Hukumar Samar da Abinci Bunkasa Noma ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da wani nazarin da ta gudanar na tsadar kayan abinci da kuma tashin farashin kayan abincin ya yawancin kasashen duniya.
Ta sanar da cewa, binkicken ta ya tabbatar da cewa tashin farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi ya tashi a cikin watan Fabrairum 2021, inda ta yi nuni da cewa, hakan ya na nufin kenan an tsafe watanni 9 farashin ya na hauhawa sama, bai ragu ba.
Har ila yau, bincike ya nuna kayan da su ka fi tashi sama sun hada da sugar da man girki, inda hukumar ta kara da cewa, farashin kayan abinci a watan Fabrairu ya tashi da kashi 2.4 fiye da watan Janairu, wato kashi 26.5 bisa 100 fiye da farashin shekarar da ta gabata daidai wancan lokacin.
Yayin da farashin sugar ya tashi sama a cikin watan Janairu saboda yawancin kasashen da ke yin sugar sun kasa wadatar wa duniya sukarin, inda ta kara da cewa, wannan karancin sukari kuma ta sa jama’a da dama shigo da sugar kasashen su daga Nahiyar Amurka.
Ta sanar da cewa, daga cikin kayan da farashin su ya kara hauhawa a duniya, har da kwakwar man ja da mayuka da dama, inda kuma a kasashe da dama ciki har da Amurka, farashin seralak da cizi ya karu da kashi 1.2, kamar yadda a Afrika farashin jar dawa ya karu da kashi 17.4, saboda tsananin bukatar ta da ake yi a kasar Chana.
Hukumar ta ci gaba da cewa, farashin masara da na alkama ya dan tashi amma kadan a yawancin kasashen duniya sun karu, inda ta bayyana cewa, farashin naman miya da sauran naman kayan kwalama da tande-tande da lashe-lashe, sai dai kuma abin mamaki shi ne yadda darajar naman alade ya ragu a duniya, musamman a kasashen Turai.
Bugu da kari rahoton ya bayyana cewa, hakan ya faru saboda kasar Chana ta rage sayen naman da al’ummar kasar su ka yi, inda kuma kasuwar naman alade ya fadi warwas a Jamus, ana barin masu sayar da nama da tulin naman alade babu mai saye.
Bugu da kari, binciken ya sanar da cewa, lamari kuwa ya faru ne saboda wasu dalilai da su ka hada da haramta shiga da naman alade da aka yi a wasu kasashen Asiya da dama.
A wata sabuwa kuwa, Cibiyar gudanar da buncike kan yayan itatuwa ta kasa ta janyo matasa da mata dake zaune a babban birin tarayyar Abuja don horas da su kan yadda zasu samu riba a noman Tumatir da ganyen Ugu.
Horon kuma ana son zai nunawa matasan da kuma matan yadda zasu noma amfani da kuma yadda za su samu riba bayan sunyi girbi.
Babban Darakta a Hukumar Dakta Abayomi Olaniyan a jawabinsa a yayin bude horon a babban birnin tarayyar Abuja ya sanar da cewa, horon ya hada da horas da mahalartan sa yadda zasu shuka Irin Tumatir da ganyen telfairia bisa yadda ya dace don sanun riba mai yawa.
A cewar Babban Darakta a Hukumar Dakta Abayomi Olaniyan horon ya kuma hada da, yadda za su samu karin tattalin arzikin daga amfanin biyu, noman su da kuma samar masu da kasuwa.
A cewar Babban Darakta a Hukumar Dakta Abayomi Olaniyan, bayar da horon yana da matukar mahimmanci, idana akayi la’akari da amfanin gonar biyu wadanda ake yin amfani dasu a kullum musamman wajen abinci mai gina jiki da kuma mahimmancin su wajen bunkasa tattalin arziki.
Babban Darakta a Hukumar Dakta Abayomi Olaniyan ya cigaba da cewa, babu wata tantama, Tumatir yana daya daga cikin kayan lambu da ake nomawa a Nijeriya, inda kuma Babban Darakta a Hukumar Dakta Abayomi Olaniyan ya kara da cewa, ana kuma sarrafa shi zuwa abubuwa da dama.