Connect with us

Ka San Jikinka

Yadda Wasu ‘Ya’yan Itatuwan Gargajiya Ke Taimakawa Lafiyar Dan’adam

Published

on

Amfani da ‘ya’yan itatuwa irin na gargajiya kamar magarya da aduwa da kurna da goriba da giginya da dai sauransu, na da matukar amfani ga lafiyar jikin dan’adam.
Kamar goriba, tana da amfani sosai a jikin mutum, domin akwai dusa a cikinta da ake kira da suna’ fibre’ a Turance. Ita dusar nan, tana taimaka wa masu fama da basir wato ‘ pile ‘ a Turance da kuma masu kiba, saboda cika ciki da take yi, sannan
kuma ta kunshi sinadiran ‘ phosphorus da ‘ vitamin C ‘, saboda wannan tsami-tsamin da dan sikarin da ke ciki yana taimakawa jikin dan’adam sosai.
Yanayin tsiron bishiyar magarya tana da sinadarin da ake kira ‘ magnesium ‘, wato dai sinadirai ne masu taimaka wa jikin dan’adam. Akwai sinadirai da ake kira da suna ‘co-N da co-factor’, masu taimakawa a irin abincin da muke ci, na jini, kamar su protein, carbohydrate. To suna taimaka wa wadanca abubuwan, don gyaran jiki da kara lafiya. Wato duk ‘ya’yan itatuwan da suke da ganye, ko suke da dandano na ‘ya’yan itace mai ‘ya’ya, to akwai wasu sinadirai da suke da shi, na ‘ vitamin A, vitamin B, vitamin K’ da kuma wasu sinadirai na wannan magnesium din da phosphorus din da suka kunshi gyaran jiki da gyaran fata da kuma kariya daga kamuwa daga cututtuka, musamman na daji wato ‘ cancer ‘.
Yanayin tsiron itatuwa a sahara. Duk wadannan kayan itacen suna taimakawa, musamman ma masu ciwon suga, wato ‘ diabetes ‘ da hawan jini, goriba da aduwa da kurna da gawasa na taimaka musu sosai, musamman ma idan suka ci tare da dusar cikita, suna sauko da sugar sosai ga masu ciwon suga. Don haka duk wadannan kayan itatuwan suna da mahimmanci sosai, kuma akwai abin da za ka
samu daban, a kowane dan itace da babu a wani, shi ya sa duk suke da amfani baki daya ga jikin dan’adam.
Yana da kyau mu tunga cin kayan itatuwan gargajiya, domin samu waraka ga wadansu cututtuka. Kamar mu yi watsar da cin kayan itatuwan gargaji, mu kama na Turawa muna ci, yin kana ba karamin kuskure ba ne. Shi ya sa za ka samu ba mu da kwari a cikin jikinmu, saboda ba ma ci abubuwan da za su gida mana ciki. Allah ya ba mu ikon cin ‘ya’yan itatuwan gargajiya, mu kyale na Bature.
Advertisement

labarai