Wani mai sayar da doya, wanda ya bayyana kansa a matsayin Yusuf, ya ce, mutane da yawa da ’yan bindiga masu addabar Jihar Kaduna suka sace, suna azabtar da su ba tare da jin kai ba, kuma a karshe su kashe su idan suka ki ba da hadin kai gare su.
Yusuf din mai shekaru 45 ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da PRNigeria ta samu, lokacin da ake yi masa tambayoyi da wani jami’in keken asiri.
Yayin da yake magana da Hausa, dan kasuwar, wanda aka sace kwanan nan, ya kwashe kwanaki takwas a hannun su, sannan daga baya ya samu kubuta, ya ce, shi da wasu mutum biyu sun biya Naira 750,000 a matsayin kudin fansa kafin ‘yan bindigar su sake su.
Da yake bayanin abin da ya faru da shi, mutumin mai shekara 45 ya ce, an sace shi tare da wasu mutum bakwai bayan wani kauye da ake kira Masalaci a Jihar Kaduna.
Ya kara da cewa, “Bayan mun wuce Masalaci, a yayin tafiyarmu, sai ga wani mutum ya fito kwatsam daga wani daji yana ihu. Daga nan ba mu san abin da ya faru ba kawai sai muka fara jin harbe-harben bindiga daga wasu wurare. A lokacin ne motarmu ta tsaya ba zato ba tsammani. Nan take direbanmu da wani fasinja suka mutu. Bayan sun hau motar mu, sai suka sace sauran mu suka kai mu cikin daji. Sun tattara duk kudadenmu sannan suka rubuta ‘Don Siyarwa’ a bayan rigunarmu.”
“‘Yan bindigan farmana sukla yi ta bugun mu babu tausayi, a yayin da suka ci gaba da jagorantar mu zuwa cikin daji. Kuma Sun yi barazanar kawar da mu idan muka ki bayyana kimar dukiyar mu. Ni da wasu abokan aiki mun yi karyar cewa muna da miliyoyi, don kawai mu ceci rayukanmu yayin da ‘yan bindiigar ke y mana barazana,” in ni shi.
Ya ci gaba da cewa, “Bayan haka, sai suka sa mana ankwa. Mutane biyu sun mutu nan take sakamakon tsananin duka. Wata Bafulatana da ta ba su labarin asalin gidanta ta samu kubuta. Bayan mun kwashe kwana biyar a hannun masu garkuwar, sai suka sako sauran matan biyu da aka sace tare da mu. Wannan ya kasance ne bayan da matan biyu suka bayyana asalin inda suka fito.”
“Amma ‘yan bindigar sun rike mu sun ki sakin sauran mu. daya daga cikinmu da ya fada musu cewa ba shi da wata alaka da danginsa, an yi masa azaba babu tausayi ba imani. Daga baya suka daure shi a kan bishiya suka harbe shi. ‘Yan kwanaki bayan an sace mu, ‘yan bindigar sun shigo da wata mace, likita da wani dan Nupe daga Wushishi, wanda daga baya suka kashe shi suka barta.”
Wani malamin jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya, a cewar Yusuf, shi ma an sace shi, a inda suka sace shi nhar gidansa.
Ya ce, “malamin ya amince zai biya su Naira miliyan 1.4 nan take, sannan kuma ya sayar da gidansa don kara wasu kudi a matsayin kudin fansa. Amma yan bindigar sun ki, suna cewa yana da wasu kadarori. Don haka, suka yi ta azabtar da shi ta hanyar zalunci. A yayin da bar kogon ‘yan bindigar, hannun hagu na likitan ya riga ya shanye saboda azaba.”
Ya kuma bayyana cewa, ‘yan bindigar sun sace wani soja da wani dan sanda, sannan suka tafi da kaki da bindigoginsu.
Yusuf ya kara da cewa, su (wadanda aka sace din) duk suna da gaskiya zai yi matukar wahala su kubuta saboda an yi musu sarka a kafafunsu.
Ya ce, “Amma ba kawai wannan ba, bugun da ‘yan bindigan suka yi mana ya nakasa mu, wanda ma sai da muka kasa guduwa.”
A cewarsa, babu daya daga cikin jami’an tsaron da suka kawo musu dauki yayin da aka yi garkuwa da su. Amma, ya ce suna ganin jiragen saman soja wani lokaci suna shawagi a yankin da aka ajiye su.
Wasu daga cikin masu garkuwa da mutanen sun ce sun rungumi ta’addanci ne yayin da suka kasa samun wani aiki mai ma’ana da za su yi bayan an sace shanunsu. Wannan shi ya sa suka dauki aniyar satar mutane, in ji su.
Sai da muka biya Naira 750,000 don kubuta, in ji Yusuf, a inda masu garkuwar suka bukaci Naira miliyan 20 akan kowannensu su ukun da suke tafiya tare. Amma sun biya Naira 750,000 kawai don kubuta.
Ya kara da cewa, “Lallai addu’o’in da masoyanmu suka yi, ya kasance babbar nakasa ga ‘yan ta’addan. Kuma bayan sun sake mu, daya daga cikin su ya yi mana rakiya zuwa wani wuri da ba a sani ba ya koma wurin abokan aikinsa.
“Mun gode wa Allah da muka dawo gida da rayukan mu, amma gaskiya dukar da muka sha a wurin ‘yan bindigar a lokacin da muke tsare, ya isa ya kashe mu,” in ji shi.