Connect with us

LABARAI

Yadda Sa Bakin Lawan Da Gbajabiamila Ya Dakatar Da Kara Kudin Lantarki

Published

on

Karin da a ka so yi ta hanyar ribanya kudin da masu amfani da hasken lantarki suke biya a kasar nan wanda aka so fara yin amfani da shi daga yau din nan, an dakatar da shi.

Hakan ya biyo bayan sa bakin da shugabannin majalisun tarayya na kasar nan ne suka yi a wani taron da suka yi da kamfanonin da suke rarraba hasken lantarkin (DisCos), hukumar samar da hasken lantarkin (NERC) da sauran masu ruwa da tsaki a wannan fannin a daren ranar Litinin.

A karshen makon nan ne kamfanonin rarraba hasken lantarkin suka bayar da sanarwar cewa karin kudin lantarkin da aka tsara yi tun daga ranar 1 ga watan Afrilu, zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Yuli.

Kamfanonin sun aike da sakon hakan ga masu amfani da hasken lantarkin ta kafafen yada labarai.

Amma masu amfani da hasken lantarkin, masu masana’antu da sauran su duk sun yi ta kokawa a kan karin kudin lantarkin da ake shirin yi wanda suka ja musu da cewa ba zai haifar da da mai ido ba, domin zai shafi harkokin kasuwanci a irin wannan mawuyacin yanayin.

Amma kamfanonin da suke rarraba hasken lantarkin sun dage a kan cewa biyan kudin lantarkin yanda ya dace shi ne kadai zai iya tabbatar da wanzuwa da inganta wannan sashen na lantarki.

Taron na su na ranar Litinin wanda shugaban majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya shugabance shi tare da rufa bayan Kakakin majalisar wakilai ta kasa, Femi Gabajamiala.

Sun kuma yi alkawarin kai koken kamfanonin rarraba hasken lantarkin gaban shugaban kasa, Muhammadu Buhari, sannan suka bukace su da su jinkirta yin karin kudin lantarkin har zuwa watan Afrilu na shekarar 2021.

Sanarwar bayan taron na su ta jiwo Lawan yana cewa, tabbas gwamnati tana bin hanyoyi masu yawa domin sauke nauyin da ke kanta domin samar da abubuwan da za su saukake rayuwa.

Ya ce: “Ina da masaniya kwarai da gaske, a wannan shekarar kadai ko daga shekarar da ta gabata, sama da Naira biliyan 600 ne gwamnati ta kebe wa wannan sashen na lantarki domin inganta shi.

“Yin karin kudin lantarki tabbas wani abu ne da ya kamata ya dauki hankalinmu a majalisun tarayya.

“Akwai wahalhalu masu yawa a kan ‘yan Nijeriya a yanzun haka, har ma a Duniya bakidaya a sabili da bullar annobar korona, ko ma kafin wannan akwai matsalolin da za su tsananta wa ‘yan Nijeriya in aka yi karin kudin lantarkin.

“Ko mun ki, ko mun so, matukar ana son inganta sashen ta yanda zai jawo hankulan masu son zuba jari, tilas ne sai an yi karin, babu shakka a kan hakan, amma matsalar ita ce a wane lokaci ne ya dace a yi hakan.”

A cewar sanarwar, Gbajabiamila ya ce, “Komai akwai lokacin da ya dace a yi shi. Duk wani tsari mai kyau na gwamnati yana iya baci in aka aiwatar da shi a lokacin da bai dace ba.

“Duk wani abu da zai iya shafan wannan gwamnatin, abu ne da ya kamata ya dami kowane guda daga cikinmu. Ina ganin kuma wannan karin in an yi shi zai iya shafan wannan gwamnatin.

“Yin karin a wannan lokacin sam bai dace ba. Ina ganin zai iya shafan gwamnatin Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, don haka matukar kuwa zai shafi gwamnatinsa, ya kamata duk mu rufa masa baya da al’ummar kasarmu, da Shugaban kasa da gwamnatinmu domin tabbatar da ba a samu wata tangarda ba.

“Maganar dai ita ce, duk mun aminta da cewa tilas ne mu yi wani abu a kan tasadar lantarkin.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: