Connect with us

KIWON LAFIYA

Yadda Wasu Likitoci Suka Gano Maganin Cutar Kanjamau  

Published

on

Wasu likitoci a asibitin ‘Beth na Israel Massachusetts’ da ke kasar Amurka sun gano maganin cutar kanjamau ‘antiretrobiral therapy (ART)’ wanda ke iya warkar da maras lafiya gaba daya daga cutar.

Likitocin dai sun bayyana cewar shi maganin ya hana kwayoyin ne su hayayyafa a jikin mutum har na tsawon har shida.

Shi dai binciken ya nuna cewar gaskiya ne idan wanda ya kamu dacutar ya daure da shan maganin zai iya warkewa gaba daya daga cutar.

Shugaban su wadannan likitocin Dan Barouch ya wani karin bayani ne inda ya ke cewar sun gano haka ne bayan binciken da suka gudanar a jikin wasu birai 44.

Ya cigaba da bayanin cewar, “bayan mun tabbatar da wadannan birai sun kamu da cutar kanjamau sai muka fara ba su wannan maganin, bayan kuma makonnin 96 sai muka ga cewa kwayoyin cutar ba su hayayyafa ba tun bayan lokacin da muka fara ba su maganin. Hakan kuma ya nuna cewar cutar bai ci gaba da yi wa garkuwar jikin su wani lahani ba.

“Daga nan sai muka rarraba su zuwa gida biyu inda rabi mu ka cigaba da ba su tsohon maganin cutar kanjamau, sai kuma rabin mu ka cigaba da ba su sabon maganin na tsawon har makonin 16.”

Dan Barouch ya bayyana cewar sakamakon da suka samu ya nuna cewar kwayoyin cutar sun kara yawa a jikin kashin biran da suka yi amfani da maganin da a ke amfani da shi a da, kashin da aka ba su sabon maganin kuwa, ba a ga kwayoyin cutar a jikinsu ba gaba daya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: