Siyan sabuwar mota yakamata ya kasance dayan lokaci mafi farin ciki a rayuwar mutum, amma ga wani matukin mota mara sa’a hakan ta juye daga farin ciki zuwa bakin ciki a lokacin da ya danna kafarsa a kan wuta a wurin siyan motar.
Wani bidiyo na yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda wani dan Indiya ke shirin fitar da sabuwar karamar motarsa mai kirar ‘Kia Carnibal’ daga wurin kamfanin sayar da motoci, a inda ba zato tsamani, sai kawai ya tafi dodar zuwa ga bango, har sai da jakar iska ya fito.
Hoton bidiyon a farko a nuna mai siyen a lokacin da yake cinikin sabuwar motar tare da ma’aikacin kamfanin, a inda yake ba shi wasu takardu na karshe kafin ya bar shi ya fita.
Abubuwan rayuwa ba daidai suke tafiya ba kamar yadda ka tsara a kullum, domin wannan mutumin ya sayi sabuwar motarsa babu ko kazane a jikin ta, amma soboda tsautsayi ya tuka ta zuwa ga bango na kankare wanda hai sai da jakar iska ya fito.
Ni kaina da farko na zata wannan wani irin wasan kwaikwayo ne ko bidiyo da aka shiryawa a kafafen sadarwa, amma ban sami wata alama da ta nuna hakan a cikin wannan bidiyon ba. Duk mutane da ke kusa a lokacin da lamarin ya faru sai da suka mamakin gaske game da hadarin, suna hanzari don bincika harabar wurin ko fasinjojin suna lafiya, kuma babu shakka ba fadi a wannan lamari.
An sanya bidiyon ne a tashar ‘BMC HD bideos’ na man-hajar YouTube a watan Yuni, amma ya fara yaduwa ne a watan jiya bayan dan wasan Indiya kuma mai barkwanci, Sunil Grober, ya raba shi a shafinsa na Instagram. Yawan ra’ayoyi akan YouTube kadai a halin yanzu yana zaune sama da miliyan 9, kuma yana kara ci gaba.