Daga Muhammad Sani Chinade, Damaturu
Al’ummar Jihar Yobe mutane ne waɗanda suka ɗanɗana kuɗarsu daga rikicin ‘ya ‘yan ƙungiyar Yusufiyya waɗanda aka fi sani da ‘yan ƙungiyar Boko Haram, na tsawon shekaru 6, wanda a yanzu kusan za mu iya cewa lamarin ya zama tarihi kasancewar mafi yawan al’ummomin yankunan da suka yi gudun hijira sun koma garuruwansu na asali, musamman ma waɗanda suka fito daga yankunan ƙananan Hukumomin Gujba da Gulani da a baya suke a hannun Boko Haram.
To amma duk da cewar wannan rikici na Boko Haram ya zama tarihi ga al’umma musamman ma garin Damaturu, fadar Jihar da abaya garin ya koma tamfar Kabul na kasar Afganistan, saboda tsananin yawaitar hare-hare masu zafi, da garin ya dinga fuskanta daga ‘yan Boko Haram. A halin da ake ciki al’ummomin wannan yanki na kokawa dangane abubuwan da suke addabarsu, sakamakon iftila’in da suka fuskanta a baya na rikicin Boko Haram, da suka haɗa da rashin aikin yi, tsadar rayuwa da kuma uwa ubansu rashin jari mai karfi daga ‘yan ɓangaren kasuwa.
Kan haka ne wakilinmu ya samu tattaunawa da wasu al’ummar garin da suka tofa albarkacin baki kan waɗanda matsalolin da ke damunsu, inda suka ce saboda rikicin Boko Haram ya kasance sanadiyar halin da suke ciki. Ga kaɗan daga ra’ayoyin al’umman yankin:
To Alhamdulilah a gaskiya kamar yadda ka ce rikicin Boko Haram da mu ka yi fama da shi a wannan yanki na mu, na Yobe da ma wasu Jihohin maƙwabta irin su Jihar Borno da Adamawa da ya haifar mana da matsalar taɓarɓarewar harkokin tsaro, lalle ya zama tarihi to amma kuma lamarin ya bar baya da ƙura saboda a halin da ake ciki yanzu mu al’ummomin wannan yanki musamman garin Damaturu garin da na ke mafi yawa-yawan mu, muna fuskanta wasu matsaloli da in ba an kawo mana taimako ba, sai mu iya cewa har yanzu tsugunne bata ƙare ba.
Gaskiyar magana kaga dai lalle Allah cikin ikonsa ya raba mu da wannan rikici na Boko Haram da taimakonsa da kuma taimakon jami’an tsaron da suka jajirce a wannan karon bugu da ƙari mun yi sa’ar samun shugaban ƙasa Muhammadu Buhari. To amma in ba an yi hoɓɓasan kawar da manyan matsalolin dake addabar mu da suka haɗa da rashin aikin yi, da tsadar rayuwa da kuna karancin jari ahannun ‘yan kasuwa ba to ai kaga akwai sauran lale. Babbar mafita ita ce dole na in gwamnati da gaske take to akwai bukatar samar da aiki ga matasa don rage shaye-shaye da sace-sace da kuma samar da abinci cikin sauki ga al’umma kana a kuma samar da jari ga ‘yan kasuwa ko da rance ne. To matukar anyi hakan za a samu sa’ida.
Oga Karumi (Shoe Shiner):
To sha’anin yanzu sai muce mun gode wa Allah amma agaskiya a halin yanzu jama’a na cikin halin matsuwa.
Kamar yadda ka sani wato matsalar tsadar rayuwa kasancewar samun kuɗi al’amarin yayi ƙaranci, kuma farashin kayayyakin abinci ya wuce yadda kowa yake tsammani, yadda abubuwa na neman gagarar mai ƙaramin ƙarfi musamman ma talakka. Ka san shi dama ya saba da halin hannu baka hannu ƙwarya.
To a gaskiya babban abin da nake sa rai akan wannan lamari shi neroƙon Allah muke yi akan ya kawo mana ɗauki kamar yadda ya kawo, manataimakon kawo ƙarshen rikicin Boko Haram, su ma Hukumomi watogwamnatocin jiha jiha da ta Tarayya su gaggauta ɗaukar wani mataki da aka san zai kawo ma al’umma kwanciyar hankali.
Malam Musa Alhaji Adam:
Abin da nake nufi ai a baiyane yake ba a ɓoye ba domin a halin daake ciki hatta mu dake harkar Kasuwanci muna ji a jikin mu saboda kuwa harkar ciniki gaskiya, ba kamar yadda yake acan baya ba.
A ganina abin da ya haifar da wannan ai bai wuce halin matsin
rayuwa ba da muke fatan Allah cikin ikon shi ya kawo mana sauki yai mana taimako.
Abubakar Ɗan Ngamdu:
Al’amuran rayuwa a yanzu da a baya ai sai ayi shiru kawai.
Tun kawo ƙarshen ta’addancin Boko Haram a Yobe matsalar tsadar rayuwa ta
sako mu agaba a nan yanki, wadda mun san lamari ne daga Allah. Fatan mu
ya kawo mana ɗauki.