Connect with us

RIGAR 'YANCI

Yadda Ruwa Sama Ya Rusa Gidaje Fiye Da 200 A Kebbi

Published

on

A jiya ne aka tabka ruwan sama daya bakin kwarya a wasu sasan jihar ta Kebbi inda ruwan saman da iska mai karfin gaske ya lalata da kuma rusa gidajen na Miliyoyin Nairori fiye da 200 a unguwar Badariya da unguwar Bayan Kara da ke a karkashin karamar Hukumar mulki ta Birnin-Kebbi a jiya.
Ruwan Sama da iskan da ya zama sanadiyar lalata matsugunan Miliyoyin Nairori na mutane a Birnin-Kebbi an kwashe kimalin Sa’o’i biyu zuwa uku iska da ruwa na barnata gidajen jama’a kafin, ‘yan uwa da abokan arziki su kai dauki ga mutanen da wannan matsala ta ruwan sama ta shafa. Kamar yadda bayyanai ke fito wa daga mutanen da matsalar ta shafa sun nuna cewar ruwan sama da iska mai karfin gaske ya soma ne da misalin karfe 6 zuwa Bakwai da rabi na daren jiya. Haka kuma wata majiya kuma na cewa iska yafi ruwan sama karfi saboda haka suna ganin cewa shine sanadiyar rusa gidajen da kuma lalacewa .
daya daga cikin gidajen da suka samu wannan matsalar a unguwar Badariya shine matsugunnin ‘yan sandan jiran ko ta kwana wata (mopol Barracks) wanda har wannan matsalar ta shafi gidan Dogarin Gwamnan jihar ta Kebbi ,Sanata Abubakar Atiku Bagudu a cikin gidajen na mopol Bariki da ke a unguwar Badariya. Bayan faruwar wannan Lamari wakilin LEADERSHIP Ayau ya samu ziyarar wuraren da wannan lamarin ya shafa a unguwar Badariya da kuma unguwar Bayan Kara don sanin yawan gidajen da suka samu matsala.
Hakazalika a zagayen da wakilin namu ya gudanar a basamu rahoton rasa rayuwa ba sai dai an samu asarar dukiyoyin Miliyoyin Nairori kama tun daga gidaje, kayan daki na mata, tufafin sawa da kuma abinci da sanadiyar iska mai karfin gaske ya lalata a wadannan unguwanni biyu da ke a karkashin karamar Hukumar Mulki ta Birnin-Kebbi.
Bugu da kari yayin zagayen da wakilin namu ya samu yin kicibis da Shugaban karamar Hukumar Mulki na Birnin-Kebbi, Alhaji Aminu Ahmad Magatakarda ya kawo ziyarar jaje ga jama’ar da matsalar ta shafa da kuma daukar mataki na ganin cewar an samar da wani tallafin gaggawa ga jama’ar da abin ya shafa. A cikin jawabin da shugaban karamar Hukumar na Birnin-Kebbi ya gudanar ga jama’arsa ya ce” jama’a karamar Hukumar Birnin-Kebbi na jajanta muku kan wannan matsala da ta same ku ta rasa gidajenku sanadiyar iska da ruwan sama da aka samu a jiya da dare.
Shugaban ya cigaba da cewa, “jama’a kuma mai da wannan al’amarin ga Allah domin shine kawai ke da karfin iko na yin hakan, saboda karamar Hukumar ta irin arsarar da kuka yi na gidaje da kuma sauran wasu dukiyoyin na miliyoyin Nairori”.
Bisa ga hakan, a matsayina na shugaban karamar Hukumar mulki ta Birnin-Kebbi na bada umurnin cewar” duk wanda wannan matsalar ta shafa muna son ya nemi mai unguwar su domin a rubuta sunansa da kuma abubuwan da yayi arsara su, domin mun gayawa dukkan masu unguwa yanzu hakan zan kara gayawa Uban Doman-Gwandu domin ya kara jaddawa dukkan masu unguwa na Badariya da Bayan Kara domin tabbatar da an gaggauta hada sunayen wadanda wannan matsala ta shafa, inji shugaban karamar Hukumar”.
