Khalid Idris Doya" />

Yadda Tagwaye Suka Nemi Yin Rufa Ido A Jarabawar JAMB A Maiduguri

Daga Khalid Idris Doya

An cafke wasu tagwaye masu suna Hassan da Hussaini a garin Maiduguri a lokacin da ake tsaka da gudanar da jarabawar share fagen shiga jami’a.

’Yan biyu ne an kamasu da zargin satar amsa a yayin gudanar da  jarabar samun izinin shiga manyan makarantu wato (UTME) a cibiyar zana jarabawar da ke jami’ar Maiduguri babban birnin jihar Borno, lamarin ta faru ne a ranar Asabar a ciki gaba da zana jarabawar a Nijeriya.

Babban jami’in da ke kura da jarabar ta JAMB, Mr. Babagana Gutti, shi ne ya shaida hakan wa kamfanin dillancin labarai ta Nijeriya, ya bayyana cewar ‘yan biyun jami’an tsaro ne suka kamasu a ranar Asabar din a garin na Maiduguri.

Gutti ya ce, ‘yan biyun sun yi amfanin da kamanninsu inda suka so su yi wasan rainin wayo wa jami’an, a yayin hakan ne kuma jami’an tsaron suka bankado shirinsu, inda aka ga daya a waje, aka shigo cikin dakin zana jarabawar ma aka sake ganin irin wannan fuskar, wannan dalilin ne ya sanya masu lura da zana jarabawar suka sanya shakku kan wanda suka tarar na zanawa, hakan ne ya janyo hankulansu bincike da dan gudanar da tambayoyi.

“Dan ya zo cibiyar zana jaraba a madadin dan uwansa, ka san suna kammani”.

Jami’an kula da jarabawar ta JAMB ya ci gaba da bayanin cewar Hussain Abdulhammeed wanda aka kama a sakamakon shaidar shigar da bayanai ta gwaji na na’ura mai kwakwalwa (CBT), ya kara da cewa, shi kuma dan uwansa mai suna Hassan Abdulhameed ya shiga zana jarabawar a madadin dan uwansa Hussaini ne.

Ya ce, “Gaskiyar magana mu ba mu iya ganowa ko kuma zargin hakan ba, har sai da daya daga cikin masu bibiyar jarabawa ya zo domin bincike sai yake shaida cewar sun gano dayan yana wajen hall din zana jarabawar,”

“Izowar mai binciken ya tambayesa wasu ‘yan kalilan din tambayoyi kan jarabawar da kuma bayanai amma bai gamsu da amsoshin da ya bayar ba; don haka ne ya fito da wanda yake zana jarabawar da kuma dayan da ke kama da shi a wajen domin bincike. Abun mamaki kuma sai muka samu bincike ya nuna cewar Hassan ya zo wajen zana jarabawar a madadin dan uwansa Hussaini ne,”

Shugaban da ke sanya ido kan jarabawar, wato Gutti ya bayyana cewar nan take ne kuma suka yanke hukuncin dakatar da jarabawar ‘yan biyun gami da kuma mikasu ga jami’an tsaro don ci gaba da bincike.

Hassan da Hussainin dai sun dan baiwa jami’an wahalar ganewa, kasantuwarsu masu kammanin da junansu.

Exit mobile version