Rabiu Ali Indabawa" />

Yadda Sojoji Suka Kashe Mayakan Boko Haram 81 A Sambisa

sambisa

Sojojin Nijeriya da suke yaki domin kawo karshen mayakan Boko Haram a dajin Sambisa, sun samu nasarar hallaka mayakan kungiyar har 81 a cikin dajin. Sai dai, ‘yan kungiyar sun hallaka soja daya a wani harin nakiya da suka harba kan sojojin. Rundunar sojojin ta kuma fatattaki wasu daga cikin ‘yan kungiyar da dama zuwa dajin, yayin da hakan ya tilastawa dakarun kungiyar juya baya, kamar yadda kafofin yada labarai suka shaida.

Kafar yada labarai ta PRNigeria ta ruwaito cewa a yayin da mayakan kungiyar ke kokarin tserewa ,sun lalata gidaje tare da kona wasu. Majiyar ta ci gaba da cewa, dakarun sojojin dai sun tarwatsa kauyukan ‘yan ta’addar da dama a yankin garin Bello, Kwoche, Lawanti da Alfa Bula Hassan da Alfa Cross da dai sauransu.

PR Nigeria ta ce wata majiyar leken asiri ta ce sojojin sun gamu da tirjiyar mayakan na Boko Haram wadanda suka ajijiye abubuwan fashewa a hanyar da dakarun Nijeriyar ke bi. Kuma a nan ne soja daya ya rasa ransa, hudu suka samu manyan raunuka. Babban hafsan soji Mejo Janar Ibrahim Attahiru ya yabi sojojin bisa jumurinsu da kwazonsu da jarumtaka, sannan ya bukaci da su ci gaba da jurewa.

A wani bangaren kuma, PR Nigeria ta ruwaito wasu mayakan Boko Haram dake tserewa sun afka wa kauyukan Zira da Gur a Karamar Hukumar Biu ta Kudu a Jihar ta Borno. Mayakan sun shiga garuruwan ne da misalin karfe 4:30 na yammacin Lahadi a kan babura da motocin yaki sannan sun kona gidaje da dama yayin da mazauna kauyukan suka tsere cikin daji domin tsira da rayukansu. Amma daga baya an samu dauki daga jirgin yakin rundunar sojan saman Nijeriya inda suka fatattaki ‘yan bindigar ta hanyar kai musu ta sama.

Exit mobile version