Idris Umar">

Yadda Taron Hisba Na Yini Biyu Ya Gudana A Zariya

Kungiyar Hisba ta kasa reshe karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna ta gudanar da taron karawa juna sani na yini 2.

Wakilin LEADERSHIP A YAU ya na daya daga cikin wakilan kafafen yada labarai da suka halacci wajan taron kuma ya aiko mana da tsaraba don amfanar masu karatunmu.
Taron an farashi ne a makarantar Commacial College da Sabon Gari Zariya kuma dubban mambobin kugiyar ne daga kananan hukumomi suka sami halattar taron.
Taron anyi mashi lakabine da hanyar da za a gane ban-bancin hukunce-hukuncen Musulunci da na dokar kasa.
Malamai masana shari’ar musulinci da lauyoyine suka gabatar da mukaloli a wajan taron dake da alaka da sanin dokoki.
Barista Abubakar Usman na daya daga cikin lauyoyin da suka gabatar da mukala a wajan taro  inda mukalar tasa ta janyo hanlalin kungiyar ta Hisba dasu samar da wani sashi dake da ilmin Shari’ar a bagaren addini da dokar kasa yace, hakan shi zai taimakawa kungiyar wajan kaucewa kalubaten dake cikin irin kokarin da suke gudanarwa a halin da ake cikin a yanzu.
Bubban limamin masallacin Jumm’a dake  garin Samaru Barista Shanwil Muhammad Nasir na cikin manyan malamai masana ilmin  Shari’ar Islama da domoki  kasa shima mukalar tasa ta kumshi sanin babbance-banbacen dokokin kasa da dokokin Shari’ar Islama.
Kuma yayi jawabi mai tsawo gaske dake karfafa neman ilmi da muhimmancinsa ga ita kungiyar Hisba da sauran al’umar musulmi baki daya.
Sashin cibiyar ma’aikanan kashe gobara ta kasa ta sami halattar taron shugaban su mai suna U.Muhammad ne ya jagorancesu inda ya nuna jin dadinsa da irin wannan taro tare da gabatar da mukalar sa akan muhimmamcin sanya hankali yayin aiki da iskan gas na dafa abinci da hita mai amfani da wutan lantarki yace, a halin yanzu sune ke gaba wajan tayar da gobara mai girma a cikin al’uma inda yayi fatan jama’a zasu kula da hakan karshe yayi fatan Allah ya bayar da hadin kai a tsakaninsu wajan gudanar da aikin dake gabansu.
Injiniya Muhammad Usman shine shugaban karamar hukumar Sabon Gari a nasa jawabin da ya aiko dashi ta bakin mai taimaka masa a harkar siyasa da yada labarai Alhaji mai Zinaru yace, kungiyar Hisba kungiyace da suke yabon aikin da suke gudanarwa kuma sunyi alkawari bata goyan baya da ikon Allah kuma ya ja hankalinsu da suji tsoron Allah a dukkan aiyukansu yace haka zaisa su sami dacewar Uban gijinsu.
An karkare taronne a bubban dakin taro na sakateriyar karamar hukumar ta Sabon Gari dake Dogarawa Inda wakilin namu ya ji dalilin shirya taron daga wajan kwamandar Hisban na karamar hukumar ta Sabon Gari malama Abubakar Awwal Adam.
Daga farko shigaban ya nuna godiyarsa ne ga Allah daya basu ikon ganin wannan rana kuma yace, makasudin shirya wannan taro shine don karawa juna sani ne akan Shari’ar Musulunci da dokokin kasa da ake amfani dasu a kasarmu Nigeria.
Yace sanin su zai taimakawa Yayan kungiyar sosai yayin gudanar da aikinsu.
Kwamandan ya yi matukar yabo ga masana Shari’a da suka zo suka shayar da mombobi su ilmi kyauta wajan taron. Kuma ya mika godiyarsa ga shugaban karamar hukumar Sabon Gari bisa kokarin da yake masu a bangarori daban-daban.
A karshe ya yi jinjina ga Yayan kungiyar tare da karrama wasu daga cikinsu bisa bayar da lokacinsu da dukiyarsu wajan ci gaban Hisaba a karamar hukumar Sabon Gari da kasa baki daya, kuma ya yabawa jama’a bisa goyan baya da ake basu yau da kullum.
An yi taro lafiya an tashi lafiya.

Exit mobile version