Abubakar Abba" />

Yadda Ta Kaya A Taron Bajekolin Noman Albasa Na Katsina

A makon da ya gabata ne aka gudanar da taron baljekolin Albasa a jihar Katsina, inda kuma taron ya samu halarcin manoman Albasa da dama.
Taron na baje kolin an gudanar dashi ne a karkashin inuwar kungiyar masu Sa ido kan Sha’anin Albasa ta Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya tare da hadak da kungiyar Manoma Albasa da Kasuwancinta ta Nijeriya sun yi taro na farko a bana a Jihar Katsina.
Manufar shiyar taron shine, farfado da rashin tsari kan kamfanonin sarrafa albasa a kasashen Afirka ta Yamma da Afirka da ta Tsakiya da suke fama da shi.
kasashe kamar su Benin, Cote d’iboire, Ghana, Mali, Nijar da kuma Togo duk sun halarci taron na bajekolin.
A jawabinsa a wurin taron, Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya sanar da cewa, Katsina, jihar manoma ce wadda ke da akalla kashi 80 cikin 100 na manoman Auduga da gyada da masara da gero da dawa da sauransu.
Masari wanda mai ba shi shawara a fanin kasuwanci, Alhaji Abubakar Yusuf ya wakilce shi a wurin taron ya ci gaba da cewa, ya ce jihar ta shahara a wajen noma kayan lambu wanda ake fitar da su zuwa kasashen waje; tun kafin 1960 inda albasar da kowa ya san amfaninta na daga ciki.
Ya ce, Jihar Katsina na da kasar noma kimanin kadada miliyan 2.4, amma kadada miliyan 1.6 ake nomawa, saura dubu 800 na nan a matsayin fili.
Ya kara da cewa, akwai madatsun ruwa 80 da ke dauke da ruwa kwatankwacin murabbain lita miliyan 1.121 domin noman rani, inda ya kara da cewa, noman albasa zai kara bayar da damar samar da ayyukan yi a tsakanin al’umma da kuma kara bunkasa tattalin arzikin kasa.
Ya ce, Katsina ta samar da wani kwamiti a kan hadaka da kamfanoni domin inganta harkokin noma, inda ya kara da cewa, an kuma samar da masu horarwa a kan harkar noma a dukkan mazabun da ke jihar.
Sa’annan gwamnati za ta ci gaba da yin nazari a inda ake samun wasu matsaloli domin shawo kansu domin gaba,inda Kuma gwamnati na shirye ta tallafa wa noman albasa a duk fadin jihar.
Shima a nasa jawabin a wurin baje kolin Shugaban kungiyar ta Afrika, Alhaji Mustafa kadiri, ya ce, wannan kungiya tasu na da manufar farfado da darajar noman albasa tare da habaka harkokin kasuwancinta.
A cewar Shugaban kungiyar ta Afrika, Alhaji Mustafa kadiri, Sannan sun zabi Jihar Katsina ce don su yi taron kungiyar na farko na 2020 ne tun a taron da suka yi a Sakkwato a bara bisa la’akari da muhimmancin da jihar ke da shi.
Shugaban kungiyar ta Afrika, Alhaji Mustafa kadiri, ya sanar da cewa, ya lura da yadda Gwamna Masari ke ba harkar noma muhimmanci.
A karshe, Shugaban kungiyar ta Afrika, Alhaji Mustafa kadiri ya sanar da cewa, akalla ana bukatar tan miliyan 1.2 na albasa daga Najeriya; sai dai har yanzu tan miliyan 1.1 ake samu.

Exit mobile version