Shi ma a nashi jawabin shugaban Hukumar Bada agajin gaggawa na jihar Kebbi wato (State Emergency Management Agency), Alhaji Sani Dododo ya ce” mun ziyarar ci dukkannin wuraren da aka samu wadannan matsalar Badariya da kuma Bayan Kaya wanda mun ga irin asarar da jama’a suka yi kama daga gidaje da kuma sauran wasu dukiyoyin na makudan miliyoyi, saboda haka muna mika gai suwar mu ta jajen abin da ya samu wadannan ‘yan uwanmu na wadannan unguwanni biyu, inji shi”. Ya ci gaba da cewa “ tabbas jama’armu sun tabka asara mai dinbin yawa amma muna kira garesu da su maida wannan al’amarin ga Allah, domin shine zayi mafi ta da yardasa.
Ya kuma cewa, “mun hada kai da shugaban karamar Hukumar mulki na Birnin-Kebbi da kuma Ubandoman Gwandu don samun tsarin cikakun sunayen dukkan wadanda matsala ta shafa don basu agajin gaggawa domin idan ka duba dukkanin wadanda abin yashafa matsakaitan talakawa ne da mafi yawansu basu da wani matsugunni bayan wannan da iska ya lalata musu, inji shugaban SEMA na jihar.”
Har ilayau ya kara da cewa” kamar yadda karamar hukumar mulki ta bada umurni ga dukkan masu unguwa dasu tabbatar da sun rubuto sunayen dukkan mutanen da matsalar ta shafa haka itama Hukumar SEMA tayi hakan don a tabbatar da duk wanda gidansa ya samu matsala ya shiga cikin jerin sunayen da za ‘a rubuto ta hannun masu unguwa . Domin ba ma son sai mun fara bada tallafin gaggawa a ce wani bai samu ba.
Saboda haka muka bada dama ga masu unguwa su rubuto sunaye domin duk wanda ya samu asara masu unguwa sun sanshi.
Daga nan Alhaji Sani Dododo ya kara da cewa “ makasudin zagayen gaggawa da hukumarsa ta gudanar domin aikin na gaggawa ga wadannan mutanen da wannan al’amarin ya rutsa dasu da a turance muke kiransa (rapid assessment). Daga karshe ya ce “ kawo yanzu hukumarsa bata tantance gidaje nawa ne suka rusa ba. Amma bisa ga abinda wakilinmu ya gano wa idanunsa gidaje fiye da 200 sun lalace a tsakinin unguwani biyu da wannan matsala ta faru a jiyan.
Haka kuma wakilinmu ya samu jin ta bakin wasu daga cikin wadanda abin ya shafa a unguwar Badariya . Inda Malam Aliyu Muhammad da kuma Malama Aisha Haruna sun bayyana cewar” iska da ruwan sama aka yi a jiya mai karfin gaske da yayi sanadiyar lalacewar gidaje da kuma roshe wa acikin sa’o’i biyu zuwa uku da iskan da ruwan saman ya taso . bisa ga hakan ne muka rasa gidajenmu da kuma sauran wasu dukiyoyinmu . yanzu haka bamu da wani matsugunni bayan wannan da iska da ruwan sama ya roshe muna, inji su”.
Saboda hakan sun yi kira ga gwamnatin jihar ta kuma hukumomin da abin yashafa don basu agajin gaggawa, sun ci gaba da cewa shugaban karamar hukumar mulki da kuma shugaban hukumar Bada agajin gaggawa na jihar sun kawo muna ziyarar jaje da kuma bayyana muna cewa sun bada umurni ga masu unguwa cewa duk wanda wannan matsala ta shafa ya tabbatar da cewa an rubuta sunansa da kuma abubuwan da suka lalace .
Advertisement

labarai