Yadda Wata Karamar Yarinya Ke Kashe Mutane Babu Ko Gezau

Yarinya

An samu nasarar cafke wata yarinya wacce ta kasance sananniyar makashiya ce a karancin shakarun ta, wacce ta bayyana cewa ana biyan ta Naira dubu 10 ne kacal akan kowane mutum daya da ta kashe.

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Legas ta taba cafke wannan yarinyar ‘yar kungiyar asiri mai shekaru 20, wacce bayan wasu tambayoyi ta amsa cewa ta kashe mutane da dama kan kudin da bai wuce na sayan kaji ba, Naira 10,000 kacal.

Yayin da ‘yan sanda suka gabatar da ita a Legas, yarinyar mai suna Mariam Abiola, ta fada wa manema labarai yadda ta kashe mutane hudu a ranar da ta sanya Hijabi.

A cewar shugaban ‘yan sanda na jihar Legas, Imohimi Edgal, wadanda ake zargin suna cikin wata kungiyar asiri mai suna ‘Eiye confraternity Cult group’.

Da take ba da labarin yadda ta shiga kungiyar asirin, Mariam, wacce ta yi ikirarin barin makarantar sakandare, ta ce, ta gudu daga gidansu ne da ke Lafenwa, Abeokuta zuwa Legas don neman aiki kuma ta hadu da wani mai suna, Sodik a yayin aikin. A cewar ta lokacin da ta je Legas.

Mista Sodik ya dauke ta zuwa gidansa da ke yankin Ilasamaja inda ya gabatar da ita ga kungiyar asirinsu ta Eiye.

“Ya kai ni wurin wani mai maganin gargajiya, wanda ya ba ni wani abu a bkƙar fata don in ci. Ya gaya min cewa aikinsu shi ne kashe mutane don kudi. Ya ba ni bindiga kuma ya koya min yadda ake harbi. Na koyi yadda ake harbi ta hanyar harbi kan Bango. Sodik ya bamu bindigogi mu uku wadanda sabbin shiga ne kungiyar, da hotunan mutane mu kashe. Ya horar da mu ukun kan yadda zamu tsere bayan mun kashe wadanda muka kashe,” in shi ta.

Kamar yadda yarinyar ta fada yayin da take bayani, ta ce, babu wani daga cikin wadanda ta zara da kisa da suka tsira daga harbin ta. Kuma ta da labarin yadda ta kashe matashi daya a yankin Fadeyi da ke Legas, da wani kuma a yankin mai suna Hassan, dayan kuma a yankin Ajah ya ke duk a Legas. Duk lokacin da ta kashe wani, shugabanta zai biya ta Naira 10, 000, amma zai biya sauran Naira 20, 000 kan kowane mutum daya da suka kashe. A cewar yarinyar ba ta taba nadama ba bayan ta kashe wani, saboda ta dauki kisa ne a matsayin aikin da ake biyanta.

Da yake magana a kan kamun, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Legas, CP Imohimi Edgal ya ce, “yakamata Iyaye su kara himma ta hanyar sa ido kan ‘ya’yansu. Akwai matukar damuwa akan yadda yarinyar ta ke furci da alfahari akan yadda take kashe-kashen. Baya ga kasancewa mai kisan kai, ita ma ta kasance mai daukar makamai ga kungiyarta.

Shari’ar wannan yarinyar akwai matukar damuwa, ya sanya mutane da dama tsokaci. An kama wannan yarinyar tare da ‘yan kungiyarta kuma an gurfanar da su a kotu bayan an gudanar da bincike mai yawa.

Yarinyar tana da shekaru 20 ne kawai a lokacin da aka kama ta, an gurfanar da ita a kotu tare da mambobin kungiyar yayin da ‘yan sanda suka ci gaba da neman sauran mambobin kungiyar asirin.

Exit mobile version