Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Yadda Shark Ya Hadiye Mai Ninkaya Tsawon Dakika 30 Kafin Ya Amayo Shi

by
8 months ago
in JAKAR MAGORI
3 min read
Shark
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Wani mai Ninkaya ya bayyana yadda wani kifin Shark ya hadiye daga baya kuma ya yi amansa.

Mutumin mai suna Michael Packard ya ce, yana cikin ninkaya ne a cikin kogin Probincetown dake , Massachusetts ta kasa Amurka, sai kwai babban kifin ya nufo shi kafin ya ankara kuma sai kawai ya ji shi a bakin kifin, ya kuma hadiye shi na tsawon akalla dakika 30 zuwa 40 kafin ya kuma amayar da shi. Cikin ikon Allah bai ji wani mummunan ciwo ba sai targade a gwiwarsa.

Michael Packard ya yi akalla shekara 40 yana aikin nikaya a cikin kogi, duk kuwa da cewa, matarsa ta dade tana neman ya canza sana’a saboda irin hatsarin da ke tattare da ninkaya a cikin ruwa.

Labarai Masu Nasaba

Kotu Ta Tsare Mutum Shida Bisa Laifin Kisan Kai

An Daure Wani Dan Kasuwa Saboda Cin Mutuncin Gwamnan Jihar Adamawa

Bayani daga Gidauniyar kula da gandun daji “World Wildlife Fund” ya nuna cewa, kifin ‘Humpback whales’ ya kan kai tsawon mita 15 ya an kuma iya kaiwa nauyin tan 36, ana kuma kyatata zaton sun kai 60,000 a fadin duniya.

“Ba zato ba tsammani, na ji wannan babban kifi, kuma komai na ga komai a duniya ya yi duhu,” in ji shi. A cewar majiyar WBZ-TB News.OUND

Da farko ya yi tunanin wani kifin ne ya kawo masa hari, domin manyan fararen fata suna yawan zuwa wurin, amma nan da nan sai ya fahimci hari ne amma ba wanda zai ji cizon hakora ba.

“Daga nan sai na gane, ‘Wayyo Allah na, ashe ina cikin bakin kifin … kuma yana kokarin hadiye ni,’ ‘Kamar yadda Packard ya shaida wa WBZ-TB News. Ya ci-gaba da cewa “Kuma na yi tunani a raina cewa, wannan ita ce ranata ta karshe kawai zan mutu.'” Tunanin Packard ya koma ga matarsa da ‘ya’yansa maza biyu, masu shekaru 12 da 15.

Ya kiyasta cewa a halin yanzu ya kasance cikin tarko a cikin bakin lebiathan na dakika 30, kuma har yanzu yana iya yin numfashi ta cikin injin numfashinsa.

Amma sai ya ji alamar kifin kamar yana cikin damuwa kuma yana son cire abin da ya hadiya ba a son ransa ba, kuma ya kasa cin abinci, domin ya hadiyi wani bakon abu, don haka ya hau girgiza kai sannan ya amayo da shi.

Ya ce, “Ni kawai ji na yi an jefar da ni cikin iska kuma na ji ni da sauka a cikin ruwa.” “Na sami ‘yanci kuma kawai sai na kama yin iyo a can gefe abin da ban taba zaton yi ba.

An dawo da Packard a cikin jirgin ruwan kamun kifi ta hannun abokin aikinsa, wanda ya kasance cikin damuwa yana binciken saman ruwa don alamun kumfa daga injin iskar odygen na Packard yana ta bayyana, lamarin da ya alamta wa abokin nasa shaida.

Abin mamaki, Packard ya tsira daga wannan hadari ba tare da wani rauni in ban da buguwa da ya yi a gwiwa.

Ganin cewa kowace irin halittar ruwa na iya hadiya, amma zai yi wuya a ce ta hadiya kuma ta fito da shi, sai dai Packard ya dan yi sa’ar fitowa daga cikin wannan kifi.

Duk da kasancewa daya daga cikin manyan nau’in kifayen girmansa har ya kai zuwa kafa 60 (mita 18), kuma an auna nauyinsa ya kai misalin tan 40, ya zama abu mai ban sha’awa (metric 36) da manyan motocin bas za su iya dauka, sabanin kananan halittun teku kamar kananan kifi, krill da plankton, ma’ana makogwaronsu yawanci inci 4 zuwa 8 (santimita 10 zuwa 20) ne kawai.

Maimakon hakora, dabbobin ruwa da suke wata wasu halittu masu kama da kusoshi 270 zuwa 400 da ake kira farantin baleen.

Suna farauta ta hanyar bude bakinsu zuwa kusan digiri 90 kafin su yi huci cikin sauri tare da saurin juya wutsiyarsu.

Wannan huci yana haifar da jan ruwa wanda ke tilasta afkawar ruwa cikin bakunansu.

Bayan sun rufe mukamukansu, akwai kuma wasu hanyoyi da suke fitar da ruwa ta ciki kafin su hadiye sauran abin da za su hadiye, kuma wadannan kifayen na iya tsotsar ruwa da yawa.

Jeremy Goldbogen, masanin ilimin halittu kuma babban Daraktan tashar jirgin ruwa ta Hopkins a Jami’ar Stanford a California, ya gaya wa Live Science a cikin imel., cewa  “Don haka kumburinsu na iya mamaye duk wani abu mai nutsewa cikin ruwa a sauki, lamari da bai fiya faruwar a gaban mutane ba.”

Wani kwararren masanin kifin ya fada wa majiyar Live Science cewa haduwar da Packard yayi da wannan kifi ba a saba gani ba, kuma hatsari ne wanda zai iya faruwa yayin da yake iyo kusa da wata “kugiya ” kwallon da sardines ke haifarwa yayin da mafarauta shi ke haifar masa da barazana ta kowane bangare.

“Kwallon bait na iya samuwa a cikin ruwa mai kwaranya wanda kuma yake kusa da kasa. Sannan kuma kifayen da suke cikinsa na farawa ta hanyar kiwo a kasan ruwa cikin yankuna da yawa.

Watakila ba za su iya ganin abu ba,” kamar mai nutsewa, Hector Guzman, masaniyar kimiyyar ruwa a ‘Smithsonian Tropical Research.’ Cibiyar a Panama, ta fada wa masana Kimiyyar Rayuwa.

Iyakar kifin da ke iya cinye Dan’adam gaba daya mai yiwuwa ne kifin ruwan mai suna Spem Whale, sanannen batun Moby Dick da aka sani yana hadiye abin da yake cinye masa abincinsa, wani kato ne mai nauyin kilogram 400, sai kuma wani kato mai nauyin kilogiram ana kiransa skuid (180).

A takaice dai shi Packard bai taba fuskantar irin wannan mummunan yanayi ba, kamar yadda ya shaida wa Libe Science ta ruwaito a baya.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

An Kama Ma’akacin Lafiya Da Ake Zargi Da Yi Wa ‘Yan Ta’adda Magani A Katsina

Next Post

ASADUL MULUK

Labarai Masu Nasaba

Kotu

Kotu Ta Tsare Mutum Shida Bisa Laifin Kisan Kai

by
9 months ago
0

...

Gwamnan Jihar Adamawa

An Daure Wani Dan Kasuwa Saboda Cin Mutuncin Gwamnan Jihar Adamawa

by
9 months ago
0

...

EFCC

EFCC Ta Gurfanar Da Wanda Ake Zargi Da Damfarar Naira Miliyan 425 Ta Intanet A Gaban Kotu

by
9 months ago
0

...

Tarbiyyar Yara

‘Yan Uwa Sun Kashe Matashiya A Indiya Saboda Ta Saka Wandon Jins

by
10 months ago
0

...

Next Post
Muluuk

ASADUL MULUK

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: