Bello Hamza" />

“Yadda Wani Fasto Ya Damfare Ni Naira 500,000’’

Damfara

A ranar Larabar makon jiya ne wani ma’aikacin gwamnati mai suna Bictoria Akyenewga, ta bayyana wa alkalin kotun majastare da ke garin Gwamgwalada Abuja, cewa, wani Fasto mai suna  Hosea Bodam, ya yaudare ta ta yadda ya karbe mata Naira 500,000.

Akyenewga ta yi wannan zargin ne a yayin ci gaba da shari’a Bodam, in da ake tuhumarsa da cin amana, zamba cikin aminci da kuma cuta.

Lauya mai gabatar da kara ya jagorance ta inda ta bayyana cewa kotu a shekarar 2016, Faston ya kira ta inda ya yaudare ta da sunan wani abin mamaki na alhairi na nan zuwa gareta, ta haka ne ya karbe mata kudaden.

Dan sanda mai gabatar da kara ya ce, laifukkan sun saba wa sashi na 312 da 332 na dokar fanet kot.

Bayan sauraren bayanan dukkan bangare, Alkalin kotun, Aliyu Shafa, ya nada wani lauya mai suna M.B Omioigbo ya yi sulhu a tsakanin bangarorin ya kuma dawo da rahoto ga kotu, ya kuma daga karar zuwa ranar 31 ga watan Maris donkarbar rahoton sulhun.

Exit mobile version