Yadda Wasu Matasa Masu Hikima Suka Samar Wa Jihar Katsina Tambarin Hoto

Za mu mayar da abin doka a fara amfani da shi – Masari

Daga Sagir Abubukar, Katsina

 

Jihar Katsina, ta bi sahun jihohi 28 na Tarayya Nijeriya wajen samar da babban tambarin da za ta sanya a matsayin wanda za a dinga amfani da shi a ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jihar.

Alhaji Faisal Ja’afar Rafin Dadi wanda ya jagoranci wasu fasihan matasan hudu domin ganin sun samar da wannan (Logo) ko Hatimi na jihar Katsina.

Ja’afar Rafin Dadi ya ce mun saka gasa ne domin ba da damar ga zakakuran Matasa masu fikira da kirkira, inda muka samu matasa 50 da suka nuna sha’awar nuna gwanintarsu a kan wannan gasar.

Bayan mun tantance su mu ka fitar da matasa Biyar, wadanda suka fi hazaka da kwarewa, inda muka hada su waje guda kowa ya ba da guddumuwar basirar da Allah ya ba shi, cikinsu akwai ni mai zane-zane Faisal Ja’afar Rafin Dadi, da Ahmed Muhammad, da Auwal Abbas da Ibrahim Muktar Zango da Jamilu Kabir da kuma Maryam Usman Dalhatu Batagarawa.

Da yake jawabi, Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, ya yaba, “Ya burge ni matuka kuma za mu gabatar da shi a gaban majalisar zartaswa, domin samun amincewa, ina da tabbacin majalisar za ta amince da shi, idan mun tattauna da kwamishinan Shari’a, idan akwai bukatar a mika wa majalisar dokokin Jihar Katsina, domin ya zamanto doka, duk za mu yi hakan,” cewar Gwamna Masari.

Exit mobile version