A ranar Laraba da yamma ne wani dan kwangila a garin Tedas da ke kasar Amurka ya makale a cikin injin shirar kudi (ATM), a inda ya yi ta amfani da hikimarsa da wasu takardu wajen kokarin fita.
A cewar KRISTB, dan kwangilar yana canja makullin dakin shiga wurin ATM dinne na Bankin Amurka, a inda ya yi rufe kansa bisa kuskure ta ciki.
Lokacin da mutane suka zo ATM din don shire kudi, sai dan kwangilar ya silalo da wasu takardu ta cikin wurin da kudi ke fitowa yana neman taimako, domin ya bar wayar salularsa a cikin mota.
Ya yi hikima da wannan abu, a inda yake cewa a cikin takardar, “Don Allah a taimake ni. Na makale a cikin wannan dakin, kuma ba ni da waya a tare da ni. Da fatan za a kira maigidana.”
Richard Olden, babban jami’in ‘yan Sanda na Corpus Christi, ya shaida wa KRISTB cewa, “a lokacin da muka iso wurin mun ji murya na fitowa daga na’urar. Don haka muka fara tunanin cewa kila raha ce.”