Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta na cikin sababbin jami’oi da su ka yi zarra ta kowanne bangare na ci gaba da dawo da martabar jami’ar a idon al’umma, saboda jajircewar shugabanta, Farfesa Armaya’u Bichi, don sadaukarwarsa da kishinsa. Amma duk da wannan nasara da cigaban da makarantar ta samu a hannu daya ta na fama da shari’a da tsohon mataimakin jami’ar ta Dutsinma, Farfesa Haruna Abdu Kaita, ya kai a gaban Kotun Masana’antu da ke Kano (Industrial Court), inda ya ke kalubalantar dakatar da shi da a ka yi.
Bayan an yi shekara uku a na shari’a ita, kotun da ke Kano ta yanke hukuncin cewar an yi wannan dakatarwar a kan ka’ida kuma ta ba shi rashin gaskiya kan cewar tunda a ka kafa kwamiti na bincike ya kamata ya tafi ya saurari kwamitin ya kare kansa, amma ba ya ki zuwa ba tunda ya ki zuwa duk da an kira shi sau da yawa lokacin zaman kwamitin, inda daga bisani su ka zauna suka kama shi da laifi, sannan ’yan majalisar jami’ar su ka yi amfani da rahoton kwamiti su ka dakatar da shi. Don haka Bayan an yanke shari’a kan dakatar da shi ya yi dai-dai.
Amma a banagaren Farfesa Haruna Kaita sai ya nuna hukuncin bai yi ma sa ba. Don haka ya kuma daukaka kara zuwa Kotun Daukaka Kara da ke Shiyyar Kano, kuma ya roki kotu ta yanke hukuncin a cikin gaggawa saboda, ‘tenure’ dinsa za ta kare a 12 ga watan Fabarairu 2021.
Ita ma Kotun Daukaka Karar bayan ta yi zamanta a ranar 4 ga Disamba, 2020, dukkan alkalan uku a karkashi Mai Shari’a Amina su ka yanke hukuncin cewa kotun kasa ta yi daidai a dakatarwar da a ka yi ma sa kuma an yi bisa ka’ida ne, sannan an bi doka.
“Babban abin da na sa gaba shi ne yadda gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta mayar da hankali akan aikin noma don haka tsangayarmu ta aikin noma muka yi mata kyakkyawan tanadin da muke hasashen wannan sashen zai kara da dukkan irinsa da ke fadin kasar nan.
“Don mu na da hazikan malamai masana da masu bincike da za su yi bincike musamman a bangaren noman shinkafa da auduga da gyada wanda wadannan abubuwa su ne iyayenmu da kakanninmu suka gada kuma duk tutiyar arzikin kasar nan da shi aka fara tun kafin man fetur. Don haka mu ke da yakinin yin hakan zai kawo ma kasarmu da al’ummarmu arziki za a ji dadi, a samu aikin yi matasa su daina zaman banza za a samu ci gaba. Wannan shi ne burinmu na farko.
“Sai kuma abu na biyu da muke son mu yi shi ne bude Faculty of Medicine da Law da ‘Engineering’ shi ma kamar yadda gwamnatin shugaba Buhari ta ke ta fafutukar ta ga an samu ci gaba a bangaren mu ma mun sa wannan kudirin a gabanmu. Fatanmu mu horar da dalibai da za su ja ragamar kasar nan a gaba.
“Abu na uku da shi ma muka sa a gaba tare da ba shi muhimmanci shi ne maganar Entrepreneur yadda matasanmu za su dogara da kansu ba tare da sai sun tsaya jiran aikin gwamnati ba. A wannan sashen a yi masa tanadi na musamman da kayan da duk ake bukata da za a koyar da daliban sana’oi daban-daban kuma a tabbatar da sun kware a kai. Wannan ba karamar dama ba ce wajen dalibanmu don samun abin dogaro da kansu.
“A karshe, mu na gode wa Allah, mu na gode wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da mai gayya mai aiki Ministan ilimi Malam Adamu Adamu muna godewa ES na NUC Farfesa Abubakar Adamu Rashid wadanda duk suka tsaya mana suka bayar da goyon baya a wannan shekara uku zuwa hudu na wadannan shari’oi mun godewa Allah mun godewa duk wanda ya taimaka mana da goyon baya da fatan alheri da addu’a na samun rinjayen wannan shari’ar.
Allah ya ci gaba da daukaka jami’ar tarayya ta Dutsim-ma. Amin.”