Wata gimbiya ta yi watsi da dukkan jin dadin gidan sarauta ta auri wani talaka gama-gari. Wannan na zuwa ne bayan haduwarsu a shekarar 2012 a makaranta, lamarin mai ban sha’awa, jama’a sun yi martani kan masoyan, inda aka tattaro maganar jama’a kan batun
Aljazeera ta ruwaito cewa za a daura auren gimbiya Mako ta kasar Japan da wani talaka mai suna Kei Komuro a watan Oktoba na 2021. A baya kadan, an lura cewa ma’auratan sun yi ta yawo a intanet kwanakin da suka gabata bayan dangantakar su ta zama sananniya ga jama’a.
Ta bar sarautarta saboda talaka domin ta auri mutumin da kowa ya san gama-gari ne kuma talaka, gimbiyar za ta ba da matsayin sarauta da gadon ta da ya kai biliyoyin kudade.
A wani faifan bidiyo da Aljazeera ta yada, ma’auratan sun hadu da juna ne a shekarar 2012. An ce Komuro wanda lauya ne da ake fafatawa da shi a kasar Amurka.
Yadda suka shirya aurensu
An soke shirin ma’auratan na yin aure a shekarar 2018, bayan rahotanni da aka samu sun ce dangin angon na fuskantar matsalar kudi. Ko da yake a kasar Japan ana tube mace daga sarautarta lokacin da ta bukaci auren talaka, hakan bai shafi maza ba. Rashin samun isassun maza a cikin iyali yana haifar da rikicin maye gurbinsu.