Shugaban kungiyar harhada magunguna ta Nijeriya ‘PSN’ reshen Abuja, Jelili Kilani ya gargadi mutane da su rage yawan shan kwayar magani da ake kira ‘Paracetamol’ ko ‘Panadol’ inda yake cewa yana yi wa Huhu da kuma kodar mutum mummunar lahani.
Kilani ya bayyana hakan ne lokacin da yake hira da kamfani dillancin labari na Nijeriya a Abuja.
Ya ci gaba da bayanin” Misali haiyar kwayoyin ‘Panadol’ uku zuwa hudu da wasu kan yi musamman don kawar da gajiya kan samar da matsala ga Huhu da kodar mutum. Sannan kuma mutum ba zai san illar da maganin yayi masa ba sai ya dauki wani lokaci mai yawa tukuna.”
Ya kara da cewar kuma ce illar da maganin ke yi a jikin mutum ba a iya gane hakan da wuri sai bayan an yi shekaru masu yawa.
Yace kamata ya yi a sha wannan magani kamar yadda likita ya bayyana , hakanan kuma sai akan dalilin cutar da ta kamata.
Daga karshe Kilani yace idan har dai sai an sha ‘Panadol’ sau daya kuma ba a sami sauki ba, ai kamata ya yi a tuntubi likita domin samun tabbacin cutar da take damun mutum.