Shugaban Hukumar bada taimakon gaggawa ta kasa ya bayyana cewar rasuwar Shugaban kamfanin jaridar LEADERSHIP, Sam Nda Isaiah wani babban rashi ne, inda kuma ya bukaci iyalansa da kuma su, ma’aikatan jaridar da suyi hakuri hakane Allah ya so saboda shine mai badawa da kuma amshewa.
Wasikar ta’aziyar wadda take dauke da sa hannun shugaban Hukumar ta NEMA, ritaya ABM Muhammadu Mohammed ya ja hankalinsu da cewar duk wani halin da suka samu kan su, sai su godewa Allah akan duk abinda ya faru.
Kamar dai yadda ya ce “Ina mai isar da gaisuwar daukacin ma’aikatan Hukumar bada taimakon gaggawa ta kasa, wani al’amari ne wanda ya girgiza hankalin mutane, wanda kuma labari ne wanda yake na jimami, dangane da rasuwar dan’uwanmu marigayi Sam Nda-Isaiah wanda ya rasu ranar 11 ga watan Disamba 2020.
“Hukuma tana da bukatar da ku ci gaba da hgakuri da irin halin da kuka kasance bayan rasuwar ta sa, don haka muna kira gare ku da ku, da cewar ku ci gaba da hakuri dukkan al’amuran daga Allah suke.
Rasuwar Sam Nda Isaiah wani babban rashi ne ga aikin jarida da kuma kasa – SEC
Hukumar sayar da hannun jari ta kasa ta bayyana rasuwar Shugaban kamfanin jaridar LEADERSHIP a matsayi wani babban rashi ga aikin jarida da kuma kasa gaba daya.
Hukumar a cikin wasikar data aiko kamfanin jaridar LEADERSHIP shekaran jiya a Abuja dauke da sa hannun Shugaban Hukumar Lamido Yuguda, ya bayyana cewar za ayi matukar rashin sa.
Yaguda ya bayyana cewar ya samu labarin rasuwar ne cikin bakin-ciki
.
Kamar Dai yadda ya bayyana “Dokta. Sam Nda-Isaiah gogaggen dan jarida ne kuma ya daga aikin jarida, bugu da kari kuma ya iya tafiyar da harkar mulki, da harkar yadda siyasa take a Nijeriya.
Ministan watsa labarai da al’adu Alhaji Lai Mohammed ya mika gaisuwar ta’aziyyar sa ga Iyalan mawallafin jaridar LEADERSHIP Sam Nda Isaiah, wanda ya ce mutuwar sa wani abin tayar da hankali ne, musamman ma idan aka yi la’akari da yadda yake da farin jinin al’umma.”.
Alhaji Mohammed a cikin takardar ta ‘aziyar wadda aka kawo ma LEADERSHIP a Abuja, ya ce kasar tana jimamin rasuwar sa, amma kuma kada a manta da amfani da ayyuka nagari daya ke yi lokacin rayuwar sa.
Ya kara bayanin cewar yin abubuwa nagari da ya yi shi ne babban abinda za ayi a rika tunawa da shi.
Kamar dai yadda ya ci gaba da bayani, “Lokacin da muke nuna jimamin rabuwa da wannan bawan Allah wanda ya samu nasara akan abinda yasa gaban sa, da kuma yadda ya tafiyar da rayuwar sa.
“Tabbatar da ci gaban abubuwa nagari da ya yi shi ne babban abinda za ayi domin tunawa da shi koda yaushe.’’
“Gare ni kamar dai yawancin abokaina, mutanen da nake hulda dasu, sai kuma masu fatan alkhairi ga shi mawallafin, rasuwar ta shi wani abu ne mai tayar da hankali.”
Nigeria tayi rashi wani babban gwarzo mai kishin kasa, kuma kwararre – NCPC
Babban sakatare na Hukumar aikin ibada ta bangaren Kiristoci Rabaran Yakubu Pam yana mika ta’ziyar sag a Shugabanni da kuma daukacin ma’aikatan jaridar kamfanin LEADERSHIP, dangane dsa rasuwar mawallafinta kuma Shugaba Sam Nda-Isiah.
Rabaran Pam a cikin takardar ta’aziyyar daya aiko shekaran jiyain, ya bayyana cewar ko shakka babu kasa tayi wani babban rashi saboda mutuwar dan kishin kasa kuma kwararre.
Shi kuma Etsu Nupe, mai martaba Alhaji Yahaya Abubakar ya nuna rashin jin dadinsa akan rasuwar mawallafin jaridar LEADERSHIP Sam Nda Isaiah, inda kuma yake cewar za a rika tuna shi sosai akan ayyukan sa.
Abubakar ya ci gaba da bayanin cewar shi mutum ne wanda baya da nuna bambanci wanda ya shafi addini ko kuma kabilanci, saboda kuwa ya taimakawa matasa maza da kuma mata wajen cimma burin su.
A cikin takardar ta Etsu Nupe wadda Etan Nupe, Ambasada Solomom Adama Yisa da kuma Dan Masani Raba Nupe, Muhammad Kudu Abubakar suka kawo, ya bayyana cewar ko shakka babu za ayi kewar sa, saboda dalilai masu yawa, saboda kuwa ya yi iyakar kokarin sa na ganin an fahimci manufarsa. Musamman ma ta bangaren siyasa, inda yake dan kishi kasa, domin shi kuwa ya tsaya ne kan kasancewar Nijeriya matsayin kasa daya, inda yin adalci, daidaituwar komai ba tare da bambanci ba, ba kawai ana cewar ayi su bane su kasance ma ana yi ne a bayyane.
Ya cigaba da bayanin cewar kasancewar sa matsayin dankasuwa, mai hada kan nal’umma, mai muradin yin al’amurra akan dacewa lokacin rayuwarsa, rasuwarsa ba karamin rashi bane ga kasa saboda kuwa zamu dade bamu manta da wannan ba.
Wani babban abin tafiya ne da yayi fice ta harkar watsa labarai- KADOBA
Kungiyar tsofaffin daliban makarantar kwalejin gwamnati ta Kaduna, a madadin kwamitin zartarwa da kuma dukkan mabobi na kwalejin gwamnati ta Kaduna, muna mika ta’aziyar gaisuwar rasuwar marigayi Sam Nda-Isaiah.
A takarda ta’aziyar wadda ke dauke da kwanan wata na 16 ga watan Disamba, 2020 wadda kuma Komrade Aliyu Dangiwa, ya sa ma hannu aka kuma aiko ta zuwa ga iyalan kungiyar ta ce “Mun rubuta wannan takardar ne saboda mu yi maku ta’aziyya dangane da rasuwar dan’uwanmu, wanda muka yi makaranta tare, marigayi Sam Nda-Isaiah, mu mkuma nuna rashin jin dadinmu akan rasuwarsa ranar 11 ga watan Disamba 2020.
“Ita wannan babbar kungiya tamu tana alfahari da Mista Sam Nda-Isaiah saboda kuwa yana daga cikin mabobi wadanda suka yi fice, musamman ma a bangaren daya shafi watsa labarai, wannan kuma kowa ya san ya nuna shaharar shi ta wannan bangaren.
“Wannan za a iya tunawa da yadda ya kafa jaridar LEADERSHIP wadda ta kasance fitila ce leka gidan kowa, ta kuma kasance wani babban alfahari ne ga ita wannan kungiyar ta tsofaffin daliban kwalejin gwamnati, saboda kuwa wata kafa ce ta sadarwa na labarai a Nijeriya.’’
Ya kara jaddada cewar Nda-Isaiah ya bayar da gaggarumin cigaba na habakar ita kungiyar ta bangaren jiha da kuma kasa baki daya.
‘’Kwamitin zartarwar ko shakka babu ta san cewar rasuwar tasa zata bar babban gibi ba wai kawai ga Iyalansa ba, har ma da wadanda suka kasance abokan huldarsa, kowa zai yi kewarsa musamman a wannan lokaci da ake bukatar taimakawarsa.
“Bugu da kari kuma mun san da cewar wannan lokaci da kuma shi yanayin da muke ciki, wani al’amari ne da yake da matukar wuya ga su mabobin iyalan shi marigayi dan’uwanmu, don haka muke rokon Allah da ya cigaba da baku hakuri da kuma karfin zuciya wajen jure shi wannan rashin daya same mu.”
Nda Isaiah mutum ne mai son samun canji a Nijeriya – Osita Chidoka
Tsohon ministan harkokin jiragen sama Osita Chidoka ya mika gaisuwar ta’ziyar sa ga iyalai da kuma ma’aikatan jaridar LEADERSHIP inda kum ayake cewar shi marigayi Nda- Isaiah wanda yake muradin ganin an samu canjin yadda aiwatar da al’amura a Nijeriya.
Da yake magana lokacin da ya kawo ziyarar ta’aziyya a hedikwatar kamfanin LEADERSHIP shekaran jiya a Abuja ya bayyana cewar lokacin da yaji labarin mutuwar shi marigayi Sam Nda-Isaiah bai yarda bane da farko.
Tsohon Ministan ya bayyana shi a matsayin wani mutum ne da yake da shawarwari masu amfani, da kuma shi al’amarin da yake damun sa shi ne ta yadda za a iya samun wani canji a kasar Nijeriya wanda zai kara sawa ta bunkasa.
Chidoka ya kara baynain cewar shi babban abinda ya dame shi shi ne yadda kasar zata cigaba da kasancewa tsintsiya daya madaurinki daya.
Ya kara yin bayani inda kuma yace “Lokacin da naji labarin ya rasu sai na kasance ina wasi- wasi al’amarin. Wannan kuwa ba domin komai ba sai don shi mutum ne da ya damu da halin da kasa take ciki, sai kuma yadda za ayi maganin matsalolinta.
