Wani abin bakin ciki ya faru yayin da wata yarinya ‘yar shekaru uku ta yi arangama da wani kare, wanda ya bar iyayenta cikin hawaye yayin da take gaya musu cewa yanzu ta munanta.
Ronin Gordon-Waldroup ta yi arangama da karen ne a gaban wani gidan abinci da ke garin Tedas a gaban iyayenta, a yayin da suka firgita.
Mahaifiyar yarinyar mai suna Cleberetta ta bayyana cewa, ‘yarsu tasu tana gaban su ne kadan don yin odar kayan abinci lokacin da karen ya tunkare ta.
Wani mashaidi ya fadawa ‘Local12 News’ cewa, haka kurin karen ya cafki fuskar yarinyar, a inda mai shi ya ja wuyarsa wanda hakan ya tilasta karen sakin yarinyar kamar wata ‘yar tsana.
Baya ga haka ne mahaifin ta mai suna James ya bi mai dabbar a guje a kan titi yayin da yake kokarin guduwa, in ji kafofin watsa labarai na cikin gida. Yarinyar ta kasance a kwance cikin jini kuma tana bukatar dinka 15 a fuskarta.
Ronin na bukatar tiyatar filastik, kuma ana fatan cewa tabon zai zama kadan a fuskarta. Bayan ta fara samun saki, yarinyar ta kan fashe da kuka yayin da ta gaji da yin amfani da kayan shafa don rufe raunukan ta.
Mahaifiyarta ta ce, “Akwai lokacin da ni da mijina muka shiga cikin dakin kwananmu muka ga tana rike ga buroshin kwalliyata, tana kokarin rufe wurin da tabon raunukan suke. Yadda diyata ‘yar shekara ukun takan zo wurina ta ce min mama na munana, yana tayar min da hankali.”
A halin yanzu, mazauna garin sun hada hannu don tara kudin tallafa wa yarinyar a harkar asibiti. Ya zuwa yanzu, masu fatan alheri sun tara zunzurutun dala 13,349 zuwa dala 100,000, tare da daruruwan mutane da ke shigowa ciki.
Shafin ya ce, “Ina rokon a yi adalci wa karamar yarinyar nan. Ronin tana da shekaru 3 kuma dole ne ayi ma ta dinka 15 a fuskarta! Idan za ku iya taimakawa ta kowane fanni koda kuwa karamin abu ne za mu zama masu godiya, ta yadda za mu iya biyan kudin daukar matakin shari’a da kuma ci gaba da biyan kudin asibitin ta.”
Wani mai ba da gudummawa ya ce, “Ina da jikoki kuma zan shiga matukar damuwa idan wannan harin ya faru da su. Zamu ci gaba da addu’a ga wannan yarinyar.”
Wani ya kara da cewa, “Ina da ‘ya ‘yar shekara 3. Shi yasa nake jin irin yanayin da kuka shiga. Ku yi hakuri, ina ma ta fatan murmurewa ba tare da ta barin tabo a daya fuskarta ba.”