Yadda Sojoji Suka Kashe Kwamandan ISWAP A Damasak

Daga Sulaiman Ibrahim

Wani babban kwamandan ISWAP, Bukar Gana (wanda aka fi sani da Abu Aisha), da dimbin mayakan sa da ke neman ramuwar gayya a Damasak, sun fada hannun sojojin Najeriya a ranar Alhamis yadda suka hadu da ajalinsu.

Dan ta’addan da mayakan sa sun hadu da ajalinsu ne yayin da suka dawo daukar fansar manyan kwamandojin ISWAP 12 da aka kashe a Karamar Hukumar Mobbar ta jihar Borno a cikin wani harin sama da kasa na tsawon mako guda da sojojin Nijeriya suka yi.

Wata motar ISWAP kenan da tasha wuta

A cikin ruwan bama-bamai ta kasa da kuma kai hare-hare ta sama da sojojin Nijeriya suka yi a wurare daban-daban a yankin Arewa maso Gabas, ‘yan ta’addan basu sami wata mafaka ba ta cigaba da kai hare-hare akan Gajiram da Damasak.

Mummunan harin sama da sojojin suka kai a kan Tudun Wulgo, Zari da Tumbun Alhaji, Kusuma, Sigir dake Ngala da Arijallamari, Abadam, Marte dake karamar hukumar Ngala, ya kai ga kashe manyan Shugabannin ISWAP.

Kwamandojin da suka halaka a harin na sama sun hada da; Mohammad Fulloja, Ameer Mallam Bello, Ba’a kaka Tunkushe, Abu Muktar Al -Ansari, Ameer Abba Kaka, Abu Huzaifa, Ameer Modu Kwayem, yayin da Goni Mustapha wanda shi ne Babban Limamin kungiyar ISWAP ya tsere da rauninkan harsashi.

Exit mobile version