WALIDA AHAMAD" />

Yadda Wasu Kawaye Ke Lalata Tarbiyyar ‘Yan Mata

Tarbiyyar 'Yan Mata

Sanannen abu ne cewa, mata akwai su da son tara kawaye barkatai, wannan kuwa ba ya rasa nasaba da tun daga tasowa yarinta za ka ga yaro yana da son dan’uwansa yaro, wadda har idan a ka hadu za ka ga suna shaukin junansu. Haka za a yi ta tafiya har girma,  lokacin girma kuma lokaci ne da ya kamata iyaye su sakawa ‘ya’yansu ido su ga da wa suke mu’amala sannan su waye kawayensu da suke rayuwar yau da kullum da su?

Na zabi na yi magana a wannan bangare na ‘ya’ya mata da tara kawaye barkatai ina mafita ganin yadda mu mata mune iyaye muke zama da yara a gida muke tarbiya sabanin iyaye maza da suke fita neman abun hasafin da za su sauke takalifinmu da na ‘ya’yanmu.

Ana fama da tabarbarewa tarbiyya a wannan lokacin, ta ina gizo yake sakar?Wace hanya ya kamata mu bi domin a gudu tare a tsira tare?     Yawan tara kawaye barkatai ya na taka muhimmiyar rawa wajen tabarbarewar tarbiya da jefa rayuwar ‘ya’ya mata a cikin hadari.

Na halarci wani zama da aka yi a kan tabarbarewar tarbiyar yara. An kuma tattauna batutuwa masu muhimmancin gaske dangane da hakan. Wani a cikin mahalarta taron sai yake cewa, “Akwai sadda yake tafe ya hadu da wasu yara mata, ga su dai sun yi shigar kamala amma suna tafe suna cin cingam.Wasu kuma kaga suna tafe suna daga sautin muryarsu wadda ke nesa dasu sai ya ji abin da suke fadi, Ko dai ya zama ana tafiya ba cikin natsuwa bazar-bazar wanda hakan sam bai dace da ma’abutan addini ba.

Wanda mu addinin Musulunci ya koyar da mu komai, hatta yadda mace za ta yi tafiya, sai da addini ya koya mana to,idan ya zamanto ba mu bin koyarwar  addinin,haka ba mu siffantuwa  da shi ba, to ya ya lamari zai kasance kenan?

Duk irin wannan tabarbarewa baya rasa nasaba da tara kawaye barkatai.

Na’am addinmu ya koya mana yadda zamu so junanmu, ‘yan uwantaka da girmamawa a tsakaninmu,kuma a kawaye akwai nagari

ana samun yaran da  ko Mahaifiyarsu basu fada mata damuwarsu, amma suna fadi ma kawarsu ta basu  shawara mai kyau su dauka, su yi amfani da ita kun ga a nan za mu ce, madallah da kawaye na gari.Ita kawa ta na tasiri ga kawarta sosai da sosai,wasu iyayen suna bakin kokarin wajen tarbiyar ‘ya’yansu,  kawaye su na ruguzawa.Kina cikin hayyacinki da kamalarki da dabi’unki na kirki  masu kyau,  sai ki watsar ‘kawa  ta nuna miki ba ki waye ba,ko ke ba ki san zamani ya ci gaba ba, ya barki k baya. Shikenan ke kuma abun nema ya samu, sai ki canza kema ki koma diyar zamani.

Shi harkar zamani kada-ram-kada- ham ake yi, kada me gani ya taka makaho.

Ba in da aka ce karki yi kawaye, abin da ake cewa, shi ne, cikin kawayen na ki da kika tara sai ki duba su waye masu dabi’u kirki, halin arziki da mutuncin, sai ya zama sune kawayenki abokan rayuwarki.

Su kuma masu mummunar dabi’a kokari za kiyi ki shiryar da su, karki yarda su rinjayeki.

 

Duk a in da kike kiyi kokari, ki dauki abin da yake shi ne dai-dai.

ki dauki fari ki ajiye baki.Hakan shi ne abunda ya kamata ki yi.Su mutane ko kawaye arziki ne babba a rayuwarki,amma fa sai kin rika kula da yin taka-tsantsan da rayuwa da su.A nayi da kai yafi ace ba’ayi da kai limamin gari ya koma San’kira.

 

Ga iyaye kuma, ga shawarwari guda uku a gare su;-

1.Ku rika sanyawa ‘ya’yanku mata idanu sosai domin sanin kawayen da suke mu’amala da su.

2.Ku yi kokarin sauke hakkin ‘ya’yanku musamman iliminsu,tufafinsu da sauran bukatu dai-dai iyawarku.

3.Ku rika yiwa ‘ya’yanku nasiha a kan hakuri da jarabawar rayuwa,rashin dogon buri,da wadatar zuci.

4.ku rika Yawan yi wa yara addu’o’i nagari da sanya musu albarka a yayin da suka aiwatar da ayyuka masu kyau da nagarta.

5.Ka ku rika daurewa ‘ya’yanku fuska,a’a ya zamanto wajibi a gare ku ku kusanto da su da jan su a jikinku ta yadda za ku san damuwarsu har ku iya magance ta.

6.A kwai bukatar kula da kawayen ‘ya’ya mata na Makaranta musamman bincikar halayen su a yayin da suke zuwa gida bayan tasowa daga  makaranta.

Wadannan batutuwa da muka kawo dukkanin uwa da uba sun yi musharaka a cikin hakan,amma ga wasu shawarwari guda biyar wadanda suka shafi Mahaifiya ita kadai:-

1.Ki zamantowa diyarki mace tamkar kawarta ta hanyar jan ta a jiki da sakar mata fuska,hakan zai sanya ta saki jiki da ke da bayyana miki halin damuwa ko farin cikin da take ciki.

2.A sadda kika fahimci yarinyarki ta kai shekaru 9-12 a dai-dai lokacin nan akwai bukatar ki kira kusanto da ita kusa da ke,saboda a lokacin ne ake tsammanin za ta fara jinin al’ada,sannan jikinta zai fara canzawa daga siffar yarinya zuwa siffofi  na Budurwa.

3.Da zaran kin fahimci ta kai shekaru 9-10 zai yi kyau ki bayyana mata ce wa  za ta iya ganin jini ya bayyana a gare ta,ko a farkon wata,ko a tsakiyarsa ko kuma a karshensa,ya kamata kuma da zaran ta gani ta sanar da ke domin ki bayyana mata yadda za ta tsaftace kan ta.

4.Ki gargade dangane da  hadarin namiji wanda ba muharraminta ba ya taba jikinta a sadda ta kai wadancan shekaru.

5.Ki bayyana mata yadda ake amfani hukunce-hukumcen shari’a da suka hau  kan ta a wannan marhalar da ta ciki.

6.Ki tarbiyyantar da ita dangane da sa hijabi ko wani Mayafi da zai suturce mata jikinta da bayyana mata hadarin yin tabarruji.

7.Ki rika gayyatar ta wajen koya mata ayyukan gida,kamar dafa abinci sharar gida da sauran ayyukan ta yadda za ta sa ba da wadannan ayyukan,saboda wata rana dai sannu-sannu za ta tafi gidan miji.

Tabbas dukkanin ‘ya’ya maza da mata amana ce mai girman gaske ga iyaye,amma shari’ar Musulunci ta fi son a  fi bayar da kulawa mai gamsarwa ga ‘ya’ya mata saboda muhimmancinsu a zamantakewar al’umma.

Exit mobile version