa na yi kasa a gwiwa ba, na ci gaba da zuwa makaranta wanda har na yi kokarin gama makaranta a haka, wanda a yanzu ina da matakin diploma guda biyu, Environmental Technology da kuma Pharmacy Techniques a School of Health Technology Birnin Kebbi ne, Ni ba ni da aure a yanzu ina ci gaba da karatuna.
Kafin ka kammala makarantar sakandare, wacce makaranta ka yi sha’awar ci gaba cikin ta, kasancewar Daliban sakandare galibi kan yi kwadayin zuwa wata makaranta ta gaba da sakandare?
Beyero Unibersity Kano, sabida na yi tunanin kowa na cewa BUK shiyasa ni ma na ce ko a sani a layi.
Ko za ka iya fadawa masu karatu abinda ya ja ra’ayin ka har ka bar burinka na shiga makarantar BUK ka koma ga School of Health Technology birnin Kebbi?
To na farko dai mahaifina shi ya yi min alkawarin zai biya min ko nawa ake biya duk inda za a shiga zai shige gaba, kuma Allah da ikonsa sai Allah ya yi masa rasuwa, Allah ya jikansa da rahama ameen. Dalilin da ya sa mahaifina duk abinda za a yi shi ne gaba da komai daga baya da na ga ba ran mahaifina sai na rage buri tun da duk wani abu ya koma kaina shiyasa.
Kafin ka gama sakandare din, me ka yi sha’awar karanta a can farko?
Me ya sa ka ke sha’awar karantar fannin magani?
Sabida ni nafi son fannin magani kuma nafi samun fahimta bangaren magani.
Idan muka koma kan neman admission, ya za ka fadawa masu karatu irin gwagwarmayar da ka sha?
To gaskiya akwai mutumin da yaron babana ne lakcara ne a BUK ya yi min alkawarin admission kuma ya rinka wasa da tunanina sai ya ce naje opis dinsa tinsafe kuma yace na jira shi amma ba zai saurareni ba, in yamma ta yi sai yace in tafi sai gobe, gobe ma haka zai min har na gaji da abinda ya ke min tsawon wata bakwai amma kin san harkar karatu ko admission sai ka na da wani babba shiyasa sabida kasa ta lalace shiyasa na hakura.
Da suwa ka fara haduwa farkon shigar ka jami’ar kuma me ce ce silar haduwar ku?
Akwai Anas, Abba, Jidda da kuma Shamsiyya. Hirar mu ta farko mun fara tattaunawa akan halin da muka tsinci kan mu a rayuwa ta gaba da sakandare. Tun da akwai ban-bancin freedom na wasu abubuwa da sakandare.
Bayan abokan ka da ka fara cin karo da su da wa ka fara abota a farkon shigar ka jami’a?
A farkon da ka fara zuwa Aji, ko za ka iya tuna kusa da wanda ka fara zama, ko kuwa da su abokan na ka da kuka fara haduwa da su ku ka zauna?
Eh duk tare muka zauna.
Na ji sosai na ji yanayin da ban taba jiba sabida yadda ake gabar da darasin. Na ji gabana yana ta faduwa sabida ban saba ba amma na ji dadi daga baya akwai wata yarinya mai suna Aisha ita ce ta kwantar min da hankali sabida haka ta ce duk abinda ban gane ba za ta nuna min.
Wanne darasi aka fara yi muku?
Anatomy
Ya gwagwarmayar zuwa makarantar ta kasance?
Eh to gwagwarmaya akwai ta wajen tafiya kullum ana yi, a takaice dai zan ce ana fama.
Wanne abu ne ya fara baka tsoro ga makarantar Jami’a?
Na ga yanayin kudin mota da abinda zan ci ya na so ya gagareni, kuma na ga abokai na ana kawosu ni kuma sai dai in zo da kaina, kuma yanayin siyan handout shi ma da zafin da darasin da ake yi na ga babanci.
Ko zaka iya tuna sabbin abubuwan da ka fara cin karo da su a jami’a?
Sabbin abubuwa akwai su tun daga yanayin zama a cikin ajin kasan ya banbanta da sauran na baya, ga kuma tsarin zamantakewa duk shi ma wani sabon abu ne, da tsare-tsaren cikin makarantar duk sabo ne wanda na san makarantun baya ba haka tsarin su yake ba.
Ya za ka banban tawa masu karatu rayuwa tsakanin sakandare da kuma ta jami’a?
Toh kamar yadda kowa ya sani tun sakandire ake karatu in kaje jami’a ba zaka sha wahala ba sabida zaka ga abubuwa masu wahala da rikitarwa amma idan ka tuna da karatun da ka yi a sakandire sai ka ga komai ya zo da sauki.
Wa yafi burgeka a cikin Aji, kuma me ya sa?
Anas da Abba sabida sun fini sanin komai amma sai su ka jani a jiki su ke koya min abinda ban iya ba kuma su na da son karatu shiyasa su ka burgeni.
Ta bangaren malamai fa, wanne malami ne yafi burgeki, kuma me ya sa?
Malam Jameel shi ta hanyar da ya ke gudanar da darasin sa ta hanya mai sauki yadda za ka fahimci mai ya ke yi, kuma ya na da wasa da dariya shiyasa ya ke burgeni.
Ya batun jarrabawa shin ka taba fuskantar matsala?
Na taba sabida har lokacin da aka fara jarabawa wasu darrusan ban fahimci inda su ka sa gaba ba.
Ya kaji a wannan lokacin?
Na ji rashin dadi sosai amma daga baya na yi farin ciki sabida Malam Jameel shi ne ya kirani ya ce “me ya ke faruwa?” na yi mai bayani ya ce ba komai zai duba lamarin shiyasa na ji farin ciki.
Wasu mazan su kan ce ba za su auri macen da ta yi jami’a ba, me za ka ce a kan hakan?
Ni a ganina ban ga wani aibu ba a auran mace ta jami’a, sabida rayuwa ta canza sabida yanzu wasu matan da su ka yi jami’a su su ke taimakawa mazansu wanda ba su yi karatu ba.
Ko zaka iya fadawa masu karatu amfanin ci gaba da karatun ‘ya mace a matakin gaba da sakandare?
Ilimin ‘ya mace ya na da amfani sosai domin idan ka ilmantar da ‘ya mace tamkar mutu goma ne, amma jami’a ta na da wani yanayi wanda ya ke na rashi jin dadi.
Idan misali aka ce yau ga ‘yarka ta gama makarantar sakandare, za ka iya barinta ta ci gaba har zuwa Jami’a?
Zan iya bari sabida ban san me za ta zama ba.
Toh ya batun Soyayya fa, ko akwai wanda ya taba kwanta miki a zuciya cikin makarantar da har ta kai kun fara soyayya da shi?
eh akwai sunanta jidda amma fa ban sanar mata cewa ina son ta ba, ita ta nemi mu yi soyayya da ita, ni kuma sai mu ke mu’amala sama-sam ni dai ban tabba ce mata ina sonta ba, ita dai ta na cewa ta na sona.
Idan na fahimceka ka na so ka ce a yanzu babu wata kenan ko ya abin yake?
Babu amma har yanzu muna waya da ita.
Me za ka iya cewa game ga hali da karatu ya ke ciki?
Gaskiya babu dadi sabida duba da yanayin da kowa zai kasance a matsayin karatun zai koma baya.
Wacce shawara za ka bawa masu kokarin shiga manyan makarantu?
Shawarata anan shi ne duk wanda ya ke karatu to ya tsaya ya yi karatu da kyau kar su yi wasa da damarsu.
Mene ne burin ka na gaba game da karatun ka?
Idan na gana ba ni da burin in samu aikin gwamnati sabida ina da kasuwancin da na ke yi shi zan ci gaba da yi amma in na samu zan yi maraba da shi na yi karatu ne sabida ya zamana ka na da ilimi.
Me za ka ce da makaranta wannan shafin na DUNIYAR MAKARANTU?
Ina yi musu fatan alkairi da ‘yan uwa da abokan arziki da fatan za su ci gaba da bibiyar wannan shafi mai albarka.
Me za ka ce da ita kanta jaridar LEADERSHIP A YAU JUMA’A?
ina yabawa wannan jaridar Allah ya kara daukaka da budi akan abinda su ke burin yi.
Ko ka na da wadanda za ka gaisar?
Akwai Khadija wace ake mata lakabi da Ummi ta na zaune a Kaduna da Musa shi ma a Kaduna akwai Auty Saude a Minna.
Mun gode, Ka huta lafiya.