“Duk kuwa da yake akwai bambambance- bambance na yadda kowannen mu yake kallon yadda al’amuran matsalolin kasa suke tafiya, amma kuma sannu a hankali sai muka fara fahimtar juna, daganan kuma sai muka fahimci cewar kowa yana da giudunmawar da zai niya badawa. Amma sai an gwada aka san na kwarai.
“Shi mutum ne da yake da shawarwari masu amfani don haka mun ba shi goyon baya domin ya samu wata dama da zai kawo amfanin su.
“Al’amari kasa shine abinda yafi damun sa bama kamar shi al’amarin ganin an samu canji na yadda ake fatiyar da al’amura bama kawai sai harkar mulkar al’umma ba wanda kuma hakan na iya sa kasa ta kai ga bunkasa.”
Nda-Isaiah Shi ne mai bukatar samun hadin kan Nijeriya da China- Jakadan kasar China
Jakadan kasar China na Nijeriyamai kula da harkokin kasar a Nijeriya, Zhao ya bayyana cewar marigayi Sam Nda-Isaiah shi wanda yake gaba- gaba ne a al’amarin dangantakar kasar China da Nijeriya.
Yong ya bayyana bakin cikinsa dangane da rasuwar wadda ya kafa jaridar LEADERSHIP ranar jumma’a data gabata 11 ga watan Disamba, sai kuma mika gaisuwar ta’aziyarsa ga iyalai da kuma daraktocin kamfanin da kuma ma’aikatan shi na kafar watsa labarai ta jarida.
Ya bayyana cewar “Mista Sam wani aboki ne mai kirki na shi ofishin jakadanci a tsawon shekaru masu yawa bugu da kari kuma Jakadun kasar China masu yawa wadanda, suka zauna da kuma yi aiki a Nijeriya.
“’ Shi ne kumawanda yake gaba- gaba a harkar kara bunkasa dankon zumunci tsakanin kasar China da Nijeriya.”
Nda-Isaiah Shugabane da ya kasance a al’amura da yawa ne- Dakuku
Tsohon Shugaban Hukumar NIMASA, Dakuku Peterside, ya bayyana cewar marigayi Sam Nda-Isaiah shi mutum ne da yake yake taimakwa wajen yin wani abu, kuma har ila yau yana al’amura masu yawa da yake bayar da tashi gudunnawar ga kowa.
Dakuku a cikin takardar ta’aziyya ya bayyana cewar “Bamu shiryama wannan al’amarin day same mu ba, amma kuma duk da hakan mun san babu abinda zamu iya cewa saboda Allah shi ke da komai da kowa, da kuma akwai lokacin mutuwar kowa.
“Kowa dai ya san mutuwa wata abu ce wadda sirrinta babu wanda ya isa ya yi ko kuma ce wani abu, faramu ita ce Allah ya kyautata masa.
“Shine ya kafa ita wannankamfanin jaridar LEADERSHIP wanda kuma ya san ba zai iya kasancewa a wurin har abada ba.
Ya kuma kalubalanci darektocin kamfanin da kuma ma’aikata cewar su kasance masu taimakawa wajen bunkasar shi kamfanin koda bayan mutuwar sa ne.
“Saboda kuwa wani lokaci wadanda suka kafa wani wuri ko kuma kamfani ba kasafai suke kammala abubuwan da suka kamata su kasance a wurin ba, domin haka kamata ya yi mu cigaba da wurin daya tsaya, basmu kawo mutuwar wurin ba.
“Ina mai kira da cewar mu yi kokari mu kai wannan kamafin jaridar zuwa ga mataki na gaba, kwanaki kadan kafin rasuwar say a kaddamar da mambobin tawagar jaridar turanci mai suna National Economy, wadda kuma ita ma ‘yar’uwace ta jaridar LEADERSHIP.
Ya kuma yi kra da su mambobin gudarwa na ita jaridar cewar su hada kansu wajen gudanar da ikin ita jaridar ba domin komai ba, sai saboda babu mutum daya da zai iya cewar shi ya san komai.
Nda-Isaiah shi Shugaba ne wanda ya yi fice sosai – BPE
Hakanan shima Shugaban Hukumar sayar da kamfanonin gwamnati Aled Omoh ya bayyana rasuwar marigay Sam Nda-Isaiah cewar shi ya kasance jagora ne abin koyi, bama kamar idan aka yi la’akari da yadda kokarinsa da taimakon Allah ya mayar da jaridar LEADERSHIP wadda ana iya cewar ta cimma tsara inda kuma ta kasance abar yin koyi da ita idan aka kalli masana’antar watsa labarai a Nijeriya.
Shugaban wanda ya bayyana yadda ita mutuwar ta mawallafin jaridar LEADERSHIP Mista Sam Nda-Isaiah ta kasance ma shi inda kuma ya ce “ An san shi a matsayin mutum wanda yake da shwarwari masu amfani idan aka yi amfani da su saboda shi aganin sa babu wani abinda za a sag aba da niyyar sai an cimma burin danagane da shi, da zai iya gagara.’’