Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Yadda ‘Yan Barka Su Ka Sace Jariri A Zariya

by
3 years ago
in LABARAI
3 min read
Yadda ‘Yan Barka Su Ka Sace Jariri A Zariya
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Wani abin almara ya faru kan yadda wasu ’yan barka su ka sace wa wata mata jariri daga zuwa barka a wata unguwa da a ke kira Layin Malam Mai-Bulala da ke garin Samaru a karamar Hukumar Sabon Garin Zariya a jihar Kaduna. Wakilinmu ya ziyarci anguwar kuma har ya zanta da mai jegon.

Malama Nafisa ita ce mai jegon da ’yan barkar su ka sacewa jaririn a wata rana gab da sallar Magariba a gidan da ta ke zaune gidan Kyauta Mai-Dissa.

Malama Nafisa ta ce, “wasu matane su biyu kowacce ta saka nikabi a fuskarsu su ka yi sallama da nufin sun zo yin ma na barkar haihuwa ne. Bayan sun gaishe ni, sai su ka ce min ina mai gidana? Sai na ce masu ba ya nan, sai su ka ce ai su matan abokinsa ne, sun zo ganin jariri ne tare da mijinsu, wanda ya na waje ya na jiran su.”

Labarai Masu Nasaba

’Yan Bindigar Da Suka Sace Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Nasarawa Sun Sako Shi

Wani Bene Ya Kuma Ruftawa Ya Danne Mutane A Legas

Hakan ya sa malama Nafisa ta amince da ’yan barka har ta dauki jariri ta ba su, su gani bisa al’adar Hausawa da su ka saba.

Amma me zai faru? Mai jego na mika wa wadannan ’yan barka jariri, sai su kuma su ka ce ma ta, “to bari mu kai wa mijin namu jaririn ya ganshi a kofar gida.” Sai mai jego ta ce ma su, “to babu komai.”

Bayan ’yan barka sun fito da jariri da kusan minti 30 ne sai mai jego ta ji shiru. Sai ta fito ta leka kofar gida, ba ta ga kowa ba. Nan take sai ta koma cikin gida ta sanar da jama’ar da ke cikin gida halin da a ke ciki, don daukar mataki.

Bayan sanarwa da sauran jama’ar da ke gida halin da a ke ciki, sai a ka sanar da uban jariri, wanda da ma ya na masallaci ya na sallah. Nan take ya fito a gigice a ka bazama cikin unguwa a na cigiyar wasu mata sanye da nikabi sun sace jaririn gidan Kyauta Mai-Dissa daga zuwa barka.

An kwashe kwana biyu cur a na rokon Allah a masallatai tare da cigiya kan lamarin. A rana ta uku ne sai a ka ji labarin wata mata ta je wata unguwa da a ke kira unguwar Gaiba kusa da gidan mai unguwar da a ke kira Malam Hamisu ta jefar da wani jariri.

Hakan ya sa jama’ar da su ka san da maganar su ka dunguma zuwa wancan iunguwa tare da mai jegon da a ka sacewa jaririn.

Cikin ikon Allah sai a ka dace yaron da a ka sacen ne a ka jefar a wannan unguwar. Nan take mai jego ta dauki jariri ta ba shi nono ya karba ya yi shiru. Da ma ya na ta tsaga kuka ne. Nan take su ka dawo gida da jariri.

Bincike ya nuna cewa, tuni ’yan unguwar da lamarin ya faru sun dauki matakin hana duk wata mata zuwa barkar haihuwar cikin dare.

Malama Nafisa ta yi matukar farin cikin ganin jaririnta da a ka sace kuma ta yi godiya da dukkan wadanda su ka taya su addu’a kuma ta yi kira ga dukkan sauran mata ’yan uwanta da su kiyaye da ’yan barka a duk lokacin haihuwa.

Kuma bincike ya nuna cewa a halin yanzu jaririn na samun kulawa kuma babu wani rauni tare da shi illa ciwon ciki da ya ke fama da shi sakamakon irin madarar da barayin su ka rika ba shi ba ta jarirai ba ce.

Uban yaron Malam Yarima ya yi godiya ga dukkan abokan arzuki da su ka taimaka da addu’a. ya ce, Allah ya saka da alkairi.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Kwankwaso Ne Ya Fara Bincikar Sarki Sanusi Ba Ganduje, Cewar Hamza Darma

Next Post

Shugabancin Majalisar Dokoki: Gwamnonin APC Sun Goyi Bayan Takarar Lawan Da Gbajabiamila

Labarai Masu Nasaba

’Yan Bindigar Da Suka Sace Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Nasarawa Sun Sako Shi

’Yan Bindigar Da Suka Sace Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Nasarawa Sun Sako Shi

by Leadership Hausa
1 hour ago
0

...

Wani Bene Ya Kuma Ruftawa Ya Danne Mutane A Legas

Wani Bene Ya Kuma Ruftawa Ya Danne Mutane A Legas

by Leadership Hausa
1 hour ago
0

...

 ‘Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum 360 Da Sace 1,389 Cikin Watanni 3 A Kaduna

 ‘Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum 360 Da Sace 1,389 Cikin Watanni 3 A Kaduna

by Muhammad Bashir
2 hours ago
0

...

An Sace Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa Tare Da Kashe Dogarinsa

An Sace Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa Tare Da Kashe Dogarinsa

by Abubakar Abba
13 hours ago
0

...

Next Post
Gbajabiamila Ya Shiga Sahun Masu Neman Matsayin Kakakin Majalisar Wakilai 

Shugabancin Majalisar Dokoki: Gwamnonin APC Sun Goyi Bayan Takarar Lawan Da Gbajabiamila

